← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 39

Sashe 19

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da horo mai tsanani,sannan kuma da tara ta naira miliyan d'aya" ya buga guduma tare da mik'ewa. Hannuwa biyu Habib ya aza akai tare da fasa k'ara yana ihun "Dady ka taimakeni" shima Alhaji Zakari duk yabi ya rud'e akan hukuncin da aka yankewa tilon d'an nasa. Mansur kuwa handala sukayi ga Allah da gode masa,Maman Abida kuwa harda sujudar shikur tayi hawaye na zuba a idanuwanta. Abida ba abinda take sai kuka,kuka takeyi har na fitar hankali,gashidai hukuncin da aka yanke abin tayi farin ciki ne, amma ina takasayin farin ciki,saboda duk hukuncin da aka masa bazai dawo mata da martabartaba har abada,idan ta tuni da hakan zuciyar ta na k'una. Jabir ne ya lura da kukan da takeyi ya k'arasa wajanta yana lallashin ta, kausar ma tazo ta kamata tana bata hank'uri, da cewa " kamata yayi tayi farin ciki ba kuka ba,kuma kuwa da irin jarabawar da Allah ya k'addara masa, shin bataga abinda ya faru ayau d'inan bane Kuma a kotun nan? uba fa mahaifi yawa 'yar cikin sa fyad'e, shin ita mizatace da tata k'addara?" Hakadai suka lalla'bata suka fito daga ciki,mutane sai tayasu murna sukeyi, mota suka shiga I sukayi gida, kai tsayi can gidansu Hajo Mansur ya umurce Jabir yayi dasu,saboda yasan Alhaji Zakari sari zai iya aikata musu wani abin. Hannu biyu Hajo ta tarbesu tare dasa a ajiye musu kayan abinci dana sha,bayani yayi mata yace yanason su zauna konan da wata biyu ko uku kafin su koma, "abasu d'akin da Baba Ilya ya zauna da iyakinsa har zuwa lokacin,tunda shi ya maida iyalin nasa can kauyan nasu". "Ba komai mai sunan Malam, ai ko anan kace su zauna har abada ba maice maka danmi?, kar kadamu kanka nasan iyayan nakama zasu amince" "Nasan da haka, danshi nace aisuzo nan su zauna dan nasan banida matsala akan wannan" Godiya sosai su Maman Abida sukayi da wannan karancin nasu,amma fa sun kasa cin komai da aka ajiye musu,gara ma itama Maman Abida tasha ruwa,amma ita abidar ko ruwa kasa sha tayi saida Hajo tayi dakyal sannan taci kad'an koshi badan dad'i ba. Hira suka d'an ta'ba kafin Hajo tace "waini mai sunan Malam yaushe zakaje ka dubo yarannan?' kai bakajeba Kuma ka hana muje, aidai yanzu nasan ko miye sun dangana tunda sun saba,yakamata muje mugansu muga halinda suke acikin,dukda kace kana waya da shugaban makarantar tasu, amma baikai mu mujeba,hankalinmu zaifi kwanciya" "Kar kidamu Hajo zanje idan nasamu dama" "Har zuwa wane lokaci zakasamu wannan damar? koda yaushe haka kake fad'a" Cikin satinnan zanje in sha Allah" "To shikenan Allah yasa" Jabir ne yace "amin Hajo,in sha Allah nida kaina zansa yaje,tarema zamuje dan in tabbatar,kar yaje ya la'be yace yaje" Dariya duk sukayi, shi kuma Mansur ya hararesa. Washe gari Washe gari da safe misalin 11 am Mansur yayi kiran Abida, bayan tazo anan falo ta tarar dashi,bayan ta gaidasa yace ta zauna akan kujera. Bayan ta zauna yace "Abida inason in yimiki wata 'yar gajeriyar nasiha ce,inason ki saurareni da kunnuwan basira". Tace "to Yaya" "Ba wani Abu bane kawai inason k'anwata mai daraja". "A wannan shekarun naki, zuciya tana da saurin bugawa ga abin da take so, kuma kalmar "soyayya" akwai da in ji. Amma a cikin soyayyar zamani, akwai tarkuna da yawa wa anda samari marasa tsoron Allah suke amfani da su. ga wasu shawarwari da za su zame miki garkuwa" "Ki San Darajar Kanki: Darajarki ba ta cikin jikinki ko kyawunki tana cikin hankalinki, tarbiyyarki, da kuma burinki a rayuwa. Kada ki bari wani saurayi ya rage miki daraja ta hanyar mai da ke tamkar abin wasa. Ke 'ya ce mai daraja, 'yar'uwa mai kima, kuma wata rana za ki zama uwa abin alfahari. Duk wanda bai ga wannan darajar ba, bai dace da ke ba" "Bambanci Tsakanin Soyayya ta Gaskiya da Sha'awa Kawai" "Soyayya ta Gaskiya: tattare da ha uri, tana son ci gabanki, tana mutunta iyakokinki, kuma tana son kusantar Allah da ke. Saurayi mai sonki da gaske zai so ya san iyayenki kuma ya biyo ki ta hanyar da ta dace" "Sha'awa Kawai: tattare da gaggawa, tana son biyan buk'ata, ta fi mayar da hankali kan jikinki, kuma kullum za ta nemi ki keta dokokin Allah. Tana cike da arya da alkawuran da ba za a cika su ba" "Kula da Wad'annan Alamun Hadarin (Red Flags Idan saurayi ya fara nuna aya daga cikin wa annan halayen, ki yi hattara" "Matsa miki kan maganar banza, idan kina sona da gaske, za ki bani?, wannan ita ce babbar alamar k'arya. Soyayya ba ta bukatar hujja ta hanyar sabon Allah" "Neman hotuna ko bidiyon tsiraicinki: Wannan babbar illa ce. Da zarar kin tura, kin rasa iko da shi har abada. Zai iya amfani da shi wajen yi miki barazana (blackmail) ko ya watsa a intanet idan kun rabu. Intanet baya mantuwa!" "Baya son a san shi a wurin 'yan'uwanki: Idan da gaske yake, zai so kowa ya san shi. Boye-boye alama ce ta rashin gaskiya" "Yana fushi idan kika ce "A'A": Saurayin da yake sonki da gaske zai mutunta ra'ayinki da iyakokinki. Wanda baya so, zai nuna bacin ransa idan bai samu abin da yake so ba" "Jikinki Amana Ne, Ba Filin Wasa Ba: Allah ya ba ki jikinki ne a matsayin amana. Bada shi ga wanda ba mijinki ba zunubi ne babba wanda zai iya barin tabo a ranki har abada. Zai iya haifar da cututtuka, ciki maras so, da kuma `danasanin da babu amfani. Karshensa kuma, saurayin zai guje ki ne ya bar ki da wannan nauyin ke ka "Ki Zama Mai Manufa a Rayuwa, Kada ki bari soyayya ta zama ita ce abu aya a ranki. Ki mai da hankali kan karatunki, sana'arki, da kuma gina rayuwarki. Idan kina da abin yi, ba za ki samu lokacin sauraron masu bata lokaci ba. Namiji na gari zai so mace mai hangen nesa" arshe, Soyayya abu ne mai kyau idan aka bi ta hanyar da ta dace. Kada ki bari gaggawa da rudin zamani su sa ki fa a a tarkon da za ki yi `danasaninsa a rayuwa. Ki zama sarauniya, ba 'yar wasa ba. duk saurayin da ya bukaci ki sadaukar da mutuncinki da addininki don soyayya, to wannan ba soyayya ba ce, yaudara c... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:30 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 17 Shiru tayi sai hawayen dake zubu mata afuska har suna saukar mata kan hijabin dake jikin ta, amma ta kasa sharesu. "Ba kuka zakiyiba!, Na fad'a miki hakanne saboda kar soyayyar zamani ta rud'aki, kiga tunda wannan jarabawar tasa kiga kin rasa duk wata kimata take kice zaki biyewa sharrin shed'an, kar kije kisa damuwa aranki har kije ki janyowa kanki wani ciyo daban" yayi shiru yana kallon ta. Sannan yaci gaba da dad'in Allah bazai ta'ba kamaki da wani laifiba tunda ba ason ranki bane abinda ya faru, amma mundin kikaje kika aikata da saninki Kuma dason ranki, to kisanin kinjawa kanki zunubi ne mai tarin yawa" Cikin kukanda har yafi na farko tace "in sha Allah Yaya bazaka ta'ba samuna da kwatan-kwacin hakaba, wannan ma k'addara ce da tariga fata,domin nasan irin azabar da Allah ya tanadarma duk wani mazinaci da bai tubaba ya komawa Allah ba". "To shikenan Allah yayi miki albarka,ya kuma za'ba miki miji nagari, tashi ki shiga ni zan fita" Asaman lab'banta ta asa da amin, tare da mik'ewa ta koma ciki. Rayuwar makaranta rayuwace wadda su Mansura zasuce su gaba d'aya basusan wahalal taba, sun maida hankalinsu ga karatunsu bamaijin kansu,wasuma d'auka suke sud'in y'an biyu ne,tsakaninsu dasu Asma u ma sai sau barka domin kansu ahad'e yake, agefe guda ga kuma Auntyn su hauwa, duk da itakan ta damu da rashin zuwan yayan nasu,domin harga Allah tana matuk'ar son ganin nasa, kala tana tambayar yaushe yayansu zaizo? hardai ta hank'ura da tambayar tasu,ita ganin takeyima su basu damu da rashin zuwan wani nasundon ya dubasu, amma hakan baisa ta hank'ura da basu kular da tasaba ba. Cikin dare Mansura ta tashi da matsanancin ciyon mara wadda har yakaita ga fita cikin haiyacinta, Rukayya itada su Asma u duk hankalinsu ya tashi sun rasa yadda zasuyi gashi dare yayi, dan yauzu akalla karfe 2:30am, gashi sai dafw marar take tare da suntse idanu, har yi take tana kamar wani sank'amewa. Rukayya ce tace "yanzu ya zamuyi? ko zamuje mu fad'awa Aunty Hauwa? kunga yadda dai take wahala" "Eh to gaskiya yakamata mu sanar da wani dan gaskiya abin yabani tsoro, amma to wai ta ta'ba yin hakane?" cewar Asma u. "Gaskiya bata ta'ba ko kwatan-kwacin hakaba ko lokacin da muke gida" Zainab tace duk ba wanan ba musan abinyi kunga yaddafa takeyi" tafad'a tana nuna musu Mansura wadda ke sank'amewa kamar wadda zata suma. Gaba d'aya hankalinsu ya tashi cikin sauri Asma u ta tashi ta fita daga cikin d'akin har tana yin tun tu'be. Babu jimawa sai gashi ta shigo tare da Aunty Hauwa dagani itama hankalin nata atashe yake, ganin yadda takene yasa tace dole sai ankaita asibiti ayanzu tunda kafin safe basusan abinda zai faruba, alokacin suka fita itada Zainab dan yanzu uku ta kusa, asibitin dake makarantar suka nufa, sun iske nurse d'inda basuyi baciba suka fad'a musu. Suma ganin yadda suke hankali tashe sukace suje,koda suka isa cikin d'akin sun iske ta suma su Rukayya sai kuka suke,dansu aganinsu ta mutune, jiki sanyaye suka k'arasa ciki Aunty Hauwa na tambayar su Lafiya mi yafaru? Asma u ce tace "Aunty Hauwa Mansura ta mutu tabarni,wayyo ni Allah". Nurse ne sukayi saurin k'arasuwa tare da dibata, Rukayya tace "da gaskene abinda Asma u ta fad'a? dan Allah kar kicemin hane domin k'wa-kwalwata bazata ta'ba iya d'auka ba". 'Dai daga cikin sune tace muma bazamu tabbatar ba sai muje can sannan musan halinda take aciki, amma ji kwantar da hankalinki in sha Allah abinda muke zato bashi bane" kasama magana tayi sai gyad'a musu Kai da tayi idanunta na zubar da hawaye. Koda suka k'arasa taimakon gaggawa suka shiga bata, sun gane dugun sumane tayi sakamakon wannan ciyon mara,koma ba komai bane ya haddasa matashi sai girman dazai kamata, Kuma baima riga da yazoba. Saida aka kira Aunty Hauwa aka mata
Chapter 19 · 0% Book details