Sashe 31
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayi amma wayan, yarinyar nan tasamu damar guduwa kenan? to da yaushe tasamu damar da har ta bud'e ta gudu? "can ya tuna da yana sauri jin ana k'ok'arin tayar da salla k'ila nan ya manta bai tsaya rufe k'ofar ba, k'wafa yayi yaje ya d'auko wayar Ummi inda ya ajiye ta sannan ya dawo falo ya zauna domin ganin wata tsiyar ya shuka aciki. Mamaki ne matuka ya kamashi ganin abinda tayi, lallai yarinyar nan sai abarta, harda sa reza ta tsaga mata riga, amma duk da haka ransa ya 'baci da shigar da Bashhama tayi amatsayin wajan zuwa gaida iyayansa, ina laifin tasa kayan da zasu mutun tamata jiki, wani wajan abinda Mansura tayi ya masa dai-dai, dolene ya nuna mata kuskuranta na zuwan musu gida ahaka, amma duk da haka zai nuna mata matar da zai aura ba abar renawar ta bace. Tashi yayi ya fito daga part d'in nasa yayi 'bangaran Hajo, yana shiga ya tarar da Hajo afalo da itama fitowarta kenan ta zauna, "Hajo ina wannan yarinyar tayi?" kallon sa tayi tace "wace yarinya kenan?" yasan tasan wacce yake nufi amma saboda baya buk'atar 'bata lokaci yace da ita "Mansura" Tace "aini tun lokacinda Mariya ta aiko da keran ta ban k'ara ganin ko keyar taba anan, sai kaje can ko tanacan" bai k'ara magana ba ya juya ya fita baki ta ta'be tace "kaji dashi" Momy ma tace "tunda suka fita tare bata saki ganinta ba" Khadija ce tace taga lokacin da take gudu ta nufi 'bangaran Ummi lokacin da ta dawo daga aikar da tayi mata wajanta. Yanajin gaka bai tsaya bata amsa ba yanufi part d'in, azaune ya tarar da Ummi atsattsaye ya gaida ita tare da tambayar ina Mansura tayi?" batama d'ago kanta ba tace masa "gatanan saman kaina" shiru yayi baice komai ba, taci gaba "wallahi kaki yayeni kuma kashiga ahankalin ka, akan dukan wannan yarinyar zan iya sassa'ba naka, kai ko kunyar kawaicin da mahaifiyar ta keyi maka akan ta bakaji? to wallahi kar inji kar in gani ka daki ta, kuma idan har kamata wani abu nida kaine agidannan, kadaiji" sun kuyar da kansa k'asa yayi yace "ayi hank'uri Ummi in sha Allah zan kiyaye" tace "da yafima". Juyawa yayi zai fita ransa a'bace yaji tace kabani wayata ko nabarmane gaba d'aya inji ne" wayar yazo ya mik'a mata ya fita. Mansura datake d'akin Ummi abinta itada Rukayya suna fira hankalin ta kwance taji shigowar ta yana tambayar ta, Rukayya tace "ga Yaya nan ya shigo tashi ki shige bayi ki 'boya tun bai cinmiki anan" tace ba inda zanje ai Ummi tace bazata bari ya dakan ba, kuma bazan bari sake ganina ba sai munzo wani hutu, lokacin nasan ya manta, lokacinda sukeji Ummi na masa fad'a Rukayya sam bataji dad'i ba har har fuskar ta ta nuna, dan haka tanajin fitar sa itama ta tashi tabarwa Mansura d'akin, domin harga Allah bataji dad'i abinda Ummi yawa Yayan nasuba, ai yana da damar da idan sukayi laifi ya yanke musu hukunci, kuma ai baya dukan su sai idan sun masa laifi. Itakan Mansura ranta fal farin ciki an hanasa dukanta, tanajin an kira sallar isha i ta tayar da salla qbin ta, tana gamawa tayi kwanciyar ta saida Ummi ta aiko kiranta tazo taci abinci sannan ta fito daga d... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 32 Washe gari saida tagama shiryawa zasu tafi sannan ta shiga part d'in Hajo d'aukar kayanta da dama shirye suke tun jiya da safe ta had'a duk wani abu datasan zata buk'ata, Hajo na ganinta tace "Mansura miyasa zakiyimin yaji baki fad'a minba, kinsan wajan uwarki zakikwan baki fad'a minba,kikasa nabar k'ofa ta awangame saida mai sunan Malam yake gayamin in tashi in koma d'aki ba anan zaki kwana ba" Duk abinda yafaru Mansura tashiga gayawa Hajo tun daga kan kiran da Momy ta aiko Khadija yimata, da cewar da tayi Yaya Mansur ya hukunta ta dama guduwar da tayi wajan Ummi,da abinda Ummi tayi masa duk saida tagaya mata. "Lallai ma mai sunan Malam daya janyowa kansa agidannan da ya dakeki akan wannan mai kama da jikokin pastor, da yau zai gane kalata agidannan dan sai na masa tijara, ita kuma uwar taku nida itane, yanzu wa zai kaiko makarantar?" "Naji Dady yana gayawa Ummi jiya cewar direba ne zai kaimu" Rukayya ce tashigo tace Mansura ki fidda kayan asa amota mana kin tsaya kina biyewa wannan tsohuwar tuni ansa nawa fa" jin abinda tace yasa tace " ok zoki tayani" bayan sugama fidda komai suka shiga part d'in Momy domin mata sallama, nasiha sosai tayi musu mai ratsa zuciya tare da fad'a musu su nutsu su kama kawunnansu suyi karatunsu su samu su gama ba wani shirme ba, musamman ke" ta fad'a tana nuna Mansura "na kula kanki na miki rawa ba kamar 'yar uwar taki ba, ku sani duk wayuwar gari girma kukeyi, dan haka kusan abinda ya kaiku ba shirme da rawar kaiba, ku tsare kawonan ku da duk abinda zai ta'ba martabar gidannan, duk da nasan banida haufi akan tarbiyar da muka baku" Momy tana musu wannan nasiha ce saboda fahimtar da tayi yarannata su dad'e da zama 'yan mata, godiya suka mata da fad'in in sha Allah bazasu basu kuya ba, nan suka sallama suka fito. Mota suka shiga suna d'agawa iyayan nasu hannu suma suna d'aga musu, wannan karon kan Mansura saida ta share hawaye ba kamar wacan karon ba da tadakewa ranta ba, Allah yasani tanason rayuwar gidansu, domin duk lokacin da take cikin sa sai ta d'aura d'aukar kanta kamar wata 'yar shekara bakwai, itama kanta ta sani duk wani rashin jin nan nata idan tana gida tafi yinsa, itama tasan da haka. Koda suka isa tuni Asmau da Zainab sun isa, sunyi matukar farin ciki da saki had'uwar su awaje daya bayan hutun da suka sha duk da suna waya da junansu ako wane lokaci sukaso ta hanyar wayoyin iyayansu, ko wanesu ya fidda tsarabar da yazo da ita suka aje na ajiyewa suka d'au wanda zasuci. ___________________Bashhama lokaci da ta shiga d'akin nata wanka tayi ta dai-daita kanta tasa wasu kaya tasanyawa idanunta kwalli wadda ma har mance take miye shi arayuwar ta, domin batason kowa ya fahinci halin da take ciki na abinda aka mata aginsu Mansur dan tafi kowa sanin halin mahaifin nata tsat zai iya cewa bazata aure saba tunda danginsa basa k'aunar ta, Duk da kuwa tasan babu wadda zatace ya mata wani abin ko baya son taba in ka cire wannan marar kunyar yarinyar, sai tsohuwar nan data lura tana mata wani gani-gani, sannan ta fito tagayawa Momy nata ta dawo, tare da nuna mata tsarabar da suka bata, godiya tayi tare da fad'in "Allah amfana kinyi sa'ar surukunnai, saidai muce Allah yakaimu wanan lokacin da zamusha budire agidannan" Murmushi kawai tayi tana danne zuciyar ta bata bare mahaifiyar tata ta fahinci komai ba kafin ta koma cikin dak'inta. Koda tashiga d'akin nata batabi kiran na Mansur ba, saidaga baya sannan, kira kusan hud'u bai d'aga ba sai ana biyar sannan ya d'auka, ajiyar zuciya ta saki lokacin da taga ya d'auka amma baiyi magana ba, "Hello husband" sai kuma ta tuna tace Assalamu alaikum" amsa wa yayi ciki-ciki kamar wadda akawa dole "husband naga kiranka lokacin ina dirabin, kuma da nadawo natsaya magana da Momy sai yanzu nac... "Ya isa hakanan, ke yanzu wannan shigar da kikayi kikaje gaida iyayena shigar da yadace kiyi ne? rashin hankali ne ko miye? ko kin d'auka iyayena marassa mutuncine kamar sauran iyaye komai? to bari kiji wallahi duk ranar da kika koma zuwan mana gida acikin wannan shigar sai ranki yayi mumunan 'baci" Ranta ya 'baci da wannan maganar tasa, shi baiji rashin kunyar da marar mutuncin nan ta masa bane yake gaya mata magana?" cikin k'asa da murya tace "amma bakaji abinda d'ayar k'anwar nan taka tamin ba ne?" Cikin 'yar hasala yace "ai abinda tamin yamin dai-dai, dama fiye da haka tamiki" hawaye ne suka zubo mata afuskarta tace "yanzu Mansur ni kake gayawa haka" "Amfad'a miki ke waye wacce ta huce dabba jaka" ya k'arasa fad'a yana kashe waya. Wannan abinfa yasanya ta koka sosai harta gode Allah,tundaga wannan lokaci kowa ya share wani kusan sati biyu, duk da itace mai jigata danshi ko akwalar jikin sa, saida taga abin bana k'arewa bane sannan ta saukar da makaman yak'in ta takirasa, duk kiran datake masa bai d'auka ba har tsawon kwana biyu,washe gari ya shirya ta tafi office d'in nasu. Mansur da baisan ita itabace yabada izinin shiga,yana ganin itace ya d'auke kansa, hawaye ne taji sun cika mata idanu,ta k'arasa gabanta ta ajiye bag d'in hannuta ta game hannuwan ta waje d'aya tace "and sorry my husband, hakan bazata sake faruwa ba in sha Allah" yi yayi kamar ma baisan da ita awajan ba, gwaiyoyita takai k'aaa tace "dan Allah na rok'eka ka yafemin" "Miyasa kikazo office bana hanaki zuwaba?" "Ya zanyi! Nakira baka d'aga ba dole tasa nazo dan na baka hank'uri, amma zan kiyaye duk abinda kace min" "Ok naji zaki iya tafiya" kai ta d'ago tace "ka yafemini?" "Nace kije ko zan kiraki" ya fad'a cikin d'aga murya, jiki asanyaye ta tashi ta fita daga office d'in shi kuma yaci gaba da aikin da yakeyi. Da yakoma bai kirataba saidai itace ta kirasa, 'bacin rai sosai ya nuna mata kafin daga baya yace komai ya huce. Tundaga wannan lokaci suka shirya duk da itace mai zakewar. Kwanci tashi hasarar mai rai, kwanakkin mu suna ta k'are wa, tuni ansanya lokacin auran Mansur da Bashhama, yanzu haka ma lokaci ake jira nan da karshan watannan za ayi shi in sha Allah, Shirye-shirye ake tako ina musamman ta 'bangaran su Bashhama zaso aurar da 'yar gaban goshin su, amarya ta shieya party kala-kala wanda zatayi ga auran. Su Mansura kuwa sai shirye-shiryan zana jarabar shiga s s two, dan basan manan za ayi bikin, Mansura dai ko akwanar rigar ta dan acewar ta babu ruwanta acikin bikin mai shigar arnaye, Rukayya ce dai ta d'an damu dan harga Allah bataso ayi bikin na Yayan su batanan ba, domin taci buri