Sashe 18
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nuna mata alamar yana aciki. Cikin irin wani yanaye naga tatashi mai tattare da sanyin jiki ta nufi k'ofar ban d'akin, k'ofar ta shiga bugawa tare da kiran sunansa "Habib, Habib,wai baka jinane ko sai nasa an "balla kofarne na shigo?" inaga jin abinda tacene yasa ya bud'e k'ofar yanayi k'asa da kansa. Hannu ta d'aga ta wankesa da lafiyayun mari guda biyu hagu da dama tare dakai masa duka ta ko ina. "mika aikata haka Habib? son kake ka tozartamu aidon duniya ne? Yanzu mikakeson in fad'a ma mahaifiyar yarinyar nan ne? daga dawowarka Habib? wallahi ka cuceni, kasa nakasa rik'e amanar da nace zan rik'e" kuka ta fashe dashi tare da durk'ushewa a k'asa. Banga alamar nadama tattare dashi ila kukan da mahaifiyar sa keyine ya sanyayar masa da jiki, ganin kuka bazai fiddataba yasa ta d'au waya yayi ta kira mahaifinsa, ba ad'au wani lokaci mai tsayi ba sai ga Alhaji yadawo, shima hankalinsa ya tashi dajin abinda d'an nasa ya aikata, gyarani yace Hajiya tayi kafin asan abinyi, amsa masa tayi dato yaja hannun Habib sukabar cikin d'akin. Hankalin Hajiya ba k'aramin tashi yaiba ganin irin 'bannar da d'an nata ya aikata,domin yajimin ciyo sosai,hakadai ta daure tasani cikin ruwan zafi har kusan so uku kafin tace inyi wanka. Cikin ruwan hawaye na daure nayi wanka domin ko tsayuwar kirki banayi sosai, itama da ta kwatanci na gama tashigo dan ta lura ayadda nake. Zuwa tayi tacewa Alhaji dolefa sai an kaini asibiti domin naji rauni sosai,kuma sai ankira mahaifiyata tunda dole sai tasan halinda ake ciki. Lokacin da Mama tazo taga halinda nake ciki tayi kuka sosai na bak'in ciki da damuwa. Alhaji Zakari yacewa Mama dan Allah tarufa masu asiri kar wadda yaji wannan maganar saboda zubaiwar mutuncinsu, Mama tayi mamakin maganar da ya fad'a. Kenan idan tanason fahinta su rufawa d'an su asiri bayan su ya tona musu nasu,dayake tana zafi sosai Mama sai tace "kamar ya banganeba?" "Kamar yadda kikaji na fad'a,zan baku daga miliyan uku,hud'u ke harma biyar idan har kuka rufe wannan maganar" cewar Alhaji Zakari. "Wannan ne kuma bazai yuba,shi ya tunawa y'ata asiriba ni Kuma in rufa masa, wallahi bazai yuba" cewar Mama cikin hasala. Nanfa rikici yasu yarikice tsakaninsu saida Hajiya tace "dan Allah kuyi shiru, ayanzu ba wannan ne agabamuba,kamata yayi musan abinyi ba tsayawa cacar bakiba, kai Alhaji tunda har musan d'an mine da laifi tunda shine ta hak'ewa yarinyar,kamata yayi mu had'asu aure shine kawai mafita da rufewar asirinmu". Shiru yayi alamar tunani kafin yace "to bak'in wannan ba, amma bari atambaye shi Habib d'in idan har ya amince ni banida matsala da wannan,mafa idan bai amintaba bazanwa d'ana auran doleba". Mama da makin wannan bawan Allah ya rufe ta kasa magana, nidai ina kwance ni kad'ai nasan yadda nake jin kaina,ga kuma zazza'bi inaji sosai, Habib d'in ya kira babu jima sai gashi ya shigo kamar wadda bai aikata komaiba kansa tsaye ya huce gun mahaifinsa "Dad gani" ya fad'a abinsa game da zama kan kujera kusa dashi. Abinda mahaifiyarsa tace ya fad'a masa, yace shin ka amince a d'aura muku aure konan da sati d'aya ne?" 'Bata fuska yayi tare damin wani irin kallo mai kama dana k'ask'anci kafi yace "ni gaskiya Dad ban tashi aure ayanzuba sainan da shekara biyu zuwa uku haka" "To shikenan Son, ai abinda kakeso shi za ayi" Cikin nuna 'bacin rai Hajiya tace "banson raine wayo Habib,baka tashi aure ba amma kasan ka kama y'ar mutane ka keta mutuncinta,to wallahi maza ka canza tunani, dan auranka da ita ba fashi" Hannu Alhaji ya d'aga mata yace "dakata malama, tunda yace bai tashi ba a kyalesa mana tunda kinsan bazan masa abinda bayaso ba,taje tajirasa har lokacinda ya fad'a idan har zasu jira,idan kuma ba hakaba to su rufawa y'arsu asiri idan sunason tasamu mijin da zata aura,dan bamuba kosu idan suje sun tona har y'arsu suka tonawa tunda kowa zaisan abinda ya faru da ita,Kinga kuwa mijin aure zai mata wuya,ba kamar shiba duk lokacinda yaso auransa zaiyi abinsa, amma idan suka rufe bakinsu basu fad'a wa kowaba ba wadda zaiji ga kuma kud'in da zasu kula da kansu" Cikin k'unar rai Mama tace "bama buk'ata ko sisi daga gareku domin mutuncin y'ata yafimin wad'ancan kud'in daka anbata,tazo ta kamani dakyar ma nake tafiya saboda yadda nakeji,ba abinda ke zuba a idanuna sai hawaye na bak'in ciki, Mama itama hawayen take da wannan abin. Dayake bamuda nisa sosai ahankan muka k'arasa gida, sauk'inmu ma unguwar batada hayaniya kuma tasamin hijabin da tazo dashi dan dama da nayi wanka Hajiya taban wata duguwar riga nasa,ita kuwa d'an kwalin kanta ta yafa da yake mai dad'i ne, duk wadda yagammu d'aukar yake lafiya ce banida ita sai suyimin sannu su huce. Kuda muka shiga gida Baba na azaune yanajiran yaji ko lafiya,yana ganin mushigo yana tambayarta lafiya? bata basa amsaba sai neman waje tayi inda taga tabarma ta shinfid'e. "Wai ba tambayarki nakeba kikamin shiru? gashi sai kuka kikeyi daga ke har ita,minene yafaru da ita kika rik'on ta haka?" Cikin kuka take gayamasa komai harda abinda Alhaji Zakari ya fad'a, aiko yace wallahi bazata sa'boba dole suje su amsa kiran hukuma" "A a Mai gida,kasan ko kakai kararsu ba inda abin zaikai za ayi watse da k'arar saboda mu talakkawa ne shi kuma mai kud'i" "Kodai yayane sai nakai k'ara, kuma nasan Allah zai tsaya mana" yana gama fad'a ya fita cikin fushi. Ashe yana fita ofishin y'an sanda yaje,tu sai akasamu sa ar ya iske masu aiki da gaskiya da rik'on amana, aranar suka aikawa Alhaji Zakari da sammaci,amma baizoba d'ansa baijeba, sune suka kaini asibi akabani kula sosai, har kud'in magani sune masu saya, nadarajin sauk'i saboda kular danake samu. Alhaji Zakari da yasamu labarin asibitin da muke yaje yasa aka koremu kuma yasa gidan da muke haya maishi yace yagyara zaiyi bazamu k'ara zamaba,yaje har Jan bulo ya kama mana haya. Nandai taci gaba da gaya musu har zuwa yanzu da take tsaye anan... ~mom surayya~ [2/15, 11:29 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 16 Gaba d'aya duk wadda ke wurin shiru kamar ba kowa awajan sai jujjuya maganganun Abida ake da tsenewa Alhaji Zakari da d'an sa Habib, Alk'ali ne ya kauda shirun da cewa "idan mahaifiyar Habib na anan koto na buk'atar ganin ta?" Koda aka duba bata zoba, domin kuwa Alhaji Zakari ne da kansa ya hanata zuwa don yasan ita kad'ai ce shida,kuma ya gargad'eta da duk tasake tazo abakin auran ta,kuma zataga abinda bata ta'ba ganiba arayuwar ta,amma duk da haka yacewa masu gadi karsu sake subari tafita sannan yabar gidan. Duk da tasan halinsa zai aikata duk abinda ya fad'a amma saida tayi yunk'urin zuwa amma masu gadinnan fafur suka hanata fita saboda suna gudun karsu rasa gun neman abincin su. Data koma ciki saida tayi kuka tana musu addu ar Allah kar yasa su Alhaji suyi nasara,duk da kuwa itace ta haifi Habib a cikinta, amma an zalunci bayin Allahn nan Kuma akullun tanawa d'an nata addu ar shiriya. Gani batazoba aka gayawa Alk'ali akan bata halatta awajan ba. dan haka yace "idan akwai wata sheda daza abayar koto na saurare,idan ba wata sheda da zata tabbatar mana cewa wannan yaron Habib Zakari da shine ta aikata wannan abinda ake zarginsa da aikatawa zamu d'age wannan k'arar, har zuwa shidda ga watannan da zamu shiga,ma ana sati biyu masu zuwa". Barrister Umar ya tashi atsaye yace "ya mai girma mai shari a,akwai shedar da zan bayar bayan wadda Abinda ta fad'a akan mahaifiyar tace shedar ta,ni zan bayarda shedar da zata tabbatar mana Habib shine da aikata wannan lifin da ake zarginsa dashi" "Koto ta baka dama" Wannan recording da Maman Abida ta d'auka ranar da Alhaji Zakari yasa aka sallamesu a asibiti ne ya bayar, kunnawa kowa yaji dakyau,sai ga muryar Alhaji Zakari ta fito K'arara kowa najin irin cin mutuncin da yayi da abinda ya fad'a duja. Alhaji da yakejin fad'in sati biyu da aka k'ara sosai,dan zai samu damar da zai ku'utar da d'an sa, amma jin cewa ga wata shedar za abayar yana sairaran ko miye. Suma mutanan dake ciki saura har sun fara tsefumin cewa "dama taya zatazo ta bada kutu shedar tabbacin d'an ta shine ya ai kata, al halin wannan ba k'aramin Abu bane, amma jin wannan magana ta Alhaji Zakari ta faranta ran dayawa daga ciki aino. Gaba d'aya zufa tagama jik'e Alhaji Zakari na tashin hankali jin wannan recording d'in,kenan shegeyar matarnan tananan tana nad'iyar duk maganar da yayi aranar, takashesa tun kwannansa basu k'are ba, Allah gani gare ka. (Kamakaru Alhaji Zakari,wato saida kaga ruwa ya k'arewa d'an kada sannan katuno da Allah) Shiru wajan yayi kamar ba mutane awurin kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyar sa. Barrister Umar yaci gaba da magana yace "bisa wannan shedar da muka kawo ya isa wannan koto mai adalci data yankewa Habib Zakari hukunci dai-dai da abinda ya aikata". "Karya ne wallahi,kai baka isa k'asa ayankewa d'ana hukuncin zaman gidan yari ba, d'ana yafi karfin zama gidan yari, sannan wannan maganar batakai hujjar da har zaisa koto ta yarda da itaba" ya fad'a yana zare idanu kamar zasu fad'o k'asa. Alkali ne ya kallesa rai ad'an 'bace da maganar da yayi yace "koma ka zauna, wannan koto da kake gani bata duba matsayin mutun ki muk'aminsa, itad'in kotoce mai adalci,zata hukunta duk wani mai laifi ko wanene kuwa!". Zama tayi jikinsa na asantaye, yasan kowanene Alk'ali Abubakar,mutunne mai matuk'ar amdani da ilminsa, yana yanke hukunce dai-dai da abinda Allah ya fad'a acikin al k'ur ani,dan haka yasan kud'i ko wani abu bazasu ta'ba canzashiba. Yakalli barrister yace "barrister Umar ko akwai wata shedar dazaka gabatar?". "A a banida ita yamai girma mai shari a" "Ok kana iya zama" zama shima tayi yana addu a acikin ransa Allah ya azasu akan wad'annan azzalummai. Shiru na wasu y'an mituna sannan Alk'ali yayi magana yace abisa hujjar da aka kawo wadda take tabbatar mana da cewa Habib Zakari shine da aikata wannan lifin saboda jin bayanan da mahaifinsa Alhaji Zakari yayi,dan haka wannan kotu mai adalci ta yankewa Habib Zakari hukuncin shekara goma agidan yari tare