← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 39

Sashe 26

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dare yayiba,tashi muje na rakaki kar Hajo tayi miki fad'a" tashi tayi amma bataso aka katse musu firar suba, Abida itama ta tashi domin rakata, har part d'in Hajo suka rakata, har zata shiga ta juyo tace "Aunty yaushe ne zamu fara?" "Mifa?'bata fuska tayi tace "kai Aunty kina nufin har kin manta?" haka da tayi yasata dariya dan dama zolayar ta takeyi, tace "kwantar da hankalin ki gobe ma zamu iya farawa idan na dawo daga makaranta, watak'ir ma in dawo sha biyu da rabi" da yake tuni Yaya Mansur yayi join d'inta makaranta tayi jarabawar ta kammala secondary d'inta, nandai sukayi sallama ta shige ita kuwa Abida suka koma itada Baba. Yau safiyar laraba,tunda ya tashi yaga message d'in Bashhama kan zata sauka Nigeria 3:30 fatar shine wadda zata fara ganin fuskarsa, bai maida mata da amsaba yayi wanka ya karya ya tafi office. A'bangaran Bashhama ganin bai maida mata amsaba bata damuba dan tasan halin kayan ta, amma tayi k'udirin duk lokacin da yazamo nata tasan sai yadda tayi dashi, duk wannan girman kan nasa zai ajiyesu gefe,tanason ya zauna daga ita sai shi da yaransu biyu ko ukku dazasu haifa kamar yadda mahaifiyar ta ta zauna da mahaifin ta. Lokacin da jirginsu ya sauka tayi mamaki k'warai da bata gansaba,kuma shine wadda takeson fara tozali dashi,dan hakanne ma bata sarnar da Dadyn ta lokacin da zasu sauka ba,tace sai zuwa 4:30 zata sauka, waya ta d'auka ta kirasa amma kira kusan shidda bai d'aga kiran nata ba,dole ba yadda zatayi ta kira gida azo ad'auketa, koda direban nata yazoma tace yabida ita ta wajan aikin nasu, amma koda sukaje akace bayanan dole ta hank'ura tayi gida. Shi kuwa alokacin yana wajan miting duk kiran da take masa wayar sa na silent, saidai yanajin vibration d'inta kad'an,baidai d'agaba saboda miting d'inda suke mai muhimmancine, koma yasan wannan kiran bazai wuce nata ba, hakanne ma yasa yace acewa duk wadda yazo nemansa ace bayanan, yasan muddin baije d'auko Bashhama ba zata iya zuwanan,kuma ko ace yana miting zatace zata jirasa ne tunda bata idoce da itaba. Iyayanta sunyi matuk'ar murna da ganin gudar tilon 'yarsu abin k'aunar su,ta tarar da tarba ta musamman abincine da abin sha kala-kala,wanka tayi tasa wasu matsatsun kaya saikace barasan wani abuba shi musullunci,riga da wando ne wadda da kad'an ya saukowa gwaiwarta, sai riga mai guntun hannu,kayan sun matseta ta ko ina,kannan nata bako hulla saima gashin dokin da aka k'ara dashi. Bashhama farace tas, farinda ake ganin har yayi yawa, amma dakaga farin kasan ba farin Allah da annabi ne kawai ba ank'ara, dan takanas take aka mata allurar da tasa dukta da fatar kanta saida tazama fara, duk da tun can ba bak'abace tanada nata hasken, ba wani kyaune da itaba amma tanada gwargwadon nata, idan ka ganta kai tsaye zakasan haihuwar Alhaji Zakari ce,domin shine tabiyo gaba d'aya kamar yayi kaki,saidai bata biyo bak'in saba tabiyo hasken mahaifiyar ta. Saukowa k'asa tayi I iyayan nata suke zaune suna jiranta ta sauko aci abinci,kuwa ka kalli fuskar sa cike take da farin ciki ganin 'yarsu tagama karatunta gaba d'aya,yanzu zata zauna kusa dasu dukda aure zai d'auke musu ita, amma dai da sauki tunda anan Nigeria ne kuma gari d'aya, duk wannan abubuwan amma tane domin kawai nuna mata farin ciki ne agare ta, amma duk wannan abubuwan basa gabanta saboda rashin ganin hasken idaniyar ya. "Lafiya kuwa uwata na ganki haka? ko akwai abinda ke damunki? fad'a min inji ko miye inji,inma wanine in maki ma ganinki tun ayanzu ko inane ko d'an wace kasace kuwa, yanzunnan zamsa amin Maganinsa" Dady dama Mamsur ne tunda na sauka garin nan nake kiransa amma yak'i fikin, bam sani ba ko laf.... Mom surayya [2/15, 11:33 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA page 26 "Shine kike damuwar kanki? dan Allah ki natsu ki kwantarmin da hankalinki kici abinci,zai kirakine,tunda kikaga bai d'aga kirankiba k'ila yana wani abinne, kinsan irin aikin su Mansur" kai ta d'aga masa tana fad'in "to Dady" ta fad'a tana share hawayan da suka zubo mata afuska. "Yauwa 'yar Dady ko kefa,idan kaji shiru to lafiya,ki daina tayar da hankalin ki nima nawa tashi yakeyi kinji" kanta ta d'aga alamar to. Yana tashi daga office gida ya huce kai tsaye batare dama ya tuna da wata ma Bashhama ba balantana har ya tuno da wani kiran nasa da tayi,da yake ya isa ak'urarran lokaci ko wanka bai tsaya yiba yayi alwalla ya huce masallaci sakamakon kiran sallar da yaji anayi, anan ya zauna saida aka gama sallar isha i sannnan ya shigo ciki,kai tsaye bayi shige domin ya watsa ruwa saboda jin kansa da yakeyi atakure,bayan ya fito ya shafa mayunkansa da turare mai taushin kamshi,ya d'au kum ya shace sumarsa madai-daiciya daya tara, saida yagama kintsawa sannnan yafito ya nufi falo. Hajo na zaune akan kujera da littafin azkar ahannun ta tana dubawa,sai Mansura agefeta wadda ga dukkan alamu aitace tagama fad'a mata, "Barka da dare Hajo" Hajo da gaba d'aya hankalin ta nakan littafin da take dubawa saida yayi maganar sannnan hankalinta yakai gareshi "Yauwa mai sunan Malam andawo?" zama yagyara daga zuk'unnan da yake yace "eh Hajo na dawo, ina abincina hanjina kamar anamin wawa tun karin safene acikina" "Kallon sa tayi tace "kaganeka mai sunan Malam kanason zama da yunwa, basan mi kakeson zamaba, ko sokake olsa takamaka ne?" Murmushi yayi tare da fad'in "wallahi Hajo damace ban samuba ko salla dakyar nake samu inje inyi,kuma bayan sallar la'asar muka shiga mitin". "Amma duk da hakanan yakamata azanka samun lokaci anacin abinci, yunwa kasan ba k'anwar uwar kuwa bace" dubanta takai ga Mansura da tayi kamar bata wajan kuma ko kad'an batama kalli Mansur ba bale har yasamu albakacin gaisuwa "Ke Mansura je ki d'aukowa yayanku abincinsa akicin,ki biyo masa da zo'bon nasa aka nasa yananan acikin firji" batare da tace komai ba ta tashi tana cinna baki gaba alamar batayi niyaba, duk abinda take yana lure da ita, tunani yakeyi aransa irin rainin da wannan yarinyar ta masa,wane irin hukunci ya kamata ya mata,yana cikin Wannan tunanin harma baisan lokacin da ta aje abincin agabansaba saidai girmawar ta yagani agabansa, binta yayi da kallo har tashige d'aki. Dubansa yakai ga Hajo yace "bansan lokacinda wannan yarinyar zatayi hankali ba sam, girma take akullu renin hankalin ta na k'aruwa,kiduba fa ko kallon ban ishetaba balantana nasamu arzik'i gaisuwa agareta" "Kaima mai sunan Malam kanada taka matsala, gaba d'aya baka sa yarannan ajikinka sai azattar dasu dakakeyi akoda yaushe, kasani duka da kyara da hantara bayasa yaran yanzu su fasa abinda sukayi niya,saima haka yak'ara musu k'aimi akan abinda sukayi niya, akoda yaushe ina sanar maka ka d'ora janyasu ajikinka kana sakar musu fuska kuna wasa da dariya kamar yadda kaga d'an uwanka Abdullah keyi,hakan zaisa duk ranar da sukayi wani laifi idan kanuna musu 'bacin ranka zasusan sunyi ba dai-daiba,idan kuma ka hukuntasu zasu gyara agaba" Kallon Hajo yakeyi da mamaki yadda take zaro zace saikace tana gaban sifika ne "naji kawai yace da ita badan ya d'au alk'awarin yin abinda ta fad'a ba,ya fad'i hane domin kawai ta shafa masa lafiya, amma duk yarinyar da tayi sake tayi abin duka zaici k'aniyar ta abanza ne kawai. Bai sake magana ba har saida yagama ya d'auki zo'bon da yayi sanyi amma ba sosai ba dai-dai tadda mutun zaisha batare daya wahalar da kansaba, itama ganin yayi shiru sai taci gaba da duba lintafinta, saida ya gama ya tashi yana mata saida safe, "Allah yabamu alheri" ta fad'a batare da ta d'ago kantaba, harzai shega cikin d'akin sa yaji maganar ta tana fad'in "bazakaje gaida iyayan nakabane kake k'okarin shiga d'aki?" "Eh wallahi, saidai zuwa da safe zan shiga in sha Allahu,akwai abinda ban k'arasaba inason in k'arasahi" kai ta d'aga tareda cewa "to shikenan". Bai samu ya k'arasa abinda yakeyiba sai kusan 10:35 mika yayi tare da fad'in Alhamdulila, ya tashi yashiga ban d'aki yayi biyan buk'atarsa sannnan ya d'aura alwalla ya fito,kabbarta sallar shafa i da wutiri yayi,bayan ya gama yayi azkar d'in da zaiyi sannnan yaje ya kwanta basa gado tare da jan bargo ya rufe daga k'afafuwanta zuwa cikinsa, har zai karanta addu ar bacci yaga wayar sa na kawo haske, hannu yasa ya d'au wayar har ta yanke, kiran ya duba wanda ya kasance na Bashhama,koda ya duba kusan kira goma sha d'aya nata sai biyar wanda yakasance wajan aikine,su yafara kira yaji abinda ke faruwa sannnan daga baya yabi kiran nata Bashhama dakecan cikin damuwa ganin duk kiran da take masa bawanda ya d'aga kuma daga baya raji yana waya,tashiga damuwa sosai har zuciyar ta na sak'a mata koda wata yakeyin wayar, hankan yasa tasake gwada keran amma har alokacin cemata ake yanayin waya,tana cikin wannan damuwar da sak'e-sak'en zuci taga kiran nasa ya shigo Jikinta har yana rawa wajan d'auka tare da fad'in "hello my husband" shiru na wasu sakani kafin daga baya taji yace "Assalamu alaikum" take tagane kuskuranta,domin yasha fad'a mata idan bazata iya masa sallamar musullunci ya tanadar ta daina damusa dawani hello kota daina kiransa, cikin k'asa da murya tace "kayi hank'uri dan Allah assl... ~Mom surayya~ [2/15, 11:33 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 27 "Assalamu alaikum" amsawa yayi kafin yace "lafiya naga wannan kiran naki haka?" shiru tayi jin abinda ya fad'a,wani abu taji ya tsaya mata awuya,amma sanin halinsa da tayi zai iya kashe wayar sa tayi saurin cewa "amma miyasa bakaje d'aukoniba bayan Kuma nagaya maka lokacinda zan iso? kuma nayi Kiran wayar ka baka d'auka ba" "Uzirine ya rik'eni" shine kawai yace da ita "amma kuma husband shine baka kirani ka gayamin ba, harfa wajan aikinku naje" ta fad'a cikin shagwa'ba da kisisina "kin ajiyenine da komai zanyi saina fad'a miki?" maganar sa tasa murmushin dake kan fuskar ta gushewa "sorry" ta fad'a cikin sanyi hawaye na cika mata idanu, maganar sace ta katse shirun nata "inada zanyi saida safe" ya kashe wayar tasa gaba d'aya kamar ta koma damunsa,yayi addu ar bacci yanajan bargo har kansa. Asuba tagari Mansur Hawayan da suka cikamata idanune suka samu gangarowa akan fuskar ta, batasan wani irin so take masaba wanda yakesa
Chapter 26 · 0% Book details