Sashe 23
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koda suka k'arasa gida yayi wanka ko abinci bai tsaya nemaba yafita bai dawo gidaba sai tara da rabi na dare, bai shiga 'bangaran iyayan nasaba ya wuce sashan Hajo domin gajiyace tattare ajikinsa, falo ya tarar da Hajo Akan kujera tana saurarar wa'azin gadon k'aya da yake, zama tayi akan kujerar dake kusa da ita yana kiran "wash Allah nah" Hajo tace "Sannu mai sunan Malam, ai dolene kaji gajiya ajikinka, ka dawo ko hutawa bakayiba ka sake fita,duk da yau ranar hutuce" zaman sa ya d'an gyara sannan yace "To ya munka iya Hajjajo Hajo, yanayin akin ne namu ahaka,awasu lokutta bamuda Hutu koda kuwa munso muyisa bai zama lalle mu hutan ba" "Amma dai dan Allah ko dinga samun lokaci ko zauna kuna hutawa ko k'wak'alwalku zata huta dan Allah mai sunan Malam, sannan abu na gaba yakamata kazo ka ajiye iyali, tunda kasan bai d ace kana zama har zuwa yanzu bakada iyali kan wani dalillai naka, sannan ko banza zaka sami wacce zata kula dakai kaima kabata naka lokacin, na fuskanci kaima kana dojewa wannan yarinyar 'yar gidan Alhaji Sammani, wama take da suna? Bashmi ko bash kaka? kudai Luke iya wannan sunan na zamani,amma ka share bakama tayar da batun mikake nufi?". Aransa yace "wannan tsohuwar akwai tayar da zauna tsaye" amma afili sai yace "kai Hajo, ai tun alokacin na fad'a miki inason ta k'arasa karatunta ne, da tagama ta dawo gida baza aja wani dogun lokaci ba za ayi auran kuwa ma ya huta nima in huta da gorin ki" "Nidai duk da wannan yarinyar bata kwantamin ba domin kwata-kwata banason had'a iri da wad'annan zuri a, dan dai ka kayamin dalillai kane, kasa manya acikin maganar abiya komai da komai yazan lokaci kad'ai za asanya da tadawo sai ayi bikin " "Bakida matsala zanyi magana dasu Abba in sha Allah duk abinda sukace dashi za ayi" cewar Mansur "Koda naji" Hajo ta fad'a domin ita harga Allah batason zaman sa ahaka, to idan kingama maganar taki ina abinci na? domin wallahi jina nake Kamar main satar d'iyan hanji" dariya Hajo tayi tare da dad'in idan har amma satar hanji ai ba wannan labarin akeyi ba, domin bama zan ganka anan zauna ba har kana fad'a ba,da tuni likitoci nakai kawo akanka" yanzu Nasan mai suna ta isa yin bacci nasanta da saurin kwanciya, jeka kicin ka d'obo wadda kasan zai isheka" "Kai Hajo, duk wannan gajiyar da na kwaso zakisani kicin in d'auko abinci". Kallon amma wannan yaron ka rainani ta masa Kafin tace "yanzu kai saboda Allah ko iyayan ka sun isa su sani aikin da banyi niyaba, matsayin ka nawa? baga Amfanin auran ba? da matar kace har hannu za awanke maka kana azaune azaune har awakenma hannu" Yace "ke yanzu matsayin wa kike ba matar takwana? kuma ki jira kigani, duk ranar da matar tawa tazo bazaki k'ara ganina wajanki nazo cin abinci ba" yana k'arasa fad'a ya mik'e yayi hanyar kicin domin d'auko abincin, bayan ya d'auko yaje ya d'auko ruwa masu madai-daicin sanyi yazo yasami wuri anan k'asa ya zauna, zama cin abincinsa yayi bai koma cewa da ita uffan ba' itama Hajo fita batunsa tayi har yagama cin abincin ya mik'e yana Mata saida safe' "Allah yabamu alheri" tace dashi tana gyara kwanciyar ta akan dugunwar kujera' wa'azin take jiran ya k'arasa itama taje ta kwanta. Mansur yana shiga d'aki wanka ya shiga yasakeyi yayi shirin bacci yazo ya kwanta asaman gadon sa da yagaji da had'uwa sai kace wani d'akin d'iya macce, maccen ma 'yar gata, tunani ya fad'a ciki, wadda baisan wani irin lokaci ya d'aukesa ba, harma baisan lokacinda bacci yayi awon gaba dashi ba, kiran salla ne ya tayar dashi wadda yaji acikin kunnuwan nasa, tashi yayi yayi alwalla ya fita zuwa masallaci, bayan angama sallar saida ya tsaya yayi azkar na tsawon wasu mintuna sannan ya fito zuwa gida' yana fitowa ya had'u dasu Abba da alama suma yanzu suka fito, gaidasu yayi suka amsa cike dason yaron nasu Anan Abba ke tambayar sa ina ya shige? tun jiya da safe rabonsa da yasanyasa a idanuwansa. bayan kun dawo daga makarantar ina kashige? nan yake gayamasa yaje yin wani aiki ne, bayason ya koma office bai k'arasa saba. "Ok shikenan Allah ya taimaka" da amin duk suka amsa shida Dady' suka d'unguma sukayi cikin gida, Hajo suka shiga sukawa barka da safiya suka d'an ta'ba fira kafin kuwa ya tashi ya nufi part d'insa. Yana shiga d'akin sa bacci ya koma domin bacci ne a idanuwan nasa. BAYAN WANI LOKACI Acikin wannan tsakanin ne su Mansura suka fara rubuta jarabawa, gaba d'aya sun maida hankalinsu akan wannan jarabawar. Aunty Hauwa kuwa tun lokacin da suka had'u da Mansur a asibiti har ya dizgata bata k'ara ganinsaba, duk da har wannan lokacin sonsa nanan dan k'are acikin zuciyar ta, saidai ta fuskanci d'an dizgine, amma tana rokon Allah idan alherine agareta Allah ya tabbatar, idan kuwa shi d'in ba alherine ba agareta, Allah ya yaye mata son nasa ya za'ba mata mafi alheri, dan Aduk abinda su Mansura suke fad'a akan sa bata ta'ba sanin haka yake ba sai alokacin da ya gunta mata kad'an daga cikin halin nasa' haka zata zauna tayi ta tunani harma ta tambayi kanta da kanta awani lokaci, wai miyasa zuciyata zata kamu da matsananciyar Kaunar sa? miyasa take son wadda ma baisan tana haukar son nasaba? zuciyata bakimin adalciba son wanda baisan danayi ba,haka zatayi kukanta sai ta k'oshi ta share hawayanta, duk tarame ta fita haiyacin ta kuma takasa koyawa kanta yadda zata cirewa kan nata sonsa, har yaso ya shafi karatun nata, saida tayi yak'i da zuciyar ta sannan ta samu tayi wannan jarabawar. Sun sami hutu na kusan wata d'aya, ko wace d'aliba ka gani fuskar ta cike take da farin ciki akan zasuje suga iyayannansu. Su Mansura tun adaran ranar suka gama shirya komai nasu safiya kawai suke jiran tayi azo ad'auke su' adaran sabuwar fira suka aza sai gwani sarkin sata yazo yayi awan gaba dasu, kiran farko suka farka suka shiga k'ara kintsawa, ana tayar da salla masu sallah suka shiga suka d'aura alwalla suka tayar da salla, wad'anda basayi suka shiga wanka, saida suka gama gaba d'aya sannan suka zauna sukaci gaba da hira da amsar lanbobin iyayan nasu domin sudinga jin junan su. Can Zainab tace "nifa banga mai maganar break fask ba acikinku, kuma wallahi nidai har ga Allah yunwa nakeji tsakanifa da Allah" dariya sukayi gaba d'ayan su Asma u tace "to acici mala inkun tauna, kefa gaba d'aya boyar ciki kike, sai kitashi ki d'aura dan nidai d'auki bazai barni ba in wani tsaya aza break fask ba ehe", duk da itama fa yuwar takeji. Tashi Zainab tayi ta d'au indomi tana fad'in "bari inga idan angama inga wadda zaice zaici yaga inda ainahin rashin nasiha yake" Rukayya tace "badaniba bari kiga" ta sauko tana taya ta. Saida suka gama kuwa ya karya sukaci gaba da rahar su, karfe takwas da kusan rabi aka fara zuwa d'akar wasu daga cikin d'alibban makarantar, acikin su kuwa Asma u ce farko zuwa d'auka, ta tafi suna farajin kewar junan su, kusan karfe tara saiga motar gidan su Mansura itama tazo, Yaya Abdullah ne shida direban gidan, shima dai yayan Rukayya ne bayanan lokacin da aka kawosu yana wajan karatu a A.B.U Zariya, ba k'aramin rud'ewa sukayi da ganin saba, shima yaji dad'in ganin 'yan kannan nasa sanyin idanuwan sa da yayi, suna cikin wannan farin ciki motar gidan su Zainab ta k'araso, nan kuwa ya shiga motar gidan su suna masu kewar juna da alk'awalin kiran juna sannan suka kama hanyar g... ~Mom surayya~ [2/15, 11:31 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=wwt Typing MANSURA BY:SARATU MUHAMMAD MOM SURAYYA Page 22 Acikin motar ma ba abinda su Mansura keyi sai jansa da surutu shi kuma yana biye musu,danshi haka yake, zai zauna da 'yan k'annasa yayi ta hira,dan haka gaba d'aya acikin yannansu maza sunfi sakewa dashi, gashi bayada zafin hannu,domin zai dad'e bai sawa mutun hannu ba, amma kaiko kar kayi fatar ya dank'eka. Rukayya ce tace ''wai Yaya dan Allah yaushe kadawo?'' K'aramar dariya yayi kafin yace ''yau k'wanana yau ukku da zuwa, kuma inajin labarin dawowarku hutu nace in sha Allah nine wadda zai d'aukoku, domin nasan zakuyi farin ciki da haka''. Mansura tace ''amma yaya kaji ba dad'i da kaji ance an kaimu bodin?'' ''K'warai naji ba dad' sosai,domin nasan k'annen nawa yarane,amma kuma da nakira yaya gamai da kaiku mskarantar, rufeni yayi da fad'a dole naja bakina nayi shiru''. Mansura tace ''bak'in mugu kawai, Allah zai saka mana,kuma burinsa bai cikaba, maimakon zalittarmu da yasu ayi sai yaga sa'banin haka. "Kedai Mansura bakinki baya ta'ba shirya, yanzu bagashinan har kun Sababa" ta'be baki tayi tare da turoshi gaba sannan tace "kaidai Yaya ayi sha'ani kawai" dariya yayi har yana bugun gefen kujera sannan yace "kinganeki, wai ayi shani" hakadai suka ci gaba da hirrarsu cikin raha har suka k'arasa. Gaba d'aya gidan taruwa sukayi apart d'inHajo, domin murnar dawowar 'yan jikokinta abin alfarinta, su Mansura sai zuba surutu ake kamar ba itaba saboda ganin kanta da tayi cikin 'yan uwanta,abincine kala-kala aka girka musu harma su kasa wane zasu faraci aciki, Ummi ta kalli Mansura tace ''ni banga 'ya'yan nawa banga alamar suna wahala amakarantaba anya kuna karatu amakaranta kuwa?'' Hajo tace ''nifa Mariya banason sa ido, mikika gani har kikasa musu ido?'' ''Yo hajo ganin nayi sunyi luwi-luwai abinsu kamar wad'anda bakaratu sukaje ba''. ''Todai idan nagane kinamin bak'in ciki da ganin Sunyi jiki ba ramaba, yadda akaso ganinsu ba haka aka gane ba, sai nad'aura bin dare ina musu addu a kar baki ya kamaminsu'' dariya duk 'yan cikin d'akin sukayi kan maganar da Hajo tayi. Nandai sukaci sukasha sannan aka ak'ara zaman bajakullin hira har tsahon wani lokaci kafin kowa ya kama gabansa. Mansur kuwa tun karfe bakwai nasafe yabar gidan, dukda kuwa yasan da dawowar 'yan makarantar amma yayi tafiyarsa,dan yasan baza arasa wadda zaizo d'aukosu, Abdullah ko direba zaije d'aukosu, bai dawo gidanba sai bayan sallar azzahar,koma koda yadawo bai shiga part d'in Hajo ba ya shige nasa, dama yayi sallar sa tun awaje, wanka kawai yayi ya kwanta