Sashe 32
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akan wannan auran, domin da tana samun dama da taje anyi da ita, to amma ba wannan damar saboda kwana biyu da fara jarabawar za a d'aura aure. Mansur gaba d'aya bai maida hankali akan wannan auran ba saboda ba wani shirye-shiryan da yake akan bikin, ko katin gaiyata baiyi ba saidai jabir ne yayi yarabawa duk wanda yadace abawa. Ankai kaya nagani na fad'a, kayan da duk wanda yagani yasan an kashe nera awajan, ba laifi yazuba nera saboda mutane sugane auran soyayya sukayi. Lokacin da Mansur yasamu labarin party da zatayi yace baza ayi ko d'aya ba, tashiga damuwa saboda tazuba buri awajan partyn, taso abuga capacity sosai awajan, ba lallashin da bata masa ba akan yabari ko guda d'aya ne ayi amma yqce san, kuma idan ta kuskura tayisa zataga 'bacin ransa sosai, zai nunamata ainahin kalar s... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 33 Rana bata k'arya saidai uwar d'iya tayi kunya inji masu karin magana, to wannan haka yake. Ayaune dubbannin mutane suka sheda d'aurin auran Mansur Idris da Hauwa u Abubakar Sammani wato (Bashhama) auran da yasamu halattar manya-manyan bak'in musamman ta 'bangaran mahaifin nata da wajan aikin su Mansur, domin ba laifi Jabir ya gaiyaci mutane harma abokansu na sakandiri aiko yasha harara awajan Mansur dan baisan duk yayi wannan gayyatar ba, dariya yayi yama kauda idanuwan sa akansa. Bayan agama suka kai sauran abokannisu na nesa masauki sukaci sukasha, domin suma zuwa sha biyu zasu wuce tunda gogan yace ba wani even da za ayi, itama dakyal da lallashi aka ya bari zatayi kamu, amma bayan shi bai yarda ayi komai ba, Jabir yace "hakan ma babu laifi, kasan yanzu mutane zasu iya cewa aure sai kace bana soyayya ba" Ycace "soce, ni dama amfad'a makane inayin abune dan mutane suyi magana? ba abinda yasha min kai da maganar mutane kaji" dariya yayi yace "mudai shikenan tunda ka bari ayi" Bashhama da tasha kyau cikin adon ta da taji labarin an d'aura ta rungome k'awarta dake kusa da ita tana sakin ihu har suna bid'ar fad'uwa, jin take yau ba wadda yakaita sa'a aduniyar nan na mallakar abin da takeso "Bashhama miye haka? kadamu kikeson yi komai?" cewar k'awar tata "Bazaki ganeba Jancy, yau jina nake kamar wacce ke yawo asararin samaniya, wai ace nice aka d'aurawa aure da Mansur, wallahi ko! da bai hanani even ba da sai an zuba capacity, gashi nagama baza zanyi party kala-kala amma ya zanyi" Wacce akakira da Jancy tace "aini bakisan irin haushin da najiba nasa, ya za'ace gudan auran ki baza ayi dina ba, ni narasa wani irin sone kike masa" "Wallahi nima kaina narasa wani irin sone nake masa, ki duba kigani irin walak'anci da nasha nasa kafin ya kar'bi tayin soyayya ta, amma daniyi hank'uri rana d'aya yacemin ya amince zai aure ni, gashi kuwa yau yazama mallakina" "Hakane kan saidai ki samu sa'ar juyashi kamar waina atanda" cewar k'awar tata "To ameen dai" wayar ta ta d'auka ta rubuta masa I love you my husband ta maida wayar ta ajiye "Kardai kifeye zak'ewa da yawa,dan naniji buhun k'aya ne duk yadda ka d'auke su sai sauke baka shirya ba saboda sukar da zasuyi maka" cewar Jancy ganin rawar kan da takeyi akan Mansur, wadda cikin k'awayan nata ba wanda baisan itace mai sonsa bashi ba, gata da tarin masoya amma tanacewa wadda bai damu da itaba. "Ya zanyi Jancy? son sane yariga yamin mugun kamun da nima bansan ta yadda zan ciresaba araina, kuma ni ina ganin rayuwar sace ahaka, kefa ni tunda nake dashi ban ta'ba ganin shi tare da wata macce ba da sunan soyayya ko inji yana hirar wata shi kawai aikin sa yasa agaba, idan yana aiki ba wadda yake saurara sai yaga ya gama sannan sai in abin mai muhimmanci ne sannan fa zai saurare ka" Baki Jancy ta ta'be tace "nidai na fad'a miki kibi asannu" hirar tasu ta katsene lokacin da k'awayan su suka shigo suna tsokanar ta da amarya amarya. Mansur da tunda aka d'aura aurannan yakeji wani iri gashine, har wani abu yakejin yakejin masa tsaye a zuciya, kamar ya ke'be kansa yayi ta kuka har sai yasamu sassaucin da yakeji, amma ahakan ya daure ya zauna cikin abokannin nasu suna fira, saidai duk wadda ya ga fuskar sa sai yasan akwai abinda ke damunsa, har wani daga cikin abokan nasa take cewa "Wannan wani irin agone fuska amurtuk'e sai kace wadda akawa auran dole kodai akwai abinda ke damun kane?" hararar sa yayi yace "Lawal bakada mutunci mi zai damine kuwa! kaifa nasan halin ka da gulma sai kace macce" Wadda aka kira da Lawal yace "eh naji d'in, ade saki fuska kar ajewa amarya ahaka taji tsoro tabarka ka kwana gwarro bayan da matar ka" filo ya d'auka ya jefa masa yana fad'in "shigen kaya, ainan kafi karfi, ni kaga tafiyata kar ka'bayamin tarbiyar dasu Hajo suka bani" ya fad'a yana tashi dan gojewa suruntun nasu, dan Allah yasani daureya ne kawai yakeyi, dariya dukaninsu sukayi shi kuwa yace "idan ni ban 'batama tarbiya ba yau Bashhama zata 'bata maka ita" shidai baiko juyoba yayi ficewar sa, Jabir ya tashi yabi bayansa. Tun kwana biyu ya rage d'aurin auran akayi jeri na gani na fad'a agidan da yakama musu, dan iyayanta sun kashe mata nera ba karya,yawancin kayan ma duk nawajene k'alilan ne na nan gida najeriya, shima da yake gidan ba k'aramin gida bane sai komai yazama gwanin sha'awa, wance part d'in Hajo tace wallahi ba nata bane dan haka bazata zauna acikinsa ba saidai ya kama haya, shima hakan yafi masa tunda ba wani dugun zama ne zasuyi ba da yasamu abinda yakeso ga mahaifita zai kad'a ta gaba, shi harma tausayin kansa yake yadda zai zauna da ita awaje d'aya. Baisan Jabir na binsa abaya ba saida yakai zaune akan kujerar dake wurin zama na shak'atawa "miye nabiyoni kuma bayan nabar muku d'akin" dariya Jabir yayi yace "Maida wuk'ar Malam ni shawara kawai nazo nabaka in zaka d'auka" "Karik'e shawarar taka bana so, shawarar d'in taka ta banza, dan Allah jeka kabani waje inason in huta" "Wannan ne kuma baka isaba wallahi saina fad'a, inma ka d'auka dan kanka idan ma baka d'auka kaine kajiyo, dama abinda zance ma kadinga sassauta wannan d'aure fuskar da kakeyi in baso kake kuwa yagane ba auran soyayya kikayi ba ko yayane kad'an saki fuskar ka" idan kujerar da yake kai tayi magana shima ya tanka, illama baya da ya bashi. Da taga abin nasa da gaskene yayi gaba abinsa da mamakin halin Mansur wani lokacin. Ankai amarya gidan ta da k'awayan ta sai shak'iyanci suke mata, itako ba abinda take sai murmushi tana maijin fargaba acikin zuciyar ta, dukda tasan ta dad'e da tushe 'barakar amma wallahi data tuna gabanta fad'uwa yakeyi,haka manya suka watse suka barta da sauran k'awayan nata, wad'anda sai angaye sunzo zasu tafi, ba abinda sukeyi sai santin gidan wasu daga cikin su bak'in ciki dank'are acikin zuciyar su, wasu kuwa kiran suke zuwa zasuyi su fidda d'aya daga masuson su su shige daga ciki, domin su tabbatar da wannan harnyar ba mai bullesu bace. Angaye suna zuwa sukayi abinda zasuyi tare da basu abinda zasu basu suka d'auke su domin maidasu gidajansu, Mansur yazo ya rufe k'ofar bayan yamusu rakiya, Bashhama nanan zaune afalon bata tashiba, baice mata uffan ba ya shige d'akin sa ya turo k'ofar, ganin haka tabisa da kallo har tsawon wasu mintuna, ta d'auka shine zaizo yajata sushiga cikin d'aki yayi mata tarba irin ta amare suyi ciye-ciyan su tare da lallashin ta amma taga sa'banin haka, ledodin dake zube atsakiyar wajan tabi da kallo, Allah yasani tanajin yunwa bata wasaba domin zumud'i ya hanata kwata-kwata ta zauna taci abin k'warai, tashi tayi tabi bayan nasa ganin ko lafiya. Koda tashiga ya ahiga wanka dan haka ta samu waje ta zauna zaman jiran sa, zaman kusan minti 20 tayi sannan ya fito, da mamaki yake kallo ta na shigo masa d'aki Kai tsaye da tayi, wannan wace irin rashin kunya ne? baidaice komai ba ya k'arasa gun miro ya shafa mai tare da fesa turare sannan yaje ya shirya cikin kayan bacci, duk da duk abinda yakeyi atakure yakeyinsa domin yanajin idanuwan ta akansa, yasaba shi kad'ai acikin d'aki yake rayuwar sa, saida yagama duk abinda zaiyi sannan yace "Kije ki d'au leda nanan afalo kici abinda zakici kafin kin kwanta dare nayi, ni akwai aikin da nake son nayi kafin na kwanta" da mamaki take kallon sa kafin tace "Aiki kuma? a irin wannan rana husband, ai ina ganin duk aikin dake gabanka kamata yayi ka ajiyesa awannan ranar" hannuwan ta ta had'e waje d'aya tace "Dan Allah husband ka ajiye ko wane irin aiki ne sainan da kwana b... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 34 "Ke! kidakatamin da wannan suruntun naki na banza, ko an gaya miki na aureki ne duk ki tsaramin yadda zanyi rayuwa tane? ya fad'a cikin fushi har jijitar kansa na tashi alamar ransa a'bace yake. Bashhama data zabura da wannan tsawar da yayi mata da mamakin mi yashiga kansa da har yake mata wannan tsawar ta mik'e tana barin d'akin cikin sauri ta koma parlour ta zauna kan kujera "Anya kansa d'aya kuwa?"tayiwa kanta wannan tambayar da babu mai bata amsa, yunwar da takejine yasa ta janyo ledodin dake zube aparlour ta janyo, bud'ewa tayi taga abinda ke ciki, kazace wacce taji gashi mai kyau sai k'anshi take zubawa, d'ayar ledar kowa fresh milk ne da sauran kayan drink's wadda aikin Jabir ne dan shi gogan baima yi tinanin sayaba, saida suka shigone sannan yake mik'a masa. Zama tayi taci iyakar cinta ta d'au fresh milk tasha sannan ta tashi ta shiga dak'inta, kayanta tacire tashiga bayi tayi wanka tazo tasanya kayan da marabin da babu kad'an ne taje ta kwanta da tunanin komai dare zai dawo. Tsaki Mansur yaja lokacin da yaga fitar ta daga cikin d'akin, bin bayanta yayi ya sakama k'ofar key ya dawo yana zama kan sofar dake cikin d'akin, hannu yasa ya janyo laptop ya bud'e