Sashe 37
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'ya'ya agun iyaye idan basu hutar da iyayan nasu ba, sannan fatafa ake muku idan baku saniba" Mansura tace "Ummi rabu da ita yanzu zamuje muyi kinsan ita dama ba aikin kitchen take soba, mi za agirka yau?" Ummi tace "yauwa y'ar albarka, kuyi tuwon shinkafa miyar alaiyahu da agushi, saiki had'a kunun aya da kwakwa" dai-dai tana gama shirya kayan tace "Shikenan Ummi, dama dan Allah gobe munason muje gidan Yaya kinga har yanzu bamuje gidan sa ba" ta fad'a tana shagwa'be fuska. "Shikenan zanwa shi Yayan naku magana in anjima idan yazo" Mansura tace "haba Ummi yanzu dan Allah sai kingaya masa zamuje, kinfa san halinsa zai iya cewa muyi zaman mu" Ummi tace "mizaida yahanaku zuwa gidan sa, in sha Allah ma bazai hana ba zakuje ku kwantar da hankalin ki" Kai ta d'agawa Ummi kafin tace "Ummi bari mushiga kitchen kar dare yayi mana" Ummi tace "afito lafiya" suka tashi suka fita daga d'akin suka nufi kitchen. Mansur kuwa bayan yazo nan gidan ya gaidasu tare da karyawa ya huce office, suna zaune shidai Jabir suna tattaunawa sai kiran Abba ya shigo, bayan ya d'aga suka gaisa duk da sun gaisa da yazo gidan, Abba yace "Mansur idan katashi wajan aiki inkazo gida kar kawuce akwai maganar da nakeson muyi" Yace "lafiya dai Abba?" "Lafiya k'alau maganar ce dai bagani bata wayaba" "Yace "shikenan Abba sai nazo" ya kashe wayar tare da ajiye ta agefen, Jabir yace "lafiya daiko?" "Nima bansaniba tunda bai fad'a minba yace sainaje sannan" Jabir yace "to Allah yagishimi alheri" Yace "ameen ya Allah", daganan sukaci gaba da abinda sukeyi. Bayan ya tashi daga office gida ya wuce kamar yadda yasaba, basu had'u da su Abba ba saida suka fito sallar isha i, da yake da yake sallar magriba bai fitoba sai yanzu, gaisawa sukayi sannan suka tafi part d'in Hajo kai tsaye. Anan part d'in sukaci abinci cikin raha da farin ciki, sannan Abba ya maida hankalin sa ga Mansur kafin yace "Mansur ba komai yasa nacema inason magana dakai sai akan maganar wannan yarinyar Abinda" Mansur yace "wani abinne ya faru Abba?" Abba ya girgiza kai yace "ko d'aya Mansur, nasan dai kasan Alhaji Kasim na nan gaba garemu kad'an?" Shiru Mansur yayi alamar tunani kafin yace "eh nagane shi wadda matarsa ta rasu watannin baya ko?" Abba yace "k'warai shi! d'azu yaje ya samemu nida Yaya akan yanason abashi auran Abida domin ya yaba da yarinyar, to shine mukace bazamu yanke hukunci har sai mun sanar dakai sannan mukai maganar ga mahaifita, amma nidai asanina da Alhaji Kasim mutunan kirkine bayada wata matsala, kuma ya gayamana dan Allah bayason aja lokaci da nisa, nidai nace masa zan nemaisa idan mun yanke shawara" Ajiyar zuciya Mansur yayi yace "Abba ba wannan ba yasan abinda ya faru da ita?" Abba yace "yasan da duk wannan kuma yace ba matsala bace tunda wannan k'addara ce bada son ransa ba, shidai buk'atar sa samun macce mai tarbiya wacce zata iya ba yaran sa tarbiya tamkar mahaifiyar su" Yace " shikenan Abba zan nemi yardar yarinyar idan har ta amince banida matsala saidai inyi musu fatar zama lafiya tunda ta gama sakandiri d'inta, da safe idan na shigo zan mata magana duk yadda ake ciki zakuji" "Shikenan Allah yayi maka albarka" "Ameen... ~mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 39 Washe gari koda yazo gidan yana gama karyawa ya aika Rukayya tayi masa kiran Abida, babu jimawa tashigo tare da Rukayya da taje kiranta, samun wuri tayi ta zauna tana cewa "Ina kwana Yaya" amsawa yayi da lafiya, tuni Rukayya ta shege d'aki dan haka su kad'ai ne a parlour "Abida!" Amsawa tayi "na'am Yaya" "Ba komai yasa nace akiramin keba sai dan neman amincewar ki akan wani da yafito yana son auranki, tun jiya yajema su Abba da maganar sukuma suka gayamin, amma nace zan miki magana idan kin amince to falillahil hamdu, in kuma sai yazo kingansa shikenan sai amasa magana in bai mikiba sai abasa hank'uri ya nemi wata". Shiru Abida batace komai ba saima hawaye da taji suna cika mata idanuwa "ke nake saurare Abida! ko abashi hank'uri ne?" ya tambaya yana mai karanta yanayin ta. Ahankali tace "Yaya kafini sanin abinda ya dace dani domin nasan bazaka ta'ba za'bamin abinda zai cuci rayuwa ta, domin kaine kazamemini gata alokacin dana fidda rai da samuwar ta, wallahi Yaya kanada ikon zartar da kowani irin hukunci ne akaina batare da kosu Baba sunyi magana ba bale har kanemi ta bakina , kuma ni mai biyayyace agareka bazan ta'ba maka butulci ba, zakasameni maiyin biyayya ako wane hali, saidai Yaya yasan ittila in da yasameni kuma yaji ya amince ze aureni ahaka batare da zaimin goriba watarana?" ta k'arasa maganar hawayen da take rik'ewa tun d'azu suka samu gangarowa akan fuskar tata. Tausayin tane ya kamasa har yanajin wani iri azuciyar sa, kuma k'warai yaji dad'in kalaman da tayi agare sa, yace "Indan wanan ne karki damu kanki domin yasan duk abinda ya faru dake amma yaji zai iya auranki ahaka, Abida ni bazan miki dole ba ko tilastaki akan ki auri Alhaji Kasim ba, nafiso saida yardar ki da amincewar ki, kije kiyi shawara nabaki daga yau har zuwa jibi duk abinda kika yanke sai ki sanarmi, amma kinsani Alhaji Kasim mutunan kirkine domin ana yabansa acikin uguwar nan da wajanta, dan haka ina mai miki sha'awar auran sa dan zaki sami duk wata kula da macce ke buk'ata, nasan dai bazaki rasa sanin raauwar da akayi ba kusan watanni hud'u da suka wuce nan gaba garemu ba?" Yayi shiru alamar jiran amsar ta. Kai ta d'aga tare da cewa "eh Yaya nasani wacce ta rasu mai yara hud'u wurin haihuwa batare da tahaifi abinda ke cikin taba" "Tabbas ita, to mijin natane ke neman auran naki, tashi kije kiyi shawara" tashi tayi jikinta asanyaye ta fita cikin parlour shima ya tashi dan har ya kusa makara. Su Mansura dake le'be ak'ofar d'akin su aunajin abinda duk ake fad'a tayi saurin cewa "tad'in jan, aure za awa Aunty Abida kuma da tsoho, wallahi zan gaya mata gaskiya kar tasake ta auresa ta k'are rayuwar ta awurin kula da yara" Rukayya tace "to miye ruwanki aciki, kijifa mamansu ce tarasu, ni wallahi najiwa Aunty Abida dad'i " Baki Mansura ta ta'be tareda fad'in "ke dama wani lokaci kanki baja yake ba, ina wani jin dad'i a auran mijin da bakaine ka wanke saba, wata duk tagama cin moriyar sa, ni dan Allah mubar wannan maganar kinji Ummi na fad'in Yaya yabarmu?" Rukayya tace "ba abinda naji tace, k'ila bai barmu ba shiyasa batamuna maganar ba" Mansura tace "tashi dai muji" ta fad'a tana kama hannunta. Abida nazuwa gun maman ta ta zauna kusa da ita tanamai share hawayanta, lafiya Abida mike faruwa?" maman ta tambaye ta cikin tashin hankali, "kimin magana Abida wallahi duk kinsa hankalina ya tashi" Zamanta ta gyara ahankali tace "Mama bafa wani abin tashi hankali bane" maman tace "ba abin tashin hankali bane Abida kike kuka dan Allah ki gayamin mike faruwa?" "Mama wai wanine yace yana sona harma an fad'awa Yaya" ajiyar zuciya mama ta saki tare da fad'in "haba Abida shine kuma abin kuka, aini aganinta wannan abin farin ciki ne" hawaye ne suka k'ara zubo mata afuska wadda itama takasa tantancewa na miye. "Yanzu ya kunkayi da Yayan naku?" Mama tajefa mata wannan tambayar. "Nidai nace masa duk abinda yaga yadace yayi ni mai biyayyace agaresa, amma yadai cemin inje inyi shawara duk abinda na yanke in gaya masa sannan awa Baba maganar, kuma yacemin shi mutunan yasan duk abinda ya faru dani" Mama dai kallon ta ta tsaya yi tanajin farin ciki har k'asan zuciyar ta, Abida taci gaba da fad'in Mama ma ai kinsan rasuwar da akayi awatannin baya, to yacemin mijin matar ne" Mama tace " Allah sarki mutanan kirki basa k'arewa, kiyi tunani da kika fad'a masa haka, in banda abin Mansur wacce shawara za ayi kuma, tashi ki k'arasa aikin naki bari Malam ya shigo nice nan zan fara yi masa maganar" Tashi tayi duk tanajin kanta wani iri, Mama kuwa ba abinda takeyi sai murmushi farin ciki na k'ara rufe ta. Shigar su parlour Mansura tayi kan Ummi dake zaune kan kujera tace "Ummi baki gaya mana batun zuwan namu gidan Yaya ba" Ummi tace "Mansura duk son tafiyar ce yasa anmance da agaidani haka" dariya tayi tace "Allah Ummi na sha'afane ina kwana?" itama Ummi dariya tayi tace "lafiya k'alau d'iyar kirki ya Hajo fatar tana lafiya?" "Lafiya k'alau take saima k'arfin da take k'arawa kullun kamar ba shekaru tafiya sukeba" "Mansura Allah ka shirya mana ke yanzu Hajon ce kikewa shak'iyanci haka?" dariya duk suka Sanya itada Rukayya da batasanya musu bakiba tun shigowar su. "Ummi ya maganar tafiyar mune?" Rukayya ce da wannan tambayar. "Kai nidai nashiga uku da wad'annan yaran, koje zuwa bayan azzahar zakuje sai ku shafamin lafiya" Sunyi matukar farin ciki da barin da akayi musu, dan haka bazasu dawoba sai magriba in sha Allah, duk da ita Mansura da biyu takeson tafiyar dan ganin k'wan, ita wallahi harga Allah wannan matar mai kama da mutanar dori bata mataba haka kawai taji batason ta, tashi sukayi suka koma 'bangaran Hajo domin sufara shiri. (Kaji masu zanzanar tafiya Tunda Malam ya dawo Mama ta tareshi da maganar batama bari yako hutaba, dayake tunda yaji sauk'i ya komawa sana'arsa kuma Mansur bai hanasaba tunda yasan Alhaji zakari ba abinda ya isa yamasa dan hankalin sa na awajan tilon d'ansa, kuma yabar sani kafi yaga abinda ya dace akansa. Bak'aramin farin ciki Malam yashigaba dajin wannan maganar, ba abinda yake sai godiya ga Allah da wad'annan mutanan, ba abinda zasu saka musu da shi saidai suce Allah ya sakamusu da aljanna mad'aukakkiya, haka suka yini cikin farin ciki da godiya ga Allah da bai bari yarinyar su ta walak'antaba. Mutanan kuwa koda akayi salla tuni sun shirya lokaci kawai suke jiran yacika su tafi, dan haka ana gama sallar sukayiwa Hajo sallama suka fito, part d'in Ummi suka nufa domin sugaya mata sun shirya asa akaisu, ita Ummi dariya ma suke bata ko zanzanar ta miye