← Book details Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 42

Sashe 27

Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikenan bazan tilas taki ba amma inason kisani nima nabar iyaye na akanki Amma tunda baki yarda dani ba kince bazaki kwana ba toni bansan inda kikeson kwana ba dan haka ga hanya nan kitafi duk inda zakije bazan hanaki ba Abu
aya ne ban yarda ba wallahi fatima idan kika bawa wani namijin kanki dagake har shi saina illata ku kuma karkiyi tunanin cewa bazan gane ba zan gane wallahi ",
Ni kuwa kuka kawai nake wiwi shi Dr Sageer sai naga ya
auko wani key yace " gashi kiyi amfani dashi dan nasan zaiyi maki amfani key
in gidan nan ne idan kin tashi kishigo kai tsaye ",
Nikam bance komai ba sai kukan danakeyi A gaskiya Dr Sageer yanada zafi sosai abun daya qara bani haushi wai idan naje nayi sex da wani
a namijin zai gane tabbas zargi ya shiga tsakanina da Dr Sageer idan qaddarar aure ta ha
a ni dashi lallai zansha wahala sosai,
A zuciye nabar gurin batareda na anshi key
in gidan ba inaji yana qwala mun kira Amma naqi ko juyowa,
Nikam tafiya naci ga dayi Amma abun haushi bansan inda zanje ba gashi dare yayi dan tun ina qofar gidan Dr Sageer akayi mangrib,
Hankalina ya fara tashi gashi babu mutane a unguwar irin silent Ariya ne ni kuwa tafiya nake dukda cewa bansan inda zanje ba ,
Abunda ya razana ni ha
e da tayar mun da hankali shine wasu manyan karnuka nagani a gabana Sun biyo hanyar inda nake ni kuwa gashi ina masifar tsoron kare dan haka da sauri na juya baya na naga wajen babu kowa hankalina ya tashi kawai saina juya na koma hanyar gidan da Dr Sageer yace in shiga,
Sauri nake sosai ganin karnukan Sun kusa isowa inda nake Dan haka da sauri na
auko waya na nakira Dr Sageer aiko nayi sa a ringin
aya ya
auka yana fa
in, daman nasan za ayi haka gani nan zuwa,
Ko magana banyi ba Dr Sageer ya kashe wayar ni kuwa saina tsinci kaina da nadamar kiranshi Amma kuma babu yanda zanyi dole saina kirashi Danni yanzu Dr Sageer ka
ai ya rage mun mai nuna kula dani ,
Tun kafin in qaraso gidan Dr Sageer ya fito cikin gidan ya biyo hanyar da nake aiko ina ganinshi sai nayi saurin isa wajen shi na 6oye a bayanshi Amma abun mamaki ko ka
an Dr Sageer bayajin tsoron karnukan saima turanci danaji yayi masu ,
Juyowa yayi ya kalleni yace" matsoraciya to muje kinyi sa a yanzu nadawo naje na siyo bargo tareda
ar siyayya ",
Bance mashi komai ba har muka shiga cikin gidan dayake *barakallahu* sabuwar unguwa ce datake garin gusau ,
Gaskiya gidan yayi kyau sosai komai akwai Amma yanayin gidan yakamata ace akwai mace cikin gidan,
Saida muka shiga babban falon naga yanayin tsaruwar falon ya burgeni kamar falon wani gomna aiko na juyo na kalli Dr Sageer nace" doctor nan gidan waye ?"
Murmushi yayi yace" teema na nada
e da kammala wannan gidan da niyyar inyi aure Amma dad ya hanani yace dole saina qaro karatu sannan gashi Kema yanzu kina barazanar hanani auren ki tunda kinqi yarda muje wajensu babanku",
Murmushi nayi batareda nace mashi komai ba amma a raina tabbas nayarda Dr Sageer yanason aure na tunda harya matsa sai munje wajen dangin babanmu ",
Juyawa nayi na kalleshi lokacin yana saka lemo a prich nace" ba haka bane doctor kasan nafa
a maka mamanmu tace idan naje gidan bata yafe mun ba",
"Hakane Fatima Amma Ai kinsan inada buqatar ki dan dole zaki yarda da auren nan idan ba haka ba hmmmm bance komai ba",
Ni kuwa raina ba qaramin 6aci yayi ba saboda A rayuwa ta na tsani Dr Sageer yace mun yanada buqata ta idan yace haka sai inga kamar jikina kawai yakeso bani ba,
Saida yagama saka lemo da maltina cikin prich sai naga ya
auko man wata leda yabani yana cewa" gashi kiyi amfani dashi always ne nasiyo maki ga toilet can kishiga kiyi wanka sai kisa dan banason inga wannan jinin",
Ansa always
in nayi nashiga toilet batareda nayi magana ba daman always
in jikina ya dameni dan haka kai tsaye nashiga toilet
in,
Toilet
in kuwa Dana shiga yasha ado hardasu water hearter Amma duk da haka ba wannan ne buri na ba fatana dai murabu lafiya Nida Dr Sageer batareda yayi mun wani cikin ba,
*kuyi haquri da wannan ba yawa*
*Ummu Meenal
[5/4, 5:38 PM] Sis Naja Atuh: [2/1, 9:24 AM] Ummu Meenal: *
LAIFI NANE
*STORY FATIMA*
*WRITTEN BY MRS SADEEQ*
*(Ummu Meenal*
*DEVOTED TO MARYAM AMINU JUMARE(Majmiy)*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours best out of the best,, our inks are melodious and droping a kinda lights to reader's}*
THE PEN OF LOVE
HEART TORCHING
TEARS OF SORROWS
CURDLES
GIGGLES
AND MARRIGE
*JUST GIVE US FOLLOW.....

Https://mobile.Facebook.com/intelligent-writer's-Association-35077435465066/insight's/
*page 116-120*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Lokacin da mamanmu taganni tsaye da Dr Sageer A jikin motar shi hankalina ba 'Karamin tashi yayi ba nan take jikina ya fara rawa kamar mazari hawaye sosai suka fara wanke mun fuska ,
Shi kanshi Dr Sageer
in saida naga ya
an rikice duk da tsananin taurin kai irin nashi Amma duk da haka baiyi tafiyar shi ba yana nan inda yake,
Ni kuwa da naga takusa isowa inda muke hankalina ya 'kara tashi sosai dan haka da sauri nayi shigewa ta gidanmu ina kuka Dan nasan da wahala mamanmu ta yarda dani ,
Shi kuwa dr Sageer yana nan tsaye harta 'karaso inda yake bai motsa ba tana zuwa ta tsaya ta kalleshi sosai nan take ta gane fuskar shi ,
Shi kuwa baice mata komai ba itama batayi mashi komai ba harya shige gida ,
Lokacin da mamanmu ta iskeni cikin gida bata tsaya komai ba sai naga ta ajiye jakar makaranta ta nufo inda nake ta sha'ke mun wuya tana fa
" Dan ubanki Fatima Ashe bakiji abunda nafa
a maki ba ?

Ashe har yanzu ke 'yar iska ce ?

Yawon iskanci ne zuwa asibiti ?

Yau saina kashe ki cikin gidan Ashe daman idan naje islamiyya saiki kawo mun 'katon kwarto cikin gida ko ?

To yau Allah ya toni asirinki ",
Ni kuwa kuka kawai nakeyi nakasa magana sai girgiza kaina danakeyi ,
Wayar wuta mamanmu ta
auko tafara lafta mun tako ina a jikina ni kuwa sai hui nakeyi saboda azabar da nakeji dan har hijabina saida ta cire mun yanda zanji zafi sosai,
Bata da
e da fara dukana ba saiga Dr Sageer ya shigo saboda kukan dayaji nawa yasan babu lafiya ,
Yana zuwa kuwa da sauri yayi kanmu ya ri'ke hannun mamanmu da 'karfin shi yana fa
"Dan Allah mamanmu kiyi mata uzuri ",....

Bai gama maganar ba mamanmu ta wanke shi da Mari har guda biyu tana fa
" Ni zaku raina ma hankali Ashe daman duk lokacin da natafi islamiyya kana zuwa nan ne kuna iskancin ku wallahi fatima nayi nadamar haihuwar ki ",
Dr Sageer yace" wallahi mama Ban ta6a zuwa nan gidan munyi wani abu ba kuma wallahi rabon da inga Fatima tun ranar da nakaita gid"......,
"Rufe mun baki wawa wallahi ka cuceni yanda kayimun kaima sai anyi maka Allah ya isa tsakanina da kai, na da
e ina bawa yarinya ta tarbiya lokaci
aya ka tarwatsa ta bazan tax yafe maka ba Kuma yau Fatima saina kashe ki cikin gidan nan ",
Da sauri Dr Sageer ya kalli mamanmu sai yaga taje ta
auko wu'ka ta nufo inda nake,
Ai kuwa Dr Sageer yayi saurin tare mamanmu yasha gabanta,
Ita kuwa mamanmu dataga haka sai tayi saurin kaucewa da saurin ta tayo kaina da wu'kar A hannunta saura ka
an takai gareni da sauri shima Dr Sageer
in yayi wajen mu ya tareda ri'ke wu'kar inda kaifin ta yake saboda inda bai ri'ke ba da saita sameni,
Ita kuwa mamanmu sai murmuza wu'kar takeyi Kim kaifin ta yana hannun Dr Sageer Ai kuwa nan take tafasa mashi hannu jini ya fara fitowa ,
Ni kuwa danake tsaye ina kuka ganin jini a hannun Dr Sageer ya tayar mun da hankali da sauri nace" doctor kaduba hannunka jini yana fitowa",
Ganin nayi ya yamutse fuska da alama yanajin zafin shigar wu'kar a tafin hannunshi sai naji yace" ki matsa daga nan kar wu'kar ta sameki ",
Sai naga ya saki wu'kar ya ri'ke hannun mamanmu wanda ta ri'ke wu'kar yana fa
in " dan Allah mama karki kashe Fatima kiyi haquri dan Allah karkiyi kisan kai wa
lahi zakiyi nadama ",
Ita kuwa mamanmu harda rantsuwar ta yau saita kashe ni shi kuwa Dr Sageer ya ri'ke mamanmu sai ha'kuri yake bata yana cewa ta tsaya yayi mata bayani Amma firr ta'ki yarda ,
Ni kuwa sai kuka nake ina bata ha'kuri Amma Amma mamanmu sai fa
in takeyi saita kashe ni ,
Tabbas A yanayin 6acin ran mamanmu nasan zata iya kashe ni Dan na tabbatar inda Dr Sageer bai shigo ba wallahi da yanzu ta kashe ni ,
Ita kam mamanmu dataga bazata iya 'kwace hannunta ba sai tace" Fatima na sallama ki kije kicanja wata uwar babu ni babu ke Fatima Kinfi 'karfi na ",
Hankalina ya tashi sosai da jin kalaman mamanmu anan na ru
e saboda nasan wahalar danasha lokacin da mamanmu ta koreni daga gida rayuwata ta 'kara ta6ar6arewa cikin matsanancin kuka nace
" Mama kiyafe mun wallahi abunda kike zargi na dashi ban aikata ba a wannan karon tunda nadawo wajenki ban 'kara zina ba ko Kula maza banayi",
Murmushin takaici mamanmu tayi tace" Fatima sai yanzu nagane Ashe zuwa na islamiyya shine yabaki damar kawo mun kwarto cikin gida Ashe dama idan natafi saiki kirashi yazo kuyi iskanci ko ?
Chapter 27 · 0% Book details