Sashe 25
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsoro take da tunanin wane irin hukunci zai aikara agare su, basudai bisa cikin d'akiba suka tsaya nan afalo dan gudun yin wani laifi, kusan mintunansu goma anan tsaye kafin ya fito yana musu wani banzan kallo kafon yace "kumin kamun kunne na mintuna talatin,sannan kuje ku gyaramin d'akina na nan da na part d'in Hajo,ku wankemin bayi banason inga wani kuskure, sakamakon haka kuwa hummm" ya fad'a yana zama bisa kujera. Mansura da tunda ya fara maganar kamun kunne taji kamar ta aza hannuwa bisa kai tafasa ihu,cikin abubiwan data tsana arayuwar ta harda wannan kamun kunne aciki,tuni Rukayya ta kama kunnenta dan wlh bayan wannan batason yasata wani abu. Mansura nanan atsaye tana shawarar yadda zata kama kunnan nata abazata taji mari afiskarta,marin da ya tafi da ganinta na hucin gadi,batasan lokacinda takai zuk'unneba saboda tsabar jin wannan marin da tayi. "Zakitashi kiyi abinda nasakaki kosai nayi k'asa-k'asa dake?" jikinta har rawa yake ta kama kunnan nata, Allah wannan marin idan tayi saken da ya sake mata na biyu sai buzun ta ba itaba. Laptop yaje ya d'auko yaje kan kujera ya fara danne-dannansa na dama, k'afafuwansu tuni sun fara rawa shi kuma da alamar kamar ya manta dasu dan sai aikin gabansa yake,saida yaga dama sannan ya d'ago kansa yacewa Rukayya ta tashi, tashi tayi tana mai hamdala acikin zuciyar ta, daurewa ne kawai take, tasan bak'aramin aikin sabane yaga takai zuk'unneba yace sai tadawo baya, da tatashi har k'afafuwanta takejin sunasun gagara d'aukar ta amma take k'arfafa kanta. "Kije ki gyaramin part d'ina dake 'bagaran Hajo, karki kuskura inga ba dai-daiba" cikin rawar baki tace "to Yaya" tana juyawa zatafi har tana tuntu'be. Hawaye ne suka zubuwa Mansura afuska, "eh dole yace ita ta tashi saboda ita k'anwar sace dasuke uwa d'aya, nifa? bak'in mugu kawai" "Ke" yakatse mata tunanin da take na zuci, d'ago kanta tayi tana kallon sa, da hamnu ya mata alamar ta tashi, taahi tayi tana rik'e kunkurunta da takejin yarek'e gaba d'aya, tashin da zatayi sai tajita k'asa k'afafuwanta sun kasa d'aukar ta, hankalin sa yana akan laptop da yake danna yaji fad'uwar abu k'asa, da mamki yake kallonta ganinta kwance ak'asa "ke miye haka? zaki tashine ko sainazo nayi k'asa-k'asa dake" tashi tayi dak'yal hawaye na zubu mata sai kace an bud'e fanfu. Ko tausayinta bai ninaba yace "shiga bedroom ki gyara bayin shima ki gyara, sannan kizo nan falon ki gyara, saura kuma inga ba dai-daiba" Idanuwan ta dake zubar hawaye tana sharewa ne suka k'ara zubuwa "amma gaskiya Yaya nawa aikin yafi na Rukayya yawa tunda ita bada falo zatayi guranba, ni gaskiya daka had'amu muyi gyaran tare" Da mamaki yake kallon ta,wai yarinyar da aka haifa akan hannuwansu itace agabansa yace ga abinda za ayi itako tana cewa ga abinda za ayi, lallai wuyanta ya isa yanka ya rik'a, baki ya bud'e yace "sonkine banayi ita nakeso ko kinada hukuncin da zakiyi? batace komaiba amma yaga lab'banta na mutsawa alamar akwai abinda take fad'a, baice komai ba ya tashi ya nufun gunya, ai tana ganin haka taja k'afafuwanta dayakejin sund'an mata dama-dama ta fad'a cikin d'akinsa da sauri, k'wafa yayi yana komawa wajan zaman sa. Mansura tana gyaran d'aki tana zaginsa buhu-buhu,amma ta tsaya nutse tayi gyaran k'arai,domin yasanma idan batayiba idan zata kwana wajannan sai yaga yayi masa yadda yakeso sannan zai barta,ta gyara d'akin taje bayi shima ta gyara,ko ina yayi tas amma tak'i sanya turare acewar ta baice ta sanyaba,saida taga yayi ba inda alamar datti yake sannan ta fito gyara falon. Har zuwa yanzu yananan yana aikinsa na fama wadda da dukkan alamu akwai wadda zaici zalinsa tunda anan yafi k'warewa yancin zalin mutane, tsaye tayi batace komaiba,shi kuwa dukda yaji tsayuwarta amma ko d'aga kai baiyiba bale har ya nuna yasan da alamar mutun awajan, kusan mintuna biyar ganin itace zata 'batawa kanta lokaci tace "na gama" K'ala baiceba ya d'au laptop yashige ciki,da harara tabisa k'asa-k'asa tace "mugu mai bak'in hali,ba abinda ta aje saicin zalin bayin Allah" sarai yaji abinda ta fad'a,dan Allah ya horemasa saurin ji kamar maciji amma ko waigowa baiyiba yayi tafiyarsa, sauri-sauri take tayi tayi ta gama ta gudu tun bai fitoba, ta kammala kenan har takai k'ofar falo sai ta tsinkayin muryarsa "ke! mi yahanaki sakamin turare? kin d'auka kuwama irinkine k'azami, eye?, maza je kisakamin turare" Kamar wata marar gaskiya ta kama ganyar d'akin, duk turaran da tagani fesashi kawai takwyi dan k'eta, na d'aki da wadda bana d'akin ba, har yana hawankai, tana gamawa ta fito,batace komaiba tabi hanyar fita,saida takai bakin k'ofa sannan tace "Allah dai ba azzalimin bawa bane" tana gama fad'a taba k'afafuwanta iska,girgiza kai kawai yayi ya koma ciki. Tana shiga bata tsaya ko inaba sai kan Hajo ta haye mata k'afafuwa tana sakin haki, "Lafiyarki kuwa kike wannan gudun sai kace wacce mugun abu ya biyuki" gyara kanta tayi dake kan Hajo tace "mi yarabashi da mugun abin, ace shidai arayuwar sa idan baici zalin mutun ba bayajin dad'i" "Hummm kedai Mansura bakinki shine maija miki akoda yauahe, kema kinsan duk laifinku, ace ga lokacin da zakudawo kukama waje kuyi zaman ku harda maida direba kice za amaidaku,itama Asma u da itama hankali bai gama shigar taba ta barku,aini yamin dai-dai dama yasani yak'ara da duka" Tashi tayi zaune daga kwanciyar da take kan k'afafuwanta tace "ai dama nasani bazaki ta'ba ganin laifinsa ba,kuma wallahi baco bilis ba ko yaushene sai na rama" ta fad'a harda cije baki, tana gama fad'a ta tashi ta shiga cikin d'aki. Bata tarar da Rukayya ba ga dukkan alamu bata 'bangaran,ban d'aki ta shiga ganin an fara kuraye-kirayan salla, wanka ta fara sannan ta d"auro alwalla,koda ta fito har antayar da salla,dan.haka mai kawai ta shafa ta zuba duguwar rigar ta ta tayar da salla. Bayan ta gama tafito ko Hajo bata kallaba dake kan sallaya anan falon gaba ayi ficewar ta, 'bangaran Ummi ta nufa kai tsaye, bata sameta anan falon ba sai tayi hanyar d'akin ya,kan sallaya ta tarar da ita tana lazimi, zama tayi abakin gadonta tajira ta gama. "Mansura sarkin shiririta andawo?" baki ta turo gaba d'aya tace "yanzu Ummi nice sarkin shiriritar?" "To Mansura idan ba shiririta ba kuda akace kudawo da anyi la'asar zaku samu waje kuyi zaman ku" ina shi Yayan naku yake... ~mom surayya~ [2/15, 11:32 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=wwt Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 25 "Yanzu sabida Allah ace duk inda zamun sai asamana lokacinda zamu dawo, harda yannan namu baza abari muje musakata mu walaba" "Nidai ba wannan na tambaye kiba, ina yayan naku yake?" "Yana ina kuwa bayan yanacan inda yasaba ajeyemu yanacin amanar mu, kuma wuta balbal dan bazan yafeba" Murfin dake gabanta ta d'auka zata jefa mata,ita kuwa ganin haka da tayi,sai tatashi ta gudu, "daki tsaya kiga, idan ban fasa bakin raahin kunya ba, kuma bari mai sunan to yazo,sai nace masa idan akayi hutu yabarku acan makarantar sai kun gama gaba d'aya" Da yake bata gama fita gaba d'aya ba,sai ta d'an dawo baya kad'an tace "idan kinga dama kicemasa idan ma mingama yabarmu acan ko mun gama,ai dama ba sonmu yakeba,Kinga sai yazuba ruwa ak'asa yasha" tana gama fad'a tayi tafiyar ta. Hajo da mamaki take kallon ta har tak'arasa fita gaba d'aya, lallai ta yarda kuma ta amince wannan makarantar ba karatu kawai suke koyaba harda rashin kunya, nari mai sunan Malam yazo, yaskiya bazasu komaba kar nan gaba suzo sufi k'arfinsu,dan itama Rukayyar ba bayaba, tsoro ne kawai ke hanata wani abin. Mansura kuwa tana fita inda Maman Abinda take zama itada mijin ta ta nufa, samunsu tayi zaune akan tabarma su duka ukku sunacin abinci, Baba ne yace "A lallai munada manyan bak'i,'yar gidan Hajo kece? ina Hajo da uban masu gida?" Zama tayi kan tabarmar kusa da Mama tare da gaidasu,sun amsa cikin farin ciki wadda yake nuna suna matuk'ar sonta sannan tace "nice Baba yaudai nace anan zanyi firata" cikin nunajin dad'i yace "kin kuwa kyauta 'yar gidan Hajo, zo mik'arasa cin abinci tare idan anyi sallar ishsha sai mizauna wajan firar" babu musu taje ta wanko hannun ta ta zauna sukaci abincin, bayan sun gama tace "Allah Mama abincin nan yayi dad'i zanzo ki koyamin" Mama tayi dariya tace "Mansura banibace zan koya miki Aunty kice ga kinan gata, sai ki tambayeta" dubanta takai wajan Abida tace "Ai Aunty nasan zaki koyamin kafin in koma makaranta ko? Allah inason koyon wannan abinci, amakaranta basa koya mana irin wannan, anan kuwa Momy nayi saidai fad'an ne banaso, kinsan Momy akwaita da Fad'a, Hajo kuwa su Abba sun hanata aikin komai nasan da zata koyamin" Duk saida sukayi dariyar zancanta, Mama tace "inbada abiki Mansura,ai dan tana k'aunar kine take miki fad'an dan ki maida hankali,kuma Kinga ko Ummin ko zata koya miki" baki ta kama tare da fad'in "Kai, Mama kinsan fad'an Momy kuwa? ai duk gidannan ba wadda yakai fad'a da saurin duka irin Momy da Wannan mugun mai bak'in hali" dariya sukayi Abida nacewa "waye mugu mai bak'in hali Mansu?" "Yaya Mansur mana, shi inba cin zalin ba abinda ya aje, kuma wallahi sai na rama akan 'ya"yansa duk lokacinda ya haihu" Abida tace "lallai bakida ta ido Mansu,yanzu agaban nawa kike cewa yayana mugu mai bak'in hali,to tabbas assalatu zatako walwale dan bazan koya miki wannan abinci ba" Saurin matsowa tayi wurin Abida jin bazata koya mataba, tace "haba Aunty ta takaina, kinsan nidake bata galan,nasan bazaki k'i koyawa 'yar k'anwar kiba, dan kinason in zamo sufa wajan iya abinci" "Daina min wani dad'in baki kike, matuk'ar kina kiran Yaya da wannan sunan bazamu shirya dake ba" "Naji na tuba bazan sake ba, zaki koyamin ay?" Hannun ta ta janyo tace "naji zan koya miki harma kizo kifini iyawa,kinga sai d'aliba tafi malamar ta iyawa" Rungometa tayi ta fad'in"yauwa Aunty ta taina Allah ya barmu tare" kiran sallar ishsha ne ya tadasu, Baba ya wuce masallaci sukuma sukayi anan, bayan sun gama sukaci gaba da firar su Mansura na basu labarin makarantar su sukuma suna dariya, basusan likaci yajaba saida Baba ya shigo,dan tunda yaje masallaci bai dawoba yanacan wajan mai gadi suna fira abinsu, cewar da yayi "y'ar gidan Hajo ananan har yanzu,baki lura da