← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 39

Sashe 16

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tundaga wannan fad'an kowa yashiga taitayinsu akan Mansura dan sun gane jidalallace akayi awajan. 'Bangaran su Hajo kuwa suma basuda wata matsala,ayanzuma sai sukejin gidan shiru saboda ba 'yar bari agidan da dukan yara, Hajo har kitan takeyi "ita yanzu bakinta har wari yakeyi saboda rashin magana,ita wallahi an cuceta na d'auke mata Mansura da akayi" Khadija ce awajamta itako ba ma'abuciya surutubace, yanzu batada aiki sai idan tagaji da bacci taje 'bangaran Ummi ko Momy,takanci ita bazata iya da harakar korameba, "Allah dai ya gwada mata Mansura tagama wanan karatun baturan tadawo gida su zauna". Idan tana fad'in wannan maganar idansu Momy nakusa saukance "toke Hajo ai Mansura 'yar gidan wanice tunda ba anan zataci gaba da zamaba aure zatayi" Itama sai tamaida musu da amsa ai Mansura atare zasu zauna gidanta domin taga irin zaman da zatayi kar acutar mata da jika" idan ta fad'i haka saidai suyi dariya suce "gasu gani ide 'ya'yan zamanine ita da kanta zata janyo k'afafuwa tadawo". Mansur ya dawo gida duk agajiye bai tsaya gaida kowa ba shiga 'bangaran sa na wajan Hajo,koda ya shiga Hajo na ad'aki tunda rayi sallar isha bata fitoba dan haka batasan da shigowar tasaba, shima da yake yayi sallar sa kuma agajiye yake yana watsa ruwa ya kwanta sai bacci. Har kusan karfe 10:30 Hajo bataga Mansur ya shigoba taba Khadija wayar ta takira Mata Mansur, takira amma bai d'agaba dan haka tafito domin taje wajan Ummi taji ko lafiya ,amma tana fitowa taga motarsa dan haka ta tabbatarda yana acikin gidan sai ta kumawarta ciki,har takai zaune wata zuciya tace taje tagansa taga ko lafiya. Bacci tasamu tabayi abinsa tace "lallai wannan yaro,wato ni kabari da damuwar rashin faninka" ta janyo masa k'ofar taje tayi kwanciyarta. Washe gari yaje yagaida iyayan nasa da kwana ya karya sannan ya huce office. Bayan yayi dube-dubensa acikin fayil sannan ya d'aga waya yayi kiran Jabir,cikin mintunan dabasu huce uku ba sai gashi yashigo office d'in. Magana yayi masa akan "wane lauya ne zasu samu mai rik'on gaskiya da amana dan ayanzu na Allah basuda yawa idan sunga kud'i tsat za a iya sayar musu da imaninsu, kasan haka Lawal yayi mana bayan mun yarda dashi bancin da iyawar Allah da yanzu bazamuyi nasara akan wacan case ba". "Wannan haka yake boss, amma in sha Allah wannan karon zamu dace, akwai wani lauya da naji ana fad'insa akan gaskiyar sa da rik'on Amana,sunan sa barrister Umar Kasim shi zamu kaiwa case d'in, sannan munada hujjoji dayawa wanda zaisa ayankewa Habib hukunci komai tak'amar ubansa" "A ina kake tunanin zamu samesa?" "Wannan bazaiyi wahalar samuba,zan nemi number sa sai mikirasa mumasa bayani,idan ya amince sai muje har office d'in nasa musamesa" "To shikenan tsakanin yau dagobe kasamar mana number tasa donjin zai amince ko yaya" "Okay in sha Allah zanyi k'ok'ari". Abida fa jiki yayi kyau sosai domin kuwa ayanzu har tana takawa da kanta saboda kular datake samu, kausar na iyakar k'ok'arinta akanta,hakama mahaifita jiki yayi kyau sosai sai abinda ba arasaba,musamman da yake jin labarin jikin Abida da sauk'i. Yanzu zaune take tana cin abincin agidansu kausar aka dafu musu dan kusan kullun acan ake kawo musu abincin, maman tace tashigo da sallama ganin 'yar tata fes-fes sai kace ba mai jinjikiba yasata cikin farin ciki sosai, kausar ta gaidata da tambayarta jikin Baba?, "da sauk'i kausar inaga in sha Allah zuwa gobe ko jibi zasu basa takardar sallama dan ko d'azu naji suna maganar" "To Allah ya k'aro sauk'i" "amen ya Allah, itama naga k'aunar taki jiki sai kyau yakeyi... Kuyi hankuri da wannan kwanannan banaji dad'i shiyasa wataran kukejina shiru ~mom surayya~ [2/15, 11:29 AM] mom surayya: Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 13 "Ai kuwa dai Mama jiki sai dad'a kyau yake gashi yauzu har tanacin abinci ta k'oshi" "Masha Allah haka akeso ai" shiru tayi nawasu mintuna kafin tace "Allah dai yasakamiki Abida amma yariga da ya cucemu" Hawaye ne suka zubuwa Abida afuska kwata-kwata taji abincin yafitarmata arai, tabbas Habib yariga da yagama da rayuwarta saboda ya k'wacemata abin tak'amar kowace d'iya mace,mizatacewa mijin dazata aura? batasaniba, bata akkaraba plate d'inda ke hannunta yayi k'asa wani irin kuka na kucce mata mai k'unar rai. Kausar ce tayi sauri k'arasawa wahanta tana lallasgunta da mata kalamai masu taushi, "haba Abida kukan ya isa hakanan ki daina zubar da hawayanki abanza kan wani d'an iskan da zaik'are rayuwar sa agidan yari,domin nasan tunda wannan case d'in yake gaban boss da oga Jabir nasan da yardar Allah bazai ta'ba ku'butaba,kuma Allah zai dubeki yabaki mijin da zai soki da kula dake saboda bada niyarki abin yafaruba". Ta juya ta kalli Mama tace "Mama bai kamata kina wannan maganar ba agabanta,yanzu Abida kwantar mata da hankali yakama ayi,kiduba kiga yanayin da tashiga jin maganar da kika fad'a" "In sha Allah zan kiyaye,abinne in natuna yana k'onamin rai" "Yaza ayi da k'addara Mama,wannan yana cikin k'addarata,kuma bawa bazaita'ba huce k'addarar saba,kuma musulmin k'ware da d'okar k'addara akasanshi ko wace irice" "Hakane kausar,kuma ai tunda abinnan yafaru muka rungomin k'addara da rok'on Allah yasaka mana agareshi" Zama tayi kan kujera tanasa gefen gyalenta ta goge hawayen da suka zubomata, ita kausar saida ta share hawayen da suka zubomata na tausayin su, ba shakka da ciyo karasa wannan abin mai matukar kima da darajja awajan d'iya macce batare da aureba,nandai sukasa Abida gaba suna k'ara bata baki harsuka samu rayi shiru ta kwanta,amma tanajin wani abu mai girma yayi mata tsaye ak'irjinta,tadaiyi shiru ganin suma suna sharar hawaye ne kawai,amma itakad'ai tasan abinda takeji,dan ganin take ayanzu batada sauran wata darajja,ta juya kanta gefen bango tana share hawaye dankar sufanta. 'Yan makarantafa rayuwar makarantarsu sukeyi hankali kwance dan ayanzu su fara sabawa sosai acikinta,basuda damuwar komai sun maida hankalunsu akan karatunsu,dan dama burinsune suyi karatu sugama su zama doctor tun basusan muhimmancin miye doctor ba,dan alokacin idan suna fira Mansura takance ita ba abinda ke burgeta ga likita kayan nannasu farare musamman idan sukasha goga,gashi kuma mutun komai girmane kazo kamasa allura koda bataso, "Allah idan nagirma nazama likita idan nazomaka allura bakaso sai nama mutun video in watsa you tube da tiktok mutane sugani suyi dariyarsa" alokacin idan tayi maganar Rukayya takance "kemafa tsoron Allurane dake, yazakiyi idan bakida lafiya?" takan bata amsa da cewa "wayafad'a miki likita nayin ciyo, shida kebada magani taya zai bari rashin lafiya takamasa,ai ciyo da kansa zaiyi gudunsa" To tun alokacin suka d'au k'udirin zama doctor tunda abinda d'ayansu keso d'ayan koda bayaso d'ayan zaiyi k'ok'arin sonsa,ra atinsu yariga da yazama d'aya, gashi sunada k'ok'ari dai-dai gwargwado,Mansuracema takeda son tsokana kuma batabarin ko takwana,idan kamata anan wajan zata rama, amma hakan baisa tanawasa da karatuntaba. Basa ganin kowa daga gida domin Mansur ya hana azomusu gudun kar hakan yasa su d'ora kuka idan sukaga d'an gida ko sufara wasa da karatunsu, saidai idan an kwatanci abincinsu yak'are da sauran abin buk'ata za'a aikowa shugaban makarantar yabasu, kala suna basajin dad'i da damuwar rashin ganin wani nasu idan sukaga duk anazowa wad'anda suke tare harsukazo suka saba, Hauwa tayi ta tambayar yaushe yayansu zaizo musu?, suma basu saniba amsar dasuke bata kenan, Mansura takance "wakilma shine yahana kowa zuwa wajansu dansuji dad'i" tana fad'a tana cika fuska sai kace yana gabanta. Har fad'in take "idan yagadama kar wanda yazo sai sungama makarantar sun koma gida kuma Allah yasa awajan aikin nasa yasamu wadda zai karya masa hannu" sai Rukayya tarufe mata baki tace "ba aminba wallahi" Hauwa saidai tayi dariya,kuma tagane yana takura musu agida da kuma jin datayi shine yasa aka kawon su wanna makarantar ta kwana Jikin Abida alhamdulillah domin taji sauk'i sosai shima Baban har an sallamesa yanacan gidan da Mansur ya kama musu na haya,dan yace su k'yale wacan, ranar Monday zasu shiga koto in sha Allah,kuma suna saran kafin lokacin itama Abida su sallameta,godiya yamasa sosai da fatar gabamawa lafiya da iyayansa lafiya dama duniyar gaba d'aya. Jikin Abida alhamdulillah idan ma basani kayiba bazakace ga abinda ya faru da ita,tayi garau abinta,suna sa ran gobe Friday asallamesu. Jabir yasamu yin magana da lauyan,kuma yace in sha Allah zaiyi tsaye akan gaskiya kuma za adace da yardar Allah. Yaje har asibiti sunyi magana da Abida,kuma tafad'a masa ikar abinda tasani tundaga A har zuwa Z,kuma yace ta tabbatar abinda zata dad'i kenan idan anje kotun, tace "to" tare da share hawayanta. "Yi shiru ki share hawayenki za a k'watar miki incinki in sha Allah" kanta ta d'aga masa tana k'ara share hawaya. Shima Alhaji Zari ganinfa shiga koto ya tabbata yasa shima ya bid'e nasa lauya, sun tsara duk yadda zasuyi domin d'ansa ya ko'bota da narka uban mak'udde,shima lauyan ya tabbatar masa da za adace kafin suyi sallama. Yau Monday 22-6 na wannan shekarar da muke ciki, koto tacika sosai saboda akwai shari ar da zayi biyu tasu Abida itace ta uku, kuma duk akan magana d'aya akan fyad'e, anfara gabatarda shari a tagaba wadda ubane yawa 'yarsa ta cikinsa fyad'e,an kira uban da yarinyar 'yar kimani shekaru goma sha shidda,itace akace tafad'i abinda ya faru, bayani ta fara kamar haka "Watarana ce wadda bazan ta'ba mantawaba arayuwata,ranar laraba muna bacci acikin d'akin da yakasance namu nida k'annena guda biyu Humaira da Abdul, Babanmu yazo ya tadani in kaimasa ruwan wanka, kasancewar mahaifiyarmu batanan taje garinsu gaisuwar matar mahaifita da tarasu,tashi nayi nakai masa ruwan tare da zuwa na sanarmasa da nakai yacemin to ya gode ni Kuma na koma d'akin mu domin cigaba da baccina, har baccin ya fara d'auka ta naji Kuma ana sake kirana na tashi naga Babanmu ne,zama na gyara nace Baba kanason wani abund?" Yace "eh taso ki zubamin abinci inci" nace "ai nazuba yananan afalo cikin cola". saboda duk yadda naga mamammu na masa nayi saboda ko tananan wataran nice ke abince,to nasan duk yadda ake masa. Maganarsa naji yace "eh nagansa inason ki zubamin aplate ne" to nace natashi nashiga kicin na dauk'o plate d'in nashi cikin falo na zuba masa na ajiye masa agabansa nace gashinan Baba" Yacemin "to nagode d'auki ga nama nan ki zuba kici" dukda nayi mamaki sosai domin nasan shi mutunne wadda kafin aci nama agidansa ko wane abin k'walan ba maza kusaba,amma nace araina
Chapter 16 · 0% Book details