Sashe 38
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma?, haka dai tace suje tagayawa direba tunda safe zai kaisu, amma fa susani karfe biyar zuwa biyar da rabi zaizo ya maidosu, ahakan ma sunyi farin ciki da aka barsu, basusan komai yasaba ba bari suna dugon yawo, kuma duk inda za akaisu sai tare da wani akusa dasu, tun abin na damunsu har sukazo suka daina damuwa, har zasu huce Rukayya tace "Mansu bamuje muka gayawa Momy ba" baki Mansura ta ta'be tace "muje kawai kinsan ita momy bason wannan tafiyar take ba, yanzu zatace yawonmu yayi yawa" Rukayya tace sudai shiga, ita Mansura bason shigar ce batayi ba illa ta tsani yawan fad'a na Momy, haka ta bita ba yadda zatayi suka shiga. Ba abinda Momy tace face Allah ya maidasu lafiya tare da jamusu kunne kar su yarda ace sun aikata wani abu marar dad'i, idan kuma ba hakaba zatayi mugun sa'ba musu, tsaraba ta d'auko tace gatanan sukai nata D'auka sukayi suka fito basu ko koma part d'in Hajo ba suka shiga mota direba yaja suka tafi. Da isarsu gidan mai gadi ya bud'e musu suka shiga dan dama kafin mai gidan yafita ya gaya masa za ayi bak'i, direba nagama dai-daita motar suka fito yace shi zai koma sai zuwa lokacin da akace yazo d'aukar su sannan zai dawo, sukace ba matsala yayi tafiyar sa, k'ofar falon suka nufa suka shiga da sallamar su. Ganin ba kuwa aparlour suka sami waje akan kujera suka zauna da tunanin watak'ila matar na cikin d'aki. Kusan mintuna goma basuga alamar matar zata fitoba yasa Mansura ta mik'e dan ta dubota. Mansura da matayi tunanin wani abuba kai tsaye ta tura k'ofar da take tunanin itace ta d'akin, abinda tagani ne ya kusa d'imotata tare da ganin wani luuuuu atare ita. Sukuwa Bashhama da Jancy da sukayi nisa cikin duniyar masha'ar su kuma basuyi tunanin wani zai shigo musu ayanzuba dan haka basumayi tunanin rufe k'ofar d'akin bale parlour, saida sukaji shigowar mutun kai tsaye acikin d'akin. Gaba d'aya dabulcewa sukayi tare da jan zane sukawa suturta jikin su, Mansura da sai yanzu take dawowa haiyacin ta tayi saurin yuyawa tabar d'akin tare da rufo k'ofar da k'arfi har tanason kifa k... ~Mom surayya ce~ Typing MANSURA BY"SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 40 Ganin yadda tafito ne yasa Rukayya tayi saurin tashi ta tareta ganin da alamar ko gabanta bata gane ayadda take tafiyar "Mansu lafiya miyake faruwa kika fito haka?" Rukayya tayi tambayar itama tanajin hankalin ta na tashi. Mansura da takejin wani abu namata kai kawo tace "Ruky zo muje mubar wannan gidan minti d'aya banason nak'ara acikin sa" Rukayya ta sake tambayar tata "Kizo muje dan zan miki batanin ko minene" ta fad'a tana jan hannun ta domin jin take tamkar ak'aya take, dole Rukayya da batada wani za'bi tabi bayan ta, mai gadi ganin yadda suka nufo hanyar fita yasa ya nufo gunsu yana mai tambayar su ko lafiya?. Basuma tsaya saurarar suba suka nufi haryar gate, da sauri ya nufi gate d'in domin hanasu fita dandai tana kyautata zaton ba lafiya ba, ganin ya rufe gate d'in yasa Mansura tace "ka bud'e mana mu fita" Maimakon ya bud'e kamar yadda ta buk'ata sai bai bud'e ba saima cewar da yayi "kiyi hank'uri bud'e wannan k'ofar zaisa jamin matsala agun aikina ki bari idan har nakira mai gidan dan yabani umarnin bud'e muku zan bud'e ko tafi" mai gadi ya fad'a yana fidda k'aramar wayar sa yana danna kiran mai gidan nasa. Mansura ranta yayi mugun 'baci har idanuwan ta na rikid'a saboda 'bacin rai, rashin kunya ga nagaba faresu ba tarbiyar su bace amma yau da yaga tijara rashin bud'e musu k'ofar da yayi, Rukayya sai lalla'ba ta takeyi dan itama harga Allah batason su fita ayanayin da take ciki gashi direban nasu yariga da yatafi dan dai ba yadda zatayine. Dai-dai lokacin Mansur yad'au wayar da mai gadi ke kiransa, gaidasa yayi kamar yana gaban sa sannan yashiga fad'a masa yaran da yace zasuzo sunzo baifi mintuna goma sha biyar ba amma gashinan sun fito wane yanayi wai na bud'e musu k'ofa su fita" Mansur dake sauraran abinda mai gadi ke fad'a masa yace "karka sake ka bud'e musu k'ofar har sai azo d'aukar tasu, bari zan kira direban yanzu yazo ya maida su amma karka kuskura wata matsala ta biyo baya" mai gadi yace "zan kiyaye in sha Allah" Mansu da yakashe wayar yamaida akalar kiran ga direban gidan nasu, umarni yabasa da yaje ya d'auko su Rukayya duk inda yake, direba da saura kad'an ya k'arasa gida dole ya juya ya koma dan cika umarni. Ganin fitar tata yasa Jancy tayi saurin tambayar Bashhama da take duk tsore "Basha wacece wannan yarinyar da zata shigo kai tsaye batare da neman izini ba?" kasa bata amsa Bashhama tayi akan yanayin da take ciki saima tashin da tayi tana zura duguwar rigar ta da suka zubar ak'asa ta diro daga kan gado ta fito zuwa parlour, bayanta Jancy tabi itama aparlour, ganin bata gansuba yasa tayi hanyar fita domin tabi bayan su ta rok'esu dasu rufa mata asiri, ganin abinda zatayi yasa Bashhama tayi saurin shan gabanta tana fad'in "Basha miye haka bakya ganin yanayin da kikene waye ita wannan yarinyar?" Hawaye ne suka zuboma Bashhama afuskarta tace "Jancy bazaki ganeba wallahi ina cikin matsala zamana da Mansur yazo karshe, wannan yarinyar da kike gani k'anwar sace kuma wallahi batada kunya ko kad'an nasan tana zuwa zata fad'a wayo Allah na shiga uku Jancy kin cucene zakisa in rabo da masoyina abin k'auna ta" Bashhama ta fad'a tana aza hannu akanta. Jancy da sai yanzu ta gane bakin zaran dan haka tace kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru" Da mamaki Bashhama ke kallon ta kadinta ce "tayaya zakice na kwantar da hankalina? sai kice baki san halin da nake ciki ba!" Dariya Jancy tayi tace "Basha kenan bari kigani yanzu aiki da cikawa" ta fad'a tana komawa cikin d'akin Bashhama d'in, babu jimawa sai gata ta fito da waya akunnan ta tana magana. Ba abinda Bashhama keyi sai kallon Jancy jin wayar da takeyi, bada kowa take wayar ba sai boka tana gaya masa abinda take buk'atar yayi mata, lallai k'awar tata ba k'aramar y'ar duniya bace, ta tafi tunani saida taji tana ta'ba ta alamar tagama wayar. "K'awata ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai rabaki da Mansur sai mutuwa, wannan abin dakikaga tagani ba wanda ta isa ta fad'awa koda kuwa uwar tace, boka cika aiki zai rufe mata baki gan, ta yadda tanason ta fad'i maganar amma bazata iya fad'a ba, ko ta bud'e baki dan ta fad'a zataji bakinta ya kasa fad'in maganar, ta yadda tanaji tana gani zata hank'ura da fad'a" rungometa tayi tana fad'in "K'awata da kinmin komai aduniyar nan, wallahi bakiji yadda nakejin zuciya taba kamar ta faso k'irjina ta fito ta baka, amma yanzu naji hankalina ya kwanta" Jancy tace "ita har wacce da zata hanamu rawar hantsi, bata isa ta hanamu abinda ke nishad'ar damu, ke nifa wallahi har naji na kwad'aitu da ita dole nema inyi duk yadda zanyi na sameta" Bashhama da sai yanzu takejin hankalin ta na k'ara kwanciya "Rufama kanki asiri idan baso kike duniya tasan halin da kike ciki, ni zan gaya miki rashin m na wannan yarinyar" Bashhama ta shiga bata labarin abinda tayi mata lokacin da taje gidan, tace "dan shine ma nan dakike ganina ban koma kwad'ayin komawa gidan ba" Jancy tace "nida nakeda boka cika aiki, ai tunda na ganta na kwad'aitu dolene nabi duk yadda zanyi na sameta, kidai zuba ido kiyi kallo, zo muje dan nidai wallahi da saura idan ke kinji normal". Haka suka koma d'aki abinsu sukaci gaba da shek'e ayarsu. Mansur kuwa da take tsaye cike da takaicin abinda mai gadinnan yayi har direban ta k'araso, direban na gama shigowa bayan mai gadi ya bud'e masa gate ko gama dai-dai ta motar baiyi ba tayi saurin shegewa batare da tace kazal ba. Shiru cikin motar bamai magana aciki har suka kai gidan, Mansura ce tafara fitowa bata tsaya komaiba tayi part d'in Hajo, Rukayya itama tafito da tunin mi yafaru haka? batada mai bata amsa dole tayi gaba itama. Hajo dake zaune tana kallon BBC taga shigowar Mansura ta zauna kan kujera tare da tagumi "ke kuma lafiyar ki kika shigowa mutane haka sai kace wadda akacema wani nata yamutu" k'ala Mansura batace mataba sai tunanin wanan mugun abu da tayi gamu dashi, yanzu wannan wannan matar mai aikata 'banna adoron k'asa yayansu ya aura, inna lillahi wa inna ilaihin raji um" ita tama rasa abinda yagani ajikin wannan abar da har ya aure ta. Rukayya itama da tashigo tasamu waje ta zauna batare da tace komai ba, Hajo tace "wai ni lafiyar ku kukazo kukasani gaba da zuba wannan uban tagumi haka?" Rukayya tace "wallahi Hajo nima basan komiye ba gatanan ki tambaye ta tunda dai ni takasa fad'a min ko miye" duba Hajo ta maida gare ta tace "ke Mansura in mana bayeni mana kin barmu aduhu" Mansura da duk takejinsu amma tarasa yadda zatayi musu bayani, tun Amota takeson wa Rukayya magana amma da zarar ta bud'e baki da zumar zata gaya mata sai taji bakinta ya rufe ta kasa fad'a, ahankali ta bud'e baki tayi magana tace "bazaku gane ba" ta tashi tayi shigewarta d'aki. "Ikon Allah! abu sai kace wadda tayi gamo, kina wani cewa bazamu ganeba ke kika gane da gyatummiki" Hajo ta fad'a tana kama baki. Rukayya madai tashi tayi tabi bayan ta, zaune ta sameta tashiga damuwa, ita kuwa ba komaine yakesata damuwar ba sai yadda takeson gaya musu abinda tagani amma takasa fad'a. Zama Rukayya tayi kusa gareta ta dafata tanajin kamar tayi kuka ganin y'ar uwar tata cikin damuwa tace "Mansu dan Allah ki fad'a min abinda kika gani agidan da harkika shiga wannan damuwar, ko wani abu Aunty Bashhama tayi miki?" girgiza kai Mansu tayi tace "wallahi Ruky narasa yadda zanyi in fad'a, bansan mike damunaba, amma kibari koda gabayane zan gayamiki" Rukayya tace "shikenan amma yanzu mizamu gayawa Yaya idan ya tambaya mi yamaidami? nasan ko Ummi idan taga direba sai tayi mamakin dawowar mu yanzu" nisawa Mansu tayi tace "wallahi nima bansaniba Ruky