← Book details Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 42

Sashe 19

Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma dad
in Dr sageer nan take yace a sallamesu su koma asibitin gusau kafin asamu biza doctors
in basuyi masu gardama ba suka basu sallama da fatan samun lafiya sosai,
Ni kuwa a ranar nayi kwanan wahala saboda ga yunwa tana damuna ga zazza6i ya rufeni sannan ga inda na kwana sauro yayi yawa kuma banida ko abun rufa lallai yau na qara tabbatar da zina ba qaramin illa bace yanzu kam kuka yazama jinin jikina ni yanzu harna Saba da kuka tun kukan yana zuwa yanzu ko zuwa bayayi sai dai zuciya ta tayi ta zafi,
Dana tashi da asuba ma da qyar nasamu ruwan alwala shima irin wanda yara suke ragewa ne idan sunzo dashi daga gida, nasamu nayi alwala nayi sallah na roqi Allah ya yafemun abubuwan dana aikata ,
Bayan nagama sallah sai kuma naji inajin kewar mahaifiya ta inda gida ne da yanzu naje na gaishe ta kamar yanda nasaba, jin nayi kamar inyi tsuntsuwa in koma gidanmu,
Ina nan zaune kan
an kwalina inda nayi sallah inata istigfarii sai naga haske yafara fitowa ganin haka yasa natashi da sauri saboda kar mutane su iskoni su zaci sata nazoyi ,
Da qyar natashi saboda banajin qarfin jikina haka nafita makaranta ina tafiya a hankali ,
Saida nafita makarantar ne Sai kuma narasa inda zanje gashi banida kowa a tsafe ,
Maganar mamanmu ce ta fa
o mun a rai inda take cewa innaje gidan dangin ta ko dangin babanmu bata yafemun ba,
Jin nayi zuciya ta tana suya ko ka
an banason in rinqa tuna irin kalaman da mamanmu tayi akaina ,
A haka nayita tafiya ina hutawa harna isa bakin titi da niyyar in hau mota in koma gida,
Wani abunda natuna dashi shine banida ko sisi na zuwa gusau gashi kuma ina kewar mamanmu inason inje in ganta mayb fushin da takeyi dani ya
an sauka akan najiya,
Tsaye nayi bakin titi narasa yanda zanyi nadamar abunda na aikata kawai nakeyi motoci kuwa sai wucewa sukeyi ni kuwa inajin kamar inshiga takaini gusau Amma babu dama,
Jikina kam a yanzu rawa yakeyi sosai saboda yunwar da nakeji kuma ga zazza6i inaji can na hangi wata mota aiko cikin rawar jiki nafara tsayar da ita duk da cewa kana ganin motar kasan ba motar haya bace ,
Su kuma mutanen cikin motar a guje suke sai kace ba a cikin gari suke wannan gudun ba abunda yasa suke sauri kuwa shine sunason sukai
ansu asibitin cikin garin gusau kafin su samu viser,
Ganin wata matashiyar yarinya tana tsaidasu yasa dad
in Dr sageer yayi saurin taka burki a cewar shi wannan yarinyar ta raina masu da wayo ta ina taga motar su tayi kamada motar haya,
Nikam zuwa yanzu na riqe cikina saboda mugun ciyon dayake yimun ga jiri ina gani,
Su kuwa suna tsayawa surayya tace" dad me zamuyi mata ?

Dad yace" bara muji ko sadaka take nema ko kuma muji rainin hankalin ta",
Mom kuwa cewa tayi" Dan Allah daddy surayya katafi ka qyale ta kana ganin my son yanajin jiki fa ",
Shikam Dr sageer ya kishingi
a a kujera idanuwanshi lumshe yanajin duk abunda ake cewa Amma yakasa bu
e idanuwanshi ,
Nikam dana leqa motar naga akwai mata sai nayi saurin cewa" dan Allah kutaimaka mun banida lafiya idan gusau zakuje nima can zanje kutaimaka kurage mun hanya",
Da sauri Dr sageer ya bu
e Idanuwanshi saboda yaji muryan da bazai ta6a mantawa da ita ba,
Nikam na daddage sai roqonsu nakeyi akan surage mun hanya sai jin nayi ance
" Fatima !

Daman baki tafi gida ba me kikeyi anan yana ganki haka ?"
Da sauri na kalli inda ake kirana sai mukayi ido hu
u da Dr sageer,
Raina naji ya 6aci saboda naganshi da iyayenshi cikin gata da kulawa duk da cewa Naga alamun buguwa a tare dashi amma hakan bai hanani jin haushin shi ba,
Kallon mahaifinshi nayi na kalli mahaifiyr shi babu tantama su suka haifeshi, lallai ma Dr sageer wato shi yana nan cikin danginshi ni kuwa nayi nisa da nawa,
Ganin nayi yayi saurin fitowa cikin motar yaja hijabina alamun inzo zamuyi magana ,
Ni kuwa mamaki yabani danaga alamun kamar bayason dad
inshi yasan alaqarmu,
Saida muka
anyi nisa dasu inajin dad
in Dr sageer yana kiranshi sai naga Dr sageer ya koma wajensu bansan meya fa
a masu ba sai naga yadawo gareni,
Yana zuwa waje na yace" teema na me kikeyi baki koma gida ba tun jiya?

Kuma naganki duk wani iri halan meya faru ?",
Nikam shiru nayi ina kallon shi takaici kamar ya kashe ni lallai A yau nayarda da maganar hausawa da suke cewa duk abunda
a namiji yayi ado ne,
Shi kuma dayaga nayi shiru sai yace" teema na Allah dai yasa baki bawa wani kanki ba saboda nawa ne ni ka
ai dan wallahi zan iya shari'a ga duk wanda kika bawa kanki ",
Takaici da haushin Dr sageer Sun kamani Amma yanzu bata wannan nake ba burina shine inje gida nima muyi sulhu da mahaifiya ta in roqeta ta yafemun in zauna gidanmu kamar kowa,
Jin nayi yace"teema na kiyimun bayani dan Allah wallahi banason shirun nan naki kinga ina tareda dad
ina karsuji haushi natsayar dasu",
Murya ta na rawa nace mashi" naje gida jiya nayima mamanmu bayani inada ciki shine ta dukeni kuma ta koreni tace kar in sake dawowa batason ganina ",
Ganin nayi ya
ora
ayan hannunshi a kai yace" innalillahi wallahi teema na kinyi wauta meyasa zaki fa
a mata kinada ciki ?

Kefa wani lokacin idan kikayi wani abu sai kace a film ko a novel to Amma tunda ta koreki yanzu ya zamuyi? kin amince da auren sirri ?",
Kaina nake girgizawa nace mashi " ina fa
a maka mama ta koreni daga gida kana yimun maganar auren sirri, ni bazanyi auren sirri ba wlh kawai inason ka kaini gida muje nida kai katayani roqon mama ta yafemun ",
Jin nayi yace" kefa har yanzu bakida wayo , Ai idan mukaje nidake zatafi jin haushinki harma tasaka korarki Amma idan kikaje me ka
ai zata iya yafe maki kuma tace ki zauna gidan",
Murya ta na rawa nace mashi banida ku
in mota sai naji yace inzo zasu kaini gusau sannan duk abunda Naga 'Yan uwanshi sunyi mun inyi haquri Kuma duk abunda naji yace a kaina kar inyi gardama ,
Banyi mashi magana ba muka tafi wajen motar Dr sageer yayi saurin bu
e mun baya inda su surayya suke ,
Ina shiga ya rufe motar sai naga yaje gaba kusa da dad
inshi ya zauna,
Jin nayi yace"dad kaga wacce nake fa
a maka nan daman inason in qara 'yar aiki Wlh ",
Ni kuwa saurin kallon Dr sageer nayi ina jinjina maganar wai nice 'yar aiki , cikin raina nace babu komai nima idan naje gida na roqi mama ta yafemun idan harta yafemun bazaka qara ganina balle kacemun 'yar aiki,
Ganin nayi surayya ta matsa daga inda nake tana toshe hanci ha
e da kawar da fuskar gefe tana fa
in "yaya ina kasamu wannan ?

Wannan Ai tayi maka qarama da aiki",
e rai naga yayi ya juyo ya nunata da yatsa yace" kinga surayya ni sa'anki ne ?

Wallahi ki kiyayeni idan ko kinason ranki ya 6aci kici gaba ",
Sai Naga dad
inshi ya jawo shi ya rungume da hannu
aya yana
an bubbuga mashi bayanshi yace" surayya karki qara cewa komai kinsan halin sageer hukuma saida lallashii bakiga a asibiti yaqi magana ba sai yanzu da muka ha
u da wannan yarinyar ba dan haka kibarshi duk abunda zaiyi da yarinyar nan yayi karki qara magana",
Dr sageer yayi saurin cewa " dad idan nace zan auri wannan yarinyar zaka barni in aure ta ?",
Murmushi dad yayi yana ka
a kai yace" lokacin auren ka baiyiba kasan tsarina inason ka qara karatu kabari idan lokacin auren ka yayi San fa
a maka kuma koda zakayi auren badai da irin waccan ba sai naga ya nunani da yatsa,
Shikam Dr sageer shiru yayi bai qara magana ba sai naji mom tace" alhaji yakamata kabar sageer yayi aure tunda yanaso ",
e rai dad yayi yace "bayanzu ba ",
Da haka har muka isa cikin garin gusau anan Dr sageer yacema dad ya saukeni wai inje in hahha
a kayana inaji dad yacema Dr sageer idan sunje gida zaiyi mashi bayanin inda yasanni har yakeson in zama mai aikin shi ,
Nikam ina fita daga mota shima Dr sageer yayi saurin fita ya anshi hand bag
ina ya bu
e yasamun ku
i yace gashi nan in hau napep Sai naga ya koma cikin motar,
Nikam zuwa yanzu yunwa ciki na taci harta fita daman ni bata abinci nakeyi burina shine inga nadawo da farin cikin mahaifiya ta nayi alqawalin mamanmu saitayi alfahari dani nan gaba fatana dai Allah yasa ta yafemun laifi na,
Napep nahau bamu tsaya ko ina ba sai gidanmu sai a lokacin naji gabana yana fa
uwa saboda bansan ya mamanmu zata tareni ba,
Ban tsaya 6ata lokaci ba nashiga gidanmu kai tsaye aiko ina shiga naga mamanmu da qannena a tsakar gida ,
Ina zuwa nafashe naje gabanta na durqusa na fashe da kuka na riqe qafafuwanta ina fa
in " mamanmu na tuba dan Allah kiyafemun wallahi bazan qara ba nashiga uku fushinki a gareni masifa ne kiyi haquri mamanmu ",.......
Chapter 19 · 0% Book details