← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 39

Sashe 20

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayani, itako tazo ta musu bayani sannan fa hankalinsu ya kwanta, Rukayya tace "yanzu ta farfad'o ne? inason in ganta" "Eh sunce amma yanzu tana bacci ne,zuwa washe gari kimai zai zama normal" "To Allah yasa" anan suka k'arasa baccin nasu saida aka kira sallar asuba sannan suka koma d'akin su akabar Rukayya koda za a buk'aci wani. Yau Asabar, yaune kuma Mansur ya tashi da k'udirin zuwa makarantar su Mansura,dan har yagayawa Jabir ya shirya misalin k'arfe 10am zasuje, bitashi faga baccin da ya komaba sai misalin 9:22am wanka yayi sannan yaje ya gaida Hajo, sunyi y'ar fira kafin Hajo tace ya batun zuwa wajan yarannan?" "Yananan in sha Allah yanzu dana karya zamu huce nida Jabir" "Amma dai dani zakaje ko?" "Ina zakije?" "Inda zakaje mana, kana tunanin zan barka kaje ni kabar ni? kama daina wannan tunanin" "To naji yanzu dai tashi ki shirya kafin na karya ingaida su Momy muje" tace "yanzu naji magana,ko kaifa,tashi ga abincinka can kaci kafin in fito wanka, tayi hanyar d'akin ta, har zata shige ta waigo tare da fad'in wallahi idan ka gudu nida kaine agidan nan,nasan halinka sarai" "Naji" kawai yace da ita, cikin ransa dariyar duramar Hajo yake, dan kamar tasan abinda yake shiryawa ya gudu ya barta. Abinci ya d'auka ya fara karyawa,yana gamawa ya tashi yaje gaida mutanan gida, 'bangaran Momy yafara zuwa gaidawa, zaune ya tarar dasu suma suna karyawa, da take yau Asabar Abba yana gida, gaidasu ya duk'a har k'asa yayi. Amsawa suka tare dare cewa ya taso ya karya, yace a a yauzu yagama karyawa,yanama gamawa yazonan,bayan sun d'an ta'ba fira kafin yace musu zaije wajansu Mansura yau, Albarka suka samasa tare da fad'in su gaidasu, mik'ewa Momy tayi tare da fad'in "barin in kawo sak'o ka kai musu" batare da tajira abinda zai ceba ta wuce, babu jimawa sai gashi ta dawo, sakon tabashi tareda fad'in "ka gaidasu" "Ok zasuji in sha Allah" nan yayi musu sallama ya fito, 'bangaran su Ummi ya nufa tareda ciro wayarsa yana kiran Jabir, "dan Allah kazo muje hakanan kasan inada abinyi" dariyar Jabir ya fashe da ita yace ok gani nan zuwa bani mintuna" "Naji, kaidai kanason wasa da abu bayan kasan abinda zanyi mai muhimmanci ne, nasan duk ranar da ka aje mata sai munkoraka gun aiki saboda lattin da zakadinga yi" "Duk abinda zaka fad'a kanada damar fad'ar ne nidai sai nazo" yanke wayar dai-dai da shiga indasu Ummi ne, nanma Dady yananan,gaidasu yayi sukan cikin sauri yace "yana saurine zaije makarantar su Mansura ne, suma dai Albarka suka samasa dajin dad'in samun d'a kamar sa, nanma kamar Momy itama Ummi sak'o tabayar akaiwa Yaran nata. Fitowa yayi ya koma 'bagaran Hajo domin yagani kota shirya, zaune kowa ya taran da ita akan kujera tasha uban d'auri, ga mayafinnan ta yafa tundaga saman kai sai kace tsofin yarbawanan,ganin yadda tayine yasashi sakin 'yar dariya tare da fad'in g... Sai zuwa Monday in sha Allah ~mom surayya ce~ [2/15, 11:30 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 18 "Gaskiya yakamata akiraki da shugabar nad'in masu d'aurin d'ankwalin garinnan, irin wanan d'auri haka, kai doline ma in biya dan nasan nine kikawa dan ingani in kasa tafiya in barki" Mayafinta ta k'ara gyarawa tace "fad'i son raka nidai yau sai kakaini naga y'an jikokina ehe" "Naji, dama kodan wannan kwalliyar da akamin ai dole inje dake". "Tashi muje Jabir ya k'arasu nasan yana waje" ya fad'a ganin kiran nasa,tashi Hajo tayi tabi bayansa dan tuni yati hanyar waje. Hasashansa gaskiya ne,domin kuwa Jabir ya k'araso yana agaban mota zaune, baban Abida ne dake zaune kan benci shida mai gadi suna y'ar fira, ganin Mansur sun fito shida Hajo kuma ga dukkan alamu fita zasuyi yasa ya taso, gaida Hajo tayi cikin girmamawa dan harda y'ar duk'awarsa, cikin mutunci Hajo ta amsa tare da tambayarsa Maman Abida da ita kanta abidar? tace "lafiya Abida bata shigoba kamar yadda tasaba?" "Lafiya lau wallahi, nabar tana wankine nasan da tak'arasa zatazo gaida kine kuma naga kamar fita zakuyi?" "Eh wallahi,zamuje ganin yarane amakaranta" "To,to shikenan agaidasu" "Zasuji in sha Allah" Mansur ne ga gaidasa shima cikin kulawa,shima ya amsa tare da k'aunar yaron har cikin ransa. Bayan mota Mansur ya bud'ewa Hajo ta shiga ya kulle, shi kuma ta bud'e gaba ya shiga, yana zama Jabir yace "na d'auka direbanka zan zama abaya zaka zauna" "Abin mamaki ne dan kazama direba na?" "Ba abin mamaki bane saboda kai oga nane, kagako baza ayi mamakin nazama direbanka" ya fad'a yana tayar da motar. Waigawa yayi baya yace "Hajo ina kwana an tashi lafiya?" "Lafiya k'alau Jabiru, ya kabaro maman taku?" "Lafiya k'alau suke Hajo, Mamy ma tace agaida ku" "Na kuwa gode sosai kwana biyu itama bata zagayomuba?" dariya yayi yace "itamadai saida ta fad'i haka, amma tace in sha Allah zata samu lokaci ta shigo ta faidaku" tace "dadai yafi. Maigadine ya bud'e musu suka fita daga cikin gidan,saida suka d'au hanya Jabir yace "Hajo baki yarda da zuwan mai gidan naki bane kika biyosa?" "Inafa zan yarda Jabiru, kasan yadda abokin naka yake, zai iya da zuwansa ya kama yaran da fad'a babu sid'i babu sad'ad'a", Dariya maganar tata tabasa yace Hajo tamu ta mutunci,miye babu sid'i babu sad'ad'a?" itama dariya tayi tace "dad'a fa, ba kurin kuke ku hausawane, amma komai baku sani acikin hausa ba" Dariya yayi yace "hakane kuma, amma zandiga samun lokaci inzo ki koyamin kozan iya" "Wai wak'a, ku bancin kama d'iyan mutane ku gark'ame mi kuka iya" hakadai sukaci gaba da hirarsu gwanin sha'awa, ba kowace fira bace Mansur kesa musu baki sai yaga dama, dagashi sai Hajo, sai kace su biyu ne kawai acikin matar har suka k'arasa. Tunda Aunty Hauwa tayi sallah bata koma bacci ba abin kari ta fara had'awa wadda zata kai musu, zuwa 7:10am tagama duk abinda zata buk'ata wadda zataje dashi sannan tashiga wanka, tana fitowa ta shirya cikin sauri tad'au abincin ta fito. Saida tabiya takira su Zainab idan sun shirya suje tare,suma ta tarar da duk suyi wanka sun shiya, Asma u na tsaye da basket nasa abinci da alamu Zainab take jira tasa hijabin datake sakawa, juyuwar dazasuyi su fito sukaga Aunty Hauwa tsaye da kayan abinci a hanunta. "La Aunty kema har kin shirya? yanzu nake cewa Zainab tayi sauri muje mukiraki munbar Rukayya ita kad'ai". "Eh nashirya, kuma baku koma bacciba kenan?" "Eh Aunty muyi musu abin karine, amma kuma naga kamar yayi musu yawa, ko mu ajiye d'aya zuwa anjima akai?" "A a Asma u muje kawai idan yaso ta za'bi wadda takeso" "Ok shikenan"suka fito suka nufi hanyar asibitin. Sun tararda har zuwa lokacin Mansura bata tashi daga baccin allurar da akamata, Rukayya na zaune ba alamar bacci a idanunta sai tunanin take mike damun y'ar uwar ta? Tana cikin wannan tunanin taji sallamar su Aunty Hauwa, kanta dake duk'e ta d'ago tana amsa musu salamar, idanunta sunyi ja sun kunbura akan kukan da tayi, k'arasuwa sukayi ciki suna tambayar ta yamai jiki? "Da sauk'i dai dan har yanzu bata farka ba, amma nurse taci babu jimawa zata farka datazo dubata, kujera d'aya Aunty Hauwa ta janyo ta zauna akai,dayake kujera biyu ne ad'akin,sukuma suka zauna gefen gadon da Mansura take akai Aunty Hauwa tace "zata farkane in sha Allah, yanzu ki zauna ki karya sannan kije ki watsa ruwa kafin lokacin in sha Allah ta farka" Rukayya ta dubeta tace "bazan iyacin komai ba aunty matuk'ar banga sister na ta tashi cikin yanayi mai kyauba" "Amma Rukayya da kinci ko kad'an ne" "Bazan iyaba Aunty,dan Allah kiyi hank'uri" "To shikenan naji,tunda bazaki iyaba yanzu kije kiyi waka kinga kayan bacci ne ajikinki tun jiya" badan tasoba ta gyad'a mata kai alamar zataje. "Yauwa kokefa, tashi kije kiyi, amma yakamata ki kira gida ki gaya musu" "Eh naso idan shugaban makaranta ya fito inje in gaya masa ya kira Yaya ya fad'a masa" "Hakan ma yayi" amma aranta addu ar take Allah yasa yazo ko ranta zai mata sanyi, tashi Rukayya tayi dan zuwa hostel tayi wankan. Wanka tayi ta dauk'o rigarta marar nauyi tasa, hijabi tasa ko kwalli bata tsaya shafawa ba ta fito, office d'in shugaban makaranta ta nufa ganin ko fito. Tafe take akan hanya acikin ranta tana addu ar Allah yasa Koda take zuwa ta tashi, "Wai Allah, Allahumma amin" ta fad'a tana shafama fuskarta. Koda ta isa akulle ta tarar da office d'in alamar baikai ga fitowa ba,dan haka ta maida akalarta zuwa asibitin. Har zuwa wannan lokaci bata farkaba zaman kira kawai suke,da tattaunawa tsakaninsu, ba yadda basuyi ba da Rukayya taci wani abin ko kad'an ne amma tace batajin ci, likita kusan zuwansa biyu yana dubata, yace musu normal ne,da zarar allurar ta saketa lafiya k'alau zata tashi. 10:45 Aunty Hauwa tace Rukayya tatai tagani ko shugaban makaranta ya zo. Amsa mata tayi dato sannan ta tashi ta tafi, wannan karon tayi sa a ta tarar dashi dan zuwansa kenan baifi mintuna biyar da zuwaba. Sallama tayi saida ya amsa mata tare da bada izini sannan ta shiga,gaidata yayi ya amsa da tambar y'ar uwar tata?, cikin sanyin ta tace "yanzu ma zuwa nayi na fad'a maka ko zaka kira gida ka fad'a musu jiya a asibiti muka k'arasa kwana" Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu har saida takai k'arshe sannan yace "subuhanallah, miyasameta?, Da sauk'i dai injin?" "To da sauk'i dai za ace,dan har yanzu bata farka daga allurar da akamata, amma sun cemana normal zata tashi dazarar ta farka" "To masha Allah,bari inkira na fad'a masa kwana biyu ma bamuyi wataba" ya ciro wayar kenan saiga sallamar su tare da shigowa cikin office d'in, cikin tsananin farin ciki Rukayya tayi wajansa tare da rungomesa, shima hannu biyu yasa tare da dafa bayan ta,domin Allah yagani shima yayi kewar su, saida Hajo tace "wato shikad'ai kikani banda muko?, nasan da Mansura ce nizata fara tarba ba wannan ba,inama take ingata? dama ita nazo gani bakeba" Hawaye ne suka zubo mata a idanu tasa gefen hijabin ta tashare, tace "dama nazone na fad'a masa ya kiraku Mansura batada lafiya jiya asibiti muka kwana" "Innalillahi wa inna ilaihin raji un, miyasameta? wane wajene asibitin
Chapter 20 · 0% Book details