Sashe 14
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga, afalo ya tarar da ita Khadija shafa mata man zafi ak'afafuwanta. "Mai sunan Malam andawo kenan? yakabaromin 'yar amanar tawa da 'yar uwar ta?, nasan dai dunacan suna kuka!" Zama yayi gefen kujera kafin yace "kekike ganin haka,dama ai duk kukan datakewa mutane da kwancin rashin lafiya duk na iya shegene, yarinyar nan da kike gani d'igon hawaye Babu afuskarta, Ruk'ayya daice harda hawayan ta saida na lalla'bata" "Kai mai sunan Malam banda sharri, Mansura ce bazatayi kukaba?! kaidai ka fad'a ne kawai kar natayar da hankali na, kuma ai dole na hank'ura tunda sun riga da sun tafi" Kallon Khadija yayi yace "ke jeki d'aukomin fura acikin firkin" Tashi tayi ta d'auko masa takawo gabansa ta ajiye,sannan ta koma kicin ta d'auko k'aramin kofi ta ajiye. Mai sunan Malam dan Allah inason yau idan k fita kabiyomin da kilishinnan da kake sayomin kwana biyu kabar sayomin... Mom surayya [8/26, 2:16 PM] Mom Surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Taping MANSURAS BY; SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Wannan littafi na kud ine akan 500,shedar biya itace 2729922771 Saratu Mohammad zenith bank, ko kuma kati na MTN ta wannan number 07089530588 Paid book Free page Page 9 "Waike wannan tsufan naki kullun k'wd'ayi yake ne? Kullun da abinda zakisa asoyo miki,indan mutun ya biye miki sai aljihunsa yayi k'asa" "Nicema mai k'wd'ayi ko mai sunan Malam? ba komai idanma kace bazaka sayaba zansa d'an Rabi ko Amadu su sayomin tunda sune na haifa ba kaiba" "Kinganki Hajo akwaiki da abu,yanzu kinji nace bazan saya bane?" "To naji kana wani maganane,alhalin bansanka da mak'oba" "Ki kwantar da hankalinki kamar kinyi bak'o ya mutu kinyi filo da gawa, idan kilishine sai kin ture" "Yauwa d'an al barka,nagode Allah shi al barka,kaima yabaka masuyima" "Ameen ameen Hajo Allah yak'ara lafiya da nisan kwana, in sha Allah har jikokina saikin gani" "Kayya mai sunan Malam,ni ko naka 'ya'yan nagani na gode Allah, wannan muruwar mai d'auke-d'auke batabar yaraba,balemu da akuda yaushe jiran tsammani muke" "In sha Allah zakima gani harki goya" "Badai jikokiba,idan kacemin 'ya'yan ka kan zan yarda" "Ai Hajo nidake ba asan gawar farin ba, karshe ta sai kiga namutu na barki" dariya tayi tace "mai sunan Malam kenan! Nidai jeka kar kuma kadawo kacemin ya k'are" fita yayi yana dariya. Yana fita a compound d'in gidan kiran Jabir ya shigo wayar sa,saida ya bud'e motar ya shiga ya zauna sosai sannan ya d'aga wayar, lokacin har tayi kusa tsinkewa, "ya akayine man?" "Dai-dai wallahi, kana inane yanzu ko kana gidane?" "Eh ina gida amma gani amota zan fita,wani abinne ko akwai matsala ne?" "Ba wata matsala nace, yarinyar nan ce wadda d'an gidan Alhaji Zakari yawa fad'e muka gano inda take itada iyayanta, saidai kamar yadda akace an canza musu asibiti abin ba hakabane" Jin wannan maganar yasa yace "wannan maganar bata waya bace kana ina yanzu?" "Ina gida ban dad'e da shigowaba, nima yanzunan Faris ke kirana" yace "shikenan ganinan zuwa" kashe wayar yayi yana tayar da mota yayi ribas, mai gadi ya bud'e masa ya fita. Koda ya isa gidansu Jabir yana tsaye ak'ofar gida yana jiransa,shida kansa ya bud'e masa get yashiga cikin gidan,bayan yayi parking aparking space ya fito,gaidasa yayi cikin girmamawa amatsayin sa na ogansa, harararsa Mansur yayi yana dad'in "miye haka? kasan nandai ba a office mukeba". Dariya Jabir yayi yace "sorry sir" kad'a Kai yayi yace "yayima kyau,zan kamakane, Umma nanan?" "Eh tananan afalo itada wannan yarinyar" "Wace yarinyar kenan?" gaba yayi yana dad'in "wanake gaya maka?" binsa yayi abaya yacewa "shegen kaya,bari in shiga daganan in ganta". Da sallama suka shiga cikin falon, Jabir ne agaba sannan Mansur, Umma ce ta amsa da fara'arta ganin wadda ke bayan d'an nata, "Mansur kaine yau agidan namu?" "Wallahi Umma", ya zauna anan k'asa yana gaidata, fuskarta da walwala take amsawa da tambaryar iyayan nasa tare da Hajo. "Kafiyar su lau Umma", "yasu Mansura lafiya suke" yace "lafiya k'alau suke yauma suna makaranta" tace "okay yau sun shiga islamiya kenan?" "A a Umma bodin ce" da d'an makiki tace bodin kuma?" "eh Umma, yau aka kaisu da safe" "To Allah yaba sa'a,amma nayi mamaki da 'yar rigimar Hajo ta zauna?" Yayi d'an murmushi yace "dolene ai taje tunda ba ita kad'ai bace" tace "hakane" Budurwar dake zaune tare da Umma ce ta gaidashi cikin girmamawa,amsawa yayi yana maid'an mata kallon gefen ido,ba laifi tanada kyauta kuma da alama tanada kamun kai. Tashi yayi yacewa Umma bari yashiga d'akin Jabir akwai abinda zasu tattauna. Tace "okay,ke Saudat tashi ki Kai masa ruwa" tashi tayi ta nufi firjin sukuma suka fito domin zuwa part d'in Jabir. Zama sukayi akan kujerun dake falo, Mansur yace yi sauri fad'a min,kace yarinyar bata asibiti?" "Eh, kamar yadda Faris ya gayamin yace basa asibiti suna a unguwar jan bulo anan mahafiyar ta ke jinyar ta,mahaifinta shima ba lafiya saboda abinda ya faru,abubuwa sunwa mahafiyar tata yawa,ga kula da muji ga kuma 'ya, kuma ya tabbatarmin da Alhaji Zakari ne yasa subar anguwar". "Allah sarki, wad'annan mutanan ya sukeso suyi da hak'in wad'annan bayin Allah?" Kafin Jabir yace wani abin Saudat tayi knocking d'in k'ofar, izini Jabir ya bada tashigo cikin sunkuyar da kai,tiran dake hannun ta ta ajiye wadda ta d'auko ruwa da jus da kofuna guda biyu, sannu ta k'ara musu,Mansur ne kawai ya amsa ta juya ta fita. "Inajinka!" "Kawai yanzu so nake nasan wane lokaci ya dace muje?" "Yau mana,ko zuwa yammane,kaga gobe akwai aiki bazamu sami lokaciba sai zuwa dare, kuma kafa akwai gajiya alokacin" "Eh hakane kuma,mu bari idan muyi sallar la'asar sai muje" "To shikenan,amma wanan yarinyar itace wacce Umma takeson ka aura?" Jabir ya ta'be baki yace "wai" "Ban gane waiba,mikake nufi da haka?" cikin rashin son maganar yace "itace,ni wallahi kwata-kwata batayiminba,gata yarinya inaga bafi 17 year's ba, ina laifin ace tayi 20 haka,ashekarannan tagama secondary School, mima tasani akan aure! kasan atsarina inason in auri wayayar macce wadda tasan kanta tasan yadda zata kula da miji da 'ya'yan da zamu haifa" "Amma sai nake ganin yarinyar nan batada matsala,gata ga dukan alamu tanada kunya da tarbiya,sannan abinda bakasaniba k'ananan yarannan wad'anda basu gama sanin miye rayuwaba sunfi dad'in zama indan kayi hank'uri dasu, sune zakace ga yadda za ayi suyima batare da 'bata lokaci ba ko canza fuska, bisa ga wadda tagama sanin kanta tana ganin takai dai-dai dakai,kabi umarnin Umma zakayi alfahari da hakan,idan yaso idan kanason tayi karatu sai tayi agidanka". "Bazaka gane abinda nake nufiba, kuma kana cewa k'ananan yara sunfi dad'in zama ai naga kai k'aramarce ka bid'a" "Ni kafi kuwa sanin dalilina na auran da zanyi na Bashhama,amma badan gakaba ba abinda zanyi da ita,amma zan baka mamaki... ~mom surayya~ [8/27, 6:12 PM] Mom Surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Taping MANSURAS BY; SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Wannan littafi na kud ine akan 500,shedar biya itace 2729922771 Saratu Mohammad zenith bank, ko kuma kati na MTN ta wannan number 07089530588 Paid book Free page Page 10 "Lallai kace irin 'yar sha biyar Kai zaka d'auka ko sha shidda?" "Kodai 'yar sha biyu ce zaka gani,kawai dai ka hank'ura kabi za'bin Umma" "Ya zanyi ai dole na hank'ura inyi biyayya,yanzu ma da kaganta nan itace tasa tadawo nan da zama wai dan mufahinci juna,ita kuma dayake k'ilama tanaso ta kwaso k'afafuwanta tazo" "Bawani tana wani sonka, biyayya tadaiyi ga iyaye, ka aure ta nan gaba zakayi al fahari da hakan, kuma zakace ni nafad'a maka" "Karka damu kanka,domin Umma ta tabbatarmin da cewa matuk'ar tana araye banida mata inba Saudat ba,kuma bakinsu d'aya da Dady, kawai saidai ince Allah yasa haka shine mafi alheri" "Shine abinda zakace,bari inzo in tafi,kabiya ka d'auke ni a motarka dan nagaji" "Okay in sha Allah" tashi suka fito gaba d'aya, saida Mansur ya shiga yama to Umma sallama sannan yazo ya shiga mota ya tafi. Alhaji Zakari fa ya damu matuk'ar gaya sai famar kira-kiran wayoyi yakeyi,duk wadda ya kira saidai tace tunda wannan case ahannun Mansur yake ya hank'ura ashiga kotun sannan susan abinyi,yanzu abinda zai fara ya bid'e lauya tun kafin lokacin shigar yayi, mutun d'aya ne yace zai tunkaresa da maganar,dukda yasan shi mutun ne mai ra'ayin kansa kud'i basashi abinda biye niyaba, amma in sha Allah zaiyi duk yadda kar aje kutunan". Yaji dad'in wannan maganar da sai yaji damama amma bacci bai gansaba acikin wannan daran,tunanin yakeyi yadda d'ansa abin k'aunarsa zai kwana acikin wanan wajan wanda yake tunanin yakeyi sauran wajan da k'undan cizo bazasu barsa suyi bacci ba, awannan daran dai bacci sai 'barawo ne yayi gaba dashi. Washe gari tunda farar safiya ya tashi, yanayin waka yaje station d'in ko karyawa baiyiba kamar yadda baici ba daran jiya, yauma kamar jiya ba abari ya gansaba duk da borin da yayi tayi amma ba wadda ya kulashin har yaga dai sun maidashi mahaukaci yasa yafita yana cewa subari su gani da d'ansa ya fita duk sai yasa an d'aure shi,duk sai yaga bayansu. Wasa wasa saida Habib ya kwashe kwana shidda station baiga koda k'eyar idanun mahaifinnasa ba,ya shiga damuwa dan sauro duk ya 'bata masa jiki,dan duk jikinsa cizon sauro ne yayi masa k'ananan k'uraje, kuma tun aranar bai k'ara ganin Mansur ko a idanunsaba,saidai akullun za akawo masa abincin safe rana dare,wannan kan kullun ba fashi,kala bai sababa har yabarwa Allah yanaci,tunda dai yunwa ba buyar gidan kuwa bace. Mansur saida ya tsaya kan haya yasayawa Hajo sak'on ta sannan yayo gida, bacci ya d'aukesa saida har sallar la'asar ta gota,dan kusan 4:25,koda ya tashi ya dubi agogo yaga lokaci ya gota yace "subuhanallah,ya akayi bacci na yayi nauyi haka?" Tashi yayi ya shiga ya d'aura arwalla yazo ya tadda salla anan cikin d'akin,yana gamawa yaje yayi wanka sauri-sauri yaje yayi wanka ya shirya dan yaga kiran Jabir har uku, koda ya gama shiryawa 4:52, yana fitowa yaga motar Jabir anan compound gidan, shi har ya manta da yace yazo ta d'auke shi, gaidasa yayi 'bata lokaci ya shiga suka huce... Koyi hank'uri da wannnan, dakyar nasamu nayi wannan saboda tafiya ta kamani gobe zuwa nijar in sha Allah,dan haka zakujini shi na kwana biyu ~mom surayya~ [2/15, 11:29 AM] mom surayya: Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMED MOM SURAYYA Page 11 Koda suka isa ak'ofar gidan da aka tabbatar musu aciki suke suka tsayarda