Sashe 30
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
d'auko tazo ta zauna kusa da Hajo suka sata tsakkiya, wayar taba Hajo tace "rik'e kigani da kyau! amma fa ki rik'e sosai kar wajan dariya ki yarda wayar mutane" sannan tasaki vidion. Tunda Hajo taga abinda vidion ya k'unsa da yadda abin ya kasance take dariya, kai Mansura ta iya k'eta wallahi, Rukayya ma dai saida tadaraya, dan wallahi ko bakayi niyar dariyaba saika dara, Hajo tace "Ni wallahi kinmin dai-dai wannan abin da kikayi, banci iskanci da lalacewar duniya taya zakizo gidan surukkai da wannan banzar shigar, kuma da sunan wai 'yar gidan musulmai, kai Allah waddaran naka ya lalace" Rukayya tace "Ni wallahi tausayi ta bani bakiga da takuma kalar tausayiba, musamman lokacin da kike fad'in haka tazo a tsirara, wallahi Mansura sai abarki, amma fa ina tausaya miki duk lokacin da Yaya ya samu labari" wayar ta ansa daga hannun Hajo tace "oho dai, nidai nasamu na rage kaso 80 na abinda yayi min, kuma wallahi yanzu duk abinda yayimin akanta zan rama duk ranar da na ganta ba ruwana ehe" Hajo tace A afa Mansura kinfa san hakin mai sunan Malam ba raga miki yakeyi ba, kar juje kiyi abinda zai halakaki abanza awofi" dariya tayi tace "halako! nabi halaka da gudu babu riga, idanma ya iya kar tabarni darai, inajin iyakar wahala kennan? barima kuji ruwan dama kuka gani tasha tazubar tace muku k'warewace tayi, ba wani K'warewar da tayi nice na bud'e na zagga musu gishiri tayadda babu yadda zatayi ta iya shansu, domin ruwanmu na gidan mutunci ne ba masu k'wai kwayo da arna ba" Dukan su idanu suka zuba mata domin abin nata ya basu maki, Rukayya tace "kai Mansura tun zuwan ta gidannan baki bare tasha iska ba ko na minti d'aya ba, koma harda wani zuwa kina kiran Aunty kiyi hank'uri waye-waye, ai tun anan nasamiki alamar tambaya?" Batakai ga bata amsa ba Khadija tayi sallama ta shigo, gaida Hajo tayi sannan ta dubi Mansura tace "Aunty wai kizo inji Momy" da sauri ta dubeta tace "Mi kuma nayi da take kirana yanzu kuma saboda Allah" tace "nima ban saniba tadaice inzo in kira mata ke" harararta tayi tace " munafuka nasan kinsani badai zaki fad'a bane kawai, je kice mata ganinan zuwa" tashi tayi batace komai ba domin tasar halinta sarai zata mangareta awajan, bayan ta ta tashi tabi dan tasan halin Momy idan ma bata jeba zata iskota ne, kuma tasan bazata sha da dad'i ba. Mansur kuwa tunda sukayi waya da Bashhama tace mai gashinan ta fito zataje yace shikenan, bai kuma bin takanta ba yaci gaba da aikin dake gaban sa, saida yaji am fara kiraye-kirayan sallama la'asar sannan ya d'au waya domin yaji ki ta koma, amma kira kusan ukku bata d'aga dan haka ya k'yaleta bai kuma kiraba,yasan idan tagani zata kirasa, ya tashi ya shiga bayi yayi alwalla yaje masallacin dake office d'in, bayan ya dawone yaga kiran Momy tayi masa 2 missed call, da yake anan office d'in ya barta, zama yayi tare da maida mata kiran yaji ko lafiya. "Assalamu Alaikum" Momy dadata d'aga kiran ta fad'a "wa alaikussalam, Momy ina wuni ya gida?" ya fad'a cikin son matar da girmamata "Lafiya k'alau Mansur ya aikin naka kuma?" yace"lafiya k'alau Momy" tace "masha Allah haka akeso, dama zance ni idan ka tashi daga office kafara biyowa tanan 'bangaran akwai maganar da nakeson muyi dakai" shiru yayi kafin yace "lafiya Momy?" dariya tayi tace "lafiya k'alau Mansur kar ka tayar da hankalinka maganace kawai zamuyi" cikin sakin ajiyar zuciya yace "to shikenan sai nazo" sukayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da aikin sa. Da sallama Mansura ta shiga falon Momy gaban ta na fad'uwa, wallahi harga Allah tana tsoron Momy dan tasan ita ba kanwar lasa bace, danshine kwata-kwata bata cika zama a inda takeba, saidai koda yaushe tana wajan Hajo ko Ummi, har takai gaba d'aya ta koma wajan Hajo gaba d'aya saboda canne tafi sakewa, zaune ta tarar da ita afalo suna magana da Khadija ahankal, kuma ga dukkan alamu akwai abinda Khadija ke gaya mata dan tana ganinta tayi saurinyi shiru tana gyara zamanta. Waje ta samu ta zauna tace "gani Momy" harararta tayi tace "na ganki kone akauniya ce aka fad'a miki?" itadai shiru tayi batace komai ba, Momy tace gaba "Wato ke rashin mutuncin naki k'aruwa yakeyi akullun ko? ban saniba ko k'yaleki da kikaga anayine komi oho, mi yarinyar mutane tayi miki kika nuna mata rashin hankalin naki afili" Tunda Momy ta fara magana jikin ta ke rawa tana neman rikicewa, "amma babu munafuka irin wannan yarinyar Khadija, wato taji lokacin da nake gwadawa su Hajo vidion nan ko" tayi duk wannan maganar tana kallon Khadija. "Miye na kallamin yarinya bani nace na tambayeki ko itace mai tambayar" ahankali ya girgiza kanta, "to bani amsar tambayar da namiki" ahankali tace "Wace yarinyar kike nufi" ta fad'a gaban ta na fad'uwa "karki rainamin da hankali Mansura, sarai kisan wacce nake nufi,ko kin d'auka duk abinda kike idanuwana basa kanki? sarai nake kallon ki dan haka ki bani amsar da nake nema akanki" jikinta ne ya kama rawa muryar ta na karkarwa tace "wallahi ban mata komai ba mom... Kafin ma ta k'arasa maganar Momy ta watsa mata marin da saida yasa takan zaunan da bata k'arasa yiba "karma kisoma min wannan banzar maganar take da bayarda zanyi da itaba sam" Mansura ta shiga tashin hankali dan wallahi batasan idanuwan Momy na akantaba da tajanza takon ta, yanzu ya zanyi? take tambayar kan nata "Bani wayar Yaya dake hannunki ko na tattakaki anan shawarakar yarinya kawai" jiki na rawa tayi saurin ciro wayar ta bata dai-dai lokacin da Mansur ke shigowa. Idanu ya zuba musu ganin irin zaman da suke kafin yasamu yace "lafiya Momy mike f... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 31 "Lafiya k'alau Mansur k'araso daga ciki mana ka tsaya abakin k'ofa" shigowar ya k'arasa kamar yadda Momy ta buk'ata, Mansura kuwa acikin raita fad'i take ta kad'e har ganyanta tasan saidai amaidawa Hajo ita akakkarye ba k'asusuwa ajikinta. "Ka'bi wayar nan kaga abinda yarinyar nan ta aikata" taji muryar Momy tana fad'in haka, ka'bar wayar da Momy ke mik'o masa yayi yana watsa ma Mansura wani kallon zaki gane bakida hankali tun baiga koma miyeba, shidai baisan yaushe ne yarinyar nan zatayi hankali ba "Momy bari inje in watsa ruwa jin kaina nake atakure" ya fad'a tare da mik'ewa tsaye, "shikenan Mansur ai kuna fama wallahi, mutun idan ya fita tunda safe bayada wani hutu sai yadawo gida,idan ya dawo ma sai yaraba dare yana fama da laptop" yace "Ya zamuyi Momy neman halal ne, dole kuma ga tanayin aikin mu da yake kuwa kansa ya sani, akan kud'i komai d'an adam zai iya yi,sai kaga idan kansa wasa komai zai joye maka" Momy "hakane kuma saidai rok'on Allah yaci gaba da dafa muku akan lamuranku" "Ameen ya Allah" kallon gefen da take yayi yace "ke tashi muje" jin tsawarsa tayi har cikin ranta jikinta na rawa tatashi, binbayan sa tayi ganin ya nufi k'ofa, zata fita taji muryar Momy tana fad'in "sakarya kawai, ko yaushe girma kike amma sai dad'a cin k'asa kike" batace komai ba ta fita tana bin bayansa, ai itayau tasan sai buzun ta sai yadda yayi da ita. Yana kai ta part d'in Hajo yayi tsaye dan yasan bazai mata wuyaba ta aka aciki, saida tayi gaba sannan yabi bayanta. Tana kai part d'in tayi tsaye tunda dolene sai yazo ya bud'e sannan, dama duk ranar da yakeson yaci zalin su anan part d'in yake kawosu ta yadda ba wadda zaiyi saurin ji bale akawo musu agaji, kuma tasan inzai yankata Momy ko lek'owa bazatayi ba ita da tasan komai. 'Dakin yayi 'yar k'ura sakamakon kwana biyu da akayi ba d'an shegesa ba, "jeki gyaramin bayi da d'aki sannan kizo ki gyara falo, saura kimin ba dai-dai ba" taji maganar tasa. Fita taga yayi harda rufe k'ofa ko ina zaina ohon masa, hakadai taje ta fara gyaran tunda batada wata mafita. Shi kuwa yana fita part d'in Hajo ya huce kai tsaye ba kowa afalon dan tini Rukayya ta koma part d'in Ummi Hajo kuwa na d'aki tunda tashiga bata fito ba, d'akinsa ya nufa yaje yayi wanka tare da d'auro al walla, shiryawa yayi cikin Kaya masu d'an nauyi dan yanajin alamar sanyi-sanyi, saida yagama duk abinda yasan zaiyi sannan ya shiga d'akin Hajo lokacin tuni anfara kiran salla, gaida ta yayi ta amsa bai tsaya wata duguwar fira ba yace zaije masallaci sai ya dawo, adawo lafiya tayi masa ya fito, part d'in nasa ta nufa yasa makulli ya bud'e falon, ba laifi ta gyara har moping tayi ko ina sai haske yake, bata afalon bai tsaya duba a ina ta shigaba ya juya ya fita jin suna k'ok'arin tada salla, wurin saurin ya manta bai tsaya rufe k'ofaba. Mansura da taje wurin d'oko turare ta fesa taga k'ofar abud'e ai batasan lokacinda tayi jefa da turaran ba ta are na kare, bata tsaya ako ina ba kai tsaye sai part d'in Ummi. Ummi dake k'ok'arin tada salla sai ganin mutun tayi ya fad'o cikin d'aki ana haki, ganin itace tace "ke Mansura lafiya keda waye?" Tana haki take gaya mata "ba Yaya Mansur bane ya kine part d'in sa zai daka shine nasamu na gudo nan" ta k'arasa zama kan gandon da take kusa dashi. "Oni 'yasu, wai yaronnan miyake son maida kansane, so yake sai ya nakkasakine zaiyi hankali, Kinga izaman ki anan idan ya isa yazonan ya dakeki" har cikin ranta taji sanyin maganar Ummi, domin tasan ko giyar wake yasha bai isa ya daketa agaban Ummi ba, kuma gobe da wuri zatasa direba yakaisu makaranta bama zata bari su had'uba. "Jekiyi alwalla kizo kiyi salla kar lokacin ta yashige" taji Ummi na mata magana, dato ta amsa tashiga bayi domin gabatar da alwallar, tana fitowa tazo ta kabbarta salla. Lokacin da Mansur ya dawo daga masallaci bai tsaya ako inaba yayo part d'in nasa, yayi mamakin ganin k'ofar abud'e,yayi saurin shiga falon ama wayan, yasan arina wai ansaci zanan mahaukacci, amma duk da haka saida ya duba cikin d'aki dama