← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 39

Sashe 29

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganinshi atacikin mayafin, yafi ahakan, aiko kunya kamar ta nutse dan kunya dukda sa ana ganin a tacikin mayafin, cikin dubara take tura Hafsat huto, ganin kunyar da takeji ne ya hana aje mata. Cikin dubara ta vidio dake gajin haka "la Aunty gashin kine nata tanada tawa? ya fad'a tana mai shafa gashin dukin da ke kanta cikin k'eta, wadda saika nutsu k'warai zaka fahinci yadda take shafar gashin nata, ai kuwa babu zato babu tsanmani sai kawai gashin dukin ya zame yayi baya sai gashin da Allah ya bata wadda yake kamar bindin akuya, saida yasha gyara dan sai wani shek'i yakeyi alamar yasha gyara. Gaba d'aya binta sukayi da kallo gashi kuma tarekeshi ahannunta, ganin gaba d'aya idanun kuwa akanta yake yasa tayi saurin tsayar da vidion da takeyi tare da kaiwa durk'ushe tana fad'in "Aunty dan Allah kiyi hankure bansan ba naki bane shi yasa nake shafar sa har yacire amma kiyi hank'uri" Bashhama dakejin gaba d'aya ta gama muzanta da kunya acikin falon yasama ta kasa amsa mata hankurin da take bata, tasan da saninta tayi mata hakan, mitayi mata kota tare mata? zata iya rantsuwa da Allah bata ta'ba ganin ko mai kama databa bale har tayi tunanin wani abu yata'ba yad'ata da ita, yarinyar da ahaihuwar awaki zata haifeta itace ta mata haka, kai dulene ma yarinyar nan tagane batada wayo duk ranar da tashigo gidan, hawayen ne suka zubo mata afuskarta na bak'in ciki. Ganin ta kasa ko mutse akan kujerar yasa momy ta k'arasa gunta ta zauna bisa kujera tana fad'in "yi hank'uri kinji 'yata halin Mansura ne sai ita amma in sha Allah zan hukunta dai-dai gwargwado kuma shima mansu zaiyi nasa idan ya dawo dan nice nan zan fad'a masa" ta fad'a tana d'ago kanta,ganin hawaye gaba d'aya sun 'bata mata fuska yasa tace "kuka kuma? kinga share hawayen ki kinji hakan bazai sake faruwaba" tana gama fad'a ta jiyo kan Mansura tana watsa mata wani mugun kallon da saida yasa cikin Mansura ya hautsina,domin tasan halin Momy sarai ba kanwar lasa bace,amma sai tadakewa ranta komai za ayi mata aitadai goge kaso sabain na takaicin abinda yayi mata ehe, tashi tayi daga wajan da take kar Momy takai mata mazga daganan, wurin firjin ta k'arasa tasaki vidion ta ajiye ta yadda zaici gaba da d'oko mata komai dai-dai sannan ta dawo kusa da Hajo ta zauna, jinjina Hajo tayi mata da babban yasta alamar tayi dai-dai, murmushi itama tayi tare da d'aga mata gira sama. Juyawar da zatayi idanuwan ta suka sauka akan rezar da Hajo tagama aiki da ita da dukkan alamu ta mance da ita ba d'auketaba, wani makirin murmushi ta saki tana fad'in haka cikin ranta "humm 'yan mata ba'afa gamaba, zakisan kin shigo gidan kura mai jiran nama d'anye basai gasashshe ba. Gefen da suke ta kalla har yanzu Momy hank'uri take bata itako tana sharar hawaye, matafenta ta d'auko ta yafa mata akan nata, hawayen fuskarta ta share tace "zanje gida" "To shikenan ba damuwa zakije kinji" kai ta d'aga alamar ansawa amma ta kasa d'ago idanunta ta kalle kuwa na wajan. Tasuwa Mansura tayi tare da rezar dake hannubnta ta k'araso gunsu tare da duk'awa tace "Aunty dan Allah kiyi hank'uri wallahi bada sanina hakan tabfaruba, kiyi hank'uri karkije da fushina" tsawa Momy tadaka mata "Mansura idan baki matsa daganan ba zan sa'ba miki" tashi tayi tana zama kan kujera tana fad'in "ni Allah Momy bazan tashiba sai ta hank'ura,ai Aunty nace, Aunty na ai kin hank'ura ko?" Badan kan idanuwan kowa akansu ba abinda zai hana ta gallarawa yarinyar nan marin dasai ta mance waye ita ba, amma ba komai taci bashi, kai ta d'aga mata alamar ya huce, rungometa tayi sosai tare da fad'in "amma nagode Aunty na,daga yau banida wata Aunty da ta huceki" Ummi tace "ina zuwa" sai itama Momy ta bi bayanta tare da fad'in Bashhama ta jirata suka fita. Suna fita Momy tace "Yaya Kinga abinda wannan yarinyar tayi ko? wallahi kwata-kwata banji dad'i ba kan abinda tayi mata" dariya Ummi tayi tace ani tayimin dai-dai wallahi,inaganin harda goro zan bata na wannan abin da tayi,wace yarinyar arzik'i ce zatayi wannan shigar da sunan zatazo gaida surukkai?" "Koma miye ai bai kamata tayi mata abinda tayiba Yaya" dariya tayi tace "nidai bari naje na bata abinda zan bata Allah ko ganinta banasonyi" itama Momy dariyar tayi tace "Allah kima watarana bakida dama Yaya" nandai kuwa yayi part d'iita domin d'oko abinda zata d'oko. Mansura kuwa tana ganin fitar su Momy tayi saurin tashi itama tayi warin firjin da ta aje waya ta tsaida,saida tayi kamar ruwa ne zatasha ta faki idanunsu ta tsaida,ruwan tasha sai ta huce kucin kamar wadda zatayi wani abin alhalin ba uwar da zata tsinana aciki, saida taji sallamar su sun dawo sannan ta fito, ko wanensu ledace a hannunsu wacce ke nuni da starabace suka mata, saida ta saki vidion sannan tazo wajan da ta tashi ta zauna, ledar suka bata suna cewa gashinan in taje ta musu tsaraba, godiya tayi musu tare da mik'ewa tsaye alamar zata tafi, Hajo ta tsaidata dacewa itama tana zuwa dole ta tsaya, da wannan damar Mansura ta samu tayi ta bayanta tasa rezar nan ta yanka mata bayan rigar dai-dai ta d'uwawonta, ahankali take tafiyar da rezar har tsagon yayi d'an tsawo sannan tayi baya kamar ba ita bace ta aikata. Hajo na fitowa itama ta bata ledar tsarabar ta tayi mata godiya sannan tace zata huce idan su Dady sunzo tana gaida su. Saida suka fara takawa har sunkai bakin k'ofa sukaji salatin Hajo dake bayansu "innalillahi, ni d'iyar salame mizangani ni yau haka?" dukansu juyowa suka ganin miye wakeyiwa kalimar haka, ganin basuga komaiba suka maida dubansu gareta suna tambayar ta maiyafaru?, Mi kuwa ya faru kudubamin wannan yarinyar haka ta biyo hanya tsirara!" ai kuwa dukkaninsu idanuwan suka zuba mata,ganin rigar ayage har ana stinkayar bak'in wandonta da tasanya wadda iyakacinsa gwaiwa, Momy ce tayi saurin kiran "yaya haka ko baki lura da yadda rigar takebane kika sanya?" Bashhama da takejin wani abu yayi mata tsaye amak'ogaro ya gagara hucewa sai dak'yar ta fisgo magana tace "wallahi lafiya kalau na san yata hasalima yau na fara sanyata, bansa ya haka takasance ba" Momy tace "to shikenan kwantar da hankalinki inaga wurin zamane rigar ta yage, ke Rukayya aje kayan dake hannunki kije ki d'auko mata hijabina ki kawo tasanya yafi tafita ahaka" Rukayya ta ajiye kayan data kar'barma Bashhama da zasu fito taje aikar Momy, Hajo kuwa ta kama fad'in "Dan Allah miye amfanin wad'annan kayan da zakaje zama su yage,kana takura kanka abanza shed'ar k'warai sai ka kasa saboda tsabar takura kai" Mansura dai da tayi seved vidion ta sai dariya take na farin ciki sannan ta biyo bayansu. Rukayya da takawo hijabin Bashhama ta mik'awa ta amsa cikin jin kanta wata iri ta Sanya sannan suka fita daga cikin falon. Sai kuma mi annemi takalmita d'aya sama ko k'asa ba agansaba, abin ya d'aurewa kowa kai na rashin ganin takalman. Bashhama dai bak'in ciki kamar ta had'eye zuciya,itadai zuwa wannan gidan bai k'areta da komaiba sai wulak'anci da k'ask'anci harma da tozarci, wanan abin dami yayi kama. Duk ma aikatan dake harabar gidan saida aka tambayesu amma ba wadda yace yagani. dan gaka akace suduba gaba d'aya filin gidan agani ko za aganshi. sunanan jiran tsanmani sai ga wadda ke bawa fulawoyin gidan ruwa yazo dashi ahannu yace acan ya ganshi cikin fulawoyin, kar'ba a doc tayi tasa amma rannan nata duk a'bace, rakata sukayi har wajan mota sukayi sallama ta tayar da mota ta fice agi... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 30 Tafe take amota tana sharar hawaye, tunda take aduniya ba ata'ba tizartata irin wannan ba,tayi danasi zuwanta gidannan yafi ak'irga,da tasan da wanan tozarcin da tayi zamanta lakacinda yace basai tajeba,amma tayi ta magiya da rok'o har ya amince mata, to ga zuwan nata abin da yajanyo mata, tanajin lokacin da wayar ta ke ringing amma ko kallon wayar batayi ba bale har taga mai kiran nata, Allah ne kawai yakaita gida lafiya. Taci sa'ar ba kowa afalon dan haka tayi saurin shigewa cikin dak'inta kafin Momy taganata da shigar da bada ita tafitaba, kuma tasan tambayoyine zata shasu wad'anda batasan mizata fad'a ba. Mansura tunda ta shiga ciki kai tsaye d'aki ta shiga dan taji anfara kiraye kirayan sallar la'asar, tunda tagama ta koma saman gado sai murmushi take, yau zuciyar ta fes take saboda abin da tayi,da ta tuna lokacin da take furzar da ruwan da tasha sai taji dariya tazo mata har k'yak'yatawa take "kai mata sunji jiki Allah kuwa" ta fad'a tana mai k'ara fashewa da dariya. Rukayya da tashigo ta tsaya tana kallonta ganin tana dariya itakad'ai sai kace zararriya ko wata sabon kamu "Ke lafiyarki kalau kuwa? wannan wace irin dariya ce haka?" Mansura da sai yanzu ta lura da ita ta tak'aita dariyar tata dare da cewa "sister bazaki ganeba, wani comedy ne idan na tuna dashi yakesani dariya" tana mai k'ara fashewa da wata dariya da ta tuna lokacin da ta cire mata gashin nata. "Ni dama wallahi nasan du wad'anna abubuan dake faruwa da saninki, yadda naga kina sakin wni makirin murmushi wadda duk wanda yasanki bazai yarda dashiba"Rukayya wacce ke k'arasa shigowa cikin d'akin ta fad'a, zama tayi tare da fad'in "amma dai kinsan baki kyuta mataba, bai kamata tazo mana matsayin bak'uwa kemata wannan abubuwan ba gaskiya" Mansura tace "Kinga! bazaki zo ina cikin farin ciki ba ki'bata min shiba, idan bazaki goyamin bayaba akan abinda nayiba sai anjima kiyi tafiyar ke, barima kigani inje in gwadawa Hajo vidion da nayi nasan ita harma tukwici zata bani" ta fad'a tana tashi tayi falo, hakan yasa itama Rukayya tabi bayan ta. Afalo suka tarar da ita wacce itama yanzunnan take fitowa tunda tashiga sallar la'asar ko zama batakai gayiba, Mansura tace "Yauwa Hajjajo zauna na nunamiki wani comedy zakisha dariya" zama tayi dare da fad'in "wannan wane irin abune za agwadamin aketa sakin murmushi?" Rukayya ma zama tayi agefen Hajo dandai itama tanason k'ara ganin komai, wayar Ummi data 'buye ak'ark'ashin filon kujera ta
Chapter 29 · 0% Book details