← Book details Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 42

Sashe 38

Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansan lokacin dana fara sakin wata razananniyar qara ba,
Gaba
aya mutanen
akin suka juyo suna kallona niko jina nakeyi kamar na haukace saboda zafi da ra
in wannan rana bazai ta6a gushewa ba kuma bazai ta6a misaltuwa ba,
Tun ina ganin mutane sun rabu bibbiyu har nazo nafara ganin dishi dishi daganan ban qara Sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi naganni a gidanmu mutane kuwa sun cika gidanmu sosai kowa yana fa
in kyawawan hali irin na mamanmu,
Farkawar da zanyi sai naji mutane suna fa
in, Allah sarki yanzu yaran nan basuda uwa basuda uba oh maraici gaba da baya ,
Da sauri natashi cikin matsanancin kuka sai naji mutane suna fa
in, wayyo kunga babbar yarinyar ta nan, Allah sarki fatima kiyi haquri kinji Allah yazama gatanku ,
Nikam ko ba'a fa
a mun ba nasan cewa mamanmu ta rassu nasan cewa mun rabu da mamanmu nasan cewa bazan qara ganinta ba Amma tabbas inaji A jikina nima bazan da
e ba zan bita saboda bazan iya rayuwa babu ita ba koba komai nasan baqin cikina shine silar mutuwar mamanmu ,
Runtse idanuwa na nayi inajin ra
in rabuwa da mahaifiya tabbas A yau nayarda cewa mutuwa tanada ciyo tunda narasa mamanmu ,
Kukan danake son inyi sai gashi A yau nakasayi sai dai zan iya cewa har qara inyi kukan da irin ra
in da nakeji a yanzu lallai idan wannan ne kukan zuci to nayarda kukan zuci yafi na fili ciyo ,
Na da
e A haka sai naji mutane suna yimun magana Amma ni hankalina baya wajensu saboda ko fahimtar su banayi,
Can kamar A mafarki sai naji wata tana cewa" fatima kije kiyima mamanku Addu'a saboda an shiryata yanzu za'a fitar da ita mutane suna jiran ayi Mata sallah ",
Gabana naji yayi mummunan fa
uwa sai nakejin kamar yanzu ake fa
a mun cewa mamanmu ta rassu , nan take hankalina yayi mummunan tashi kamar an tsikareni aiko nayi yunqurin tashi cikin kuzari da fa
uwar gaba naje
akin da aka shirya mamanmu,
Ina shiga
akin sai naga mutane sun kewaye mamanmu wasu
an uwan ta ne niko nan take naji duniyar tayi mun duhu da sauri na nafa
a a jikin mamanmu ina kuka ina roqon ta gafara,
Wata qanwar mamanmu ce ta 6an6areni daga jikin mamanmu tana fa
in "haba fatima Addu'a yakamata kiyi Mata ba kuka ba ",
Kaina nake girgizawa ina fa
in ,Wallahi da gaske mamanmu ta rassu ta tafi ta barmu Ashe da gaske ne mamanmu nazaci zaki farka sai naga har yanzu baki farka ba dan Allah mamanmu kitashi haka karsuje su binneki ",.......

Sukam mutane da sukaga sambatuna yafara yawa sai suka kamani suka fitar dani
akin da qarfinsu niko sai tirjewa nakeyi ina kuka ,
Haka suka riqeni sukaqi sakina ina kallo aka fito da gawar mamanmu cikin mankara wani tunani yazo mun cewa yanzu shikenan bazan qara ganin mamanmu ba har abada aiko ban qarasa tunanina ba naji numfashi na yafara sama sama nan take kaina yafara juyawa daganan ban qara sanin inda nake ba ban kuma san wainar da ake toyawa ba,
Bayan wani dogon lokaci nafarka naganni Ana yimun qarin ruwa kuma da alama dare yayi sosai aiko bansan lokacin dana fizge qarin ruwan ba ina nan take abubuwan da suka faru
azu yafara dawomun ,
Dafe kaina nayi da zuciya ta saboda irin ra
in da nakeji da qyar natashi naje nayo alwala a nan tsakiyar gidanmu nazo na tada sallah saboda inason zanyi ramuwar sallah ,
Haka cikin daren nan na rinqa sallah ina kuka ina roqon Allah yasa mamanmu ta dace,
Su kuwa mutane duk abun nan danakeyi babu Wanda yasani dan barcin su sukeyi harda minshari jin nayi indama ace daga barcin nan kowa ya mutu,
Da asuba ina zaune kan dadduma idanuwa na duk sun kumbura sai naji qanwar babanmu tana fa
in "Bisimillahi shigo ai jikin nata da sauqi ",
Juyowar da zanyi sai naga Dr Sageer ne wai ake cewa yashigo,
Da sauri na kauda fuskata daga kallonshi sai naji qanwar mamanmu tana yimashi godiya kamar zata duqa mashi saita juyo gareni tace
" Fati kiyima bawan Allah nan godiya wallahi duk hidimar da akayi jiya shiya
auki nauyi tundaga abinci har ruwan sha da lemo ke harda kula da lafiyanki duk shi ya
auki nauyi",
Wani mugun takaici ya kamani lokacin danaji tace wai inyima mugun nan godiya abun qarin takaici wai har hidima akayi kenan bansani ba,
Wasu zafafan hawaye suka zubo mun cikin raina nace lallai gidan mutuwa ya koma gidan biki haddasu lemo ,
Kaina nasa A qafafuna ina kuka ni saboda takaici banma San tafita ba sai jin nayi Dr Sageer ya rufe qofar da sakata duk da haka ban
ago kaina ba sai naji Dr Sageer ya duqa gabana yasa hannuwanshi ya
ago mun fuska ,
Da sauri na buge hannun Shi iya qarfina duk da haka nakasa magana sai kuka nakeyi sai naji yace" fatima ya haqurinmu ?

Dan Allah kirage damuwa kituna cewa Wanda ya bamu mamanmu Shi ya ansheta kuma yafimu sonta ",
Wata muguwar harara nayi mashi har saida yayi shiru yana kallona cikin muryan kuka nace mashi " qarya kakeyi Sageer kai harni zaka fa
ama Allah ?

Ai bakasan Allah ba baqin cikin mu ne ya kashe mamanmu kuma inaso kasani wallahi babuni babu kai har abada mugu kawai azzalumi ",
Duqar da kanshi yayi qasa batareda yacemun komai ba saida mukayi wajen Mintuna goma sannan yace" fatima dan Allah kiyi haquri da abubuwan da suka faru tsakanin mu tabbas nasan ban kyauta ba nayi amfani da son da kike yimun na keta maki haddi kuma nasakaki cikin baqin cikin da har ki mutu bazaki manta ba Amma insha Allah nayi maki al'awalin zan riqeki amana nidai fatana idan kin haihu lafiya kiyarda muyi Aure dan mu gina rayuwa mai tsafta" ,
Wani baqin ciki naji ya kamani danni harna manta cewa inada ciki kuma cikin ikon Allah cikin bai ta6a motsi ba Amma A yanzu sai naji marana tana harbawa da sauri da sauri kuma sosai,
Ni kuwa da cikin da Dr Sageer
in ba qaramin haushi suke bani ba dan haka cikin 6acin rai nace" wallahi Sageer bazan ta6a iya auren fasiqin mutum ba ",
Duqawa yayi har qasa sai naga idanuwanshi sun ciko da hawaye niko nayi saurin kauda fuskata sai naji yace" Wallahi wallahi wallahi kinji nayi maki rantsuwar musulmi wallahi fatima ban ta6a sanin wata
a mace ba saike ban ta6a sex da kowa ba sai ke kema kuma qureni kikayi kituna kinyi mun magana na qyaleki picture
in bress
inki da kika turo mun shine yaja hankalina Amma wallahi ni ba mazinaci bane nidai nasan ina qoqarin kare kaina da fa
awa cikin zina banason in aikata zina Amma fatima ke kika turo mun picture
in bress
inki Wanda hakan yasa nakasa control kaina Cox ni cikakken namiji ne kuma mabuqaci kinga idan haka ne ke kika jefani cikin zina",
'Daga mashi hannu nayi alamun ya isa haka duk da nasan yanada gaskiya tabbas lokacin danayi mashi magana ko kulani baiyi ba abokinshi ne yabani shawarar intura mashi picture
in bress
ina yafa
a mun cewa Dr Sageer baya kula
an Mata Amma idan natura mashi brass
ina mayb indace ya kar6i soyayya ta duk da cewa lokacin son Dr Sageer ya rufemun ido,
Dagani har Shi babu mai magana sai can naji yace" fatima dan Allah kiyafe mun ",
Tsaki nayi cikin
aga murya nace mashi " wallahi bazan ta6a yafe maka ba kuma kayi gaggawar barin
akin nan dan karkayi mun fya
e saboda saboda bunsuru babu ruwanshi duk inda yaga dama Abu
aya yakeyi dan haka kafita ko kuma inyi maka ihu kuma in tona Asirin duk abunda ya faru tsakani na da kai ",
Kallo na yayi tareda ha
iye miyau na baqin ciki sai yace mun" idan dai ni bunsuru ne to ai kece Akuyar sannan idan ke
ar halas ce dan Allah kiyi ihun yanzu kuma banason ki rufe duk wani Abu daya shiga tsakanin mu dan naga ke har yanzu quruciya gareki ",
Dummmm naji nayi nakasa magana saboda banida abunda zance sai naga ya qara matsowa kusa gareni ya dafa cikina yace " kuma Dada qanwar babanmu kenan yanzu zata kawo maki abinci inason kiyi gaggawar cinyewa sannan kishirya next week zaki fara zuwa Awo Anti-natal ",
Yana gama fa
in haka sai naga ya bu
e qofar yayi tafiyar shi babu tsoro ko fargaba a taredashi ,
Dafe kaina nayi cikin raina nace yanzu inda mamanmu tana nan bai isha ya shigo gidanmu ba Amma dayake
an uwan babanmu ya cikasu da ku
i gashi har
akina ake kawoshi harda fa
in wai inyi mashi godiya,
Tabbas nasan
an uwan babanmu sunason ku
i shiyasa lokacin da babanmu yana raye kusan duk sati sai sunzo saboda yana basu ku
i kuma yana taimaka masu Amma tunda ya rassu suka daina zuwa yanzu kuwa idan suka samu Dr Sageer ai nasan zasuyi murna saboda zai cikasu da ku
i duk dan yasamu biyan buqatar Shi duk da cewa daman can mutane sun shaideshi cewa shi ba marowaci bane,
Nikam duniya tayimun muni narasa uwa saboda abun kunyar dana sakata tabbas nasan baqin cikina ne ya kashe ta lallai zina babbar masifa ce,
Wani mugun takaici ya kamani lokacin danaji cikina yana motsi aiko cikin fushi nasa hannuna na daki dai dai inda yake Motsin ,..............
*Ummu meenal ce
[5/4, 5:40 PM] Sis Naja Atuh: *
LAIFI NANE
*STORY FATIMA*
*WRITTEN BY MRS SADEEQ*
*(Ummu Meenal*
*DEVOTED TO MARYAM AMINU JUMARE(Majmiy)*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours best out of the best,, our inks are melodious and droping a kinda lights to reader's}*
THE PEN OF LOVE
HEART TORCHING
TEARS OF SORROWS
CURDLES
GIGGLES
AND MARRIGE
*JUST GIVE US FOLLOW.....
Chapter 38 · 0% Book details