← Book details Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 42

Sashe 2

Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A.W" ,
Hakan daya fa
a mun sai naji sanyi a raina dan haka ban 6ata lokaci ba nakar6i number dr sageer kamar yanda naji yafa
Shima anan yabani tashi number da sunanshi amir a cewar shi idan na dace inkira in fa
a mashi,
Haka mukayi sallama inajin da
i cikin raina,
Lokacin dana isa gida cikin ikon Allah jikin Aysha yayi sau'ki sosai dan harda
an wasan ta takeyi,
Ina zuwa nayima mamanmu bayanin 'karya nace ai dr yayi mata wasu allurai sannan yace basai tasha magani ba amma idan anga jikin yafara zafi to a ji'ka towel da ruwa mai kyau a daddana mata jikin sai kuma a bata paracetamol,
Mamanmu ta yarda da magana ta kuma taji da
i sosai tace aikinga 'kara da akaje asibitin yafi dan ayi maganin ciyon da gaggawa,
Nikam bance mata komai ba nayi saurin shiga
aki na dan inkira hubby na sunan danasa mashi a waya kenan wato *hubby na*
Ina zuwa na kwanta kan katifa na danna kiran number hubby na.........
*kubiyoni danjin cigaban wannan labarin mai ban tausayi da ban haushi*
*Ummu Meenal ce
*pls share*
[5/4, 5:36 PM] Sis Naja Atuh: *
LAIFI NANE
*STORY. ..........*
*WRITTEN BY MRS SADEEQ*
*(Ummu meenal)*
*True lyf story*
GORGEOUS WRITER'S FORUM
*Home of gorgeous, writer's intelligent and expert writers we the best among the rest*
*DEDICATED TO MARYAM AMINU JUMARE (Majmiy)*
*page 6-10*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ina zuwa na kwanta kan katifa na danna kiran number hubby na,
Abun haushi kuwa nakirashi kusan sau goma bai
aga wayar ba,
Anan na kifa kaina kan katifa ina tunanin yanda zamuyi rayuwar aure da hubby na duk da cewa duk abun nan da nakeyi hubby na baisan inayi ba,
Haka na wuni ranar banci abinci ba saboda gaba
aya tunanin hubby na ya hanani sakat, sallah kawai take tashina akan katifa na,
Haka kuwa da daddare da 'kyar nasamu naci abinci saboda gaba
aya hankali na ya tashi saboda idan nakira hubby na baya
auka, Amma duk da haka banga laifinshi ba saboda bai San number ba mayb baya
aukar baquwa number ,
Nan take na yanke shawarar bara in tura mashi massage inyi mashi bayanin kaina mayb ya taimaka rayuwa ta ,
Haka kuwa akayi na
auko waya ta na rubuta mashi text kamar haka,
*Assalamu alaikum!*
*hubby na ina fatar kana lafiya nasan bakasan koni wacece ba amma dan Allah katsaya ka saurare ni, ni dai sunana Fatima nice wa
ce kuna tsaye da wani nazo ta gaban ka na tsaya, gaskiya bazan 6oye maka ba ina sonka kuma da aure nake sonka ina fatar kaima zaka soni*
Ina gama rubutawa na tura mashi,
Bayan na tura mashi sainaji gabana yana fa
uwa dalili kuwa ban sani ba kobazai anshi tayin soyayya ta ba,
Bayan natura mashi text
in da kamar minti talatin saina 'kara kira Amma abun takaici bai
auka ba,
Haka na ha'kura badan raina yaso ba nayi kwanciya ta, a daren ranar barci rabi da rabi nayi duk akan soyayyar da nake yima hubby na Dr ,
Washe gari mamanmu ta aika amina wai tana kirana, haka natashi naje wajen mamanmu jikina babu 'kwari ina zuwa na du'ka har 'kasa kamar yanda nasaba na gaishe ta,
Kallo na takeyi musamman dataga duk na rame cikin kwana
aya ga rashin cin abinci da banayi duk a cikin kwana
aya,
Allah sarki mamanmu cikin kulawa tace" Fatima wai meyake damunki tsakanin jiya da yau naga duk kin canja kina cikin damuwa?

"
Naso na 6oye hawayen da suke ma'kale a Idanuwa na Amma nakasa, hawaye sharrr suka rin'ka fitowa cikin manyan Idanuwa na,
Mamanmu hankalin ta ya tashi saboda batason taganmu cikin damuwa shiyasa take yawan Kula da duk wani motsi namu zata iya sadaukar da nata farin cikin dan taganmu cikin farin ciki,
Kai tsaye nace mata" mama ciki na yake ciyo tun jiya ",
Mamanmu cikin nuna damuwa tace" haba Fatima kinsan bakida lafiya shine baki sanar dani ba ai inda kin fa
amun da tun jiya nakaiki hospital amma ko yanzu kitashi ki
auko mayafinki inkaiki hospital ",
Allah sarki mamanmu sai naji tabani tausayi saboda nasan batasan asalin abunda yake damuna ba batasan son masa wani ne yake damuna ba amma saboda banason inyi mata gardama saina tashi naje
aki na na
auko hijabina nasa muka fita da mamanmu zuwa asibiti saboda ciyon ciki na,
Wannan shine karo na farko na zuwa asibiti na da sunan naje ganin likita,
Dayake mamanmu tasan kan asibiti bamu wani sha wahala ba nan take ta bu
e mun kati mukabi layin ganin likita,
Ina nan zaune layi yanata tafiya mutane suna raguwa ita kuma mamanmu tana daga gefe tana kallo na saboda ance ni ka
ai zan shiga
akin Dr tunda ina iyayin magana,
Muna nan zaune da haka har layi yazo kaina,
Tashi nayi nashiga
akin Dr gabana yana fa
uwa saboda bansan mezance ma Dr ba idan nashiga tunda nidai nasan ciyon 'karya ne sai nake ganin kamar Dr zai gane cewa 'karya nakeyi,
Raina a 6ace nashiga
akin Dr ina shiga
akin Me zan gani,
Hubby na ne zaune kan kujera wai Ashe shiyake duba marassa lafiya,
Gabana ne ya fa
i musamman danaga ya murtu'ke fuska babu alamar fara'a tare dashi,
A hankali naje na zauna kan kujerar da Marar lafiya yake zama Dan yayima Dr bayani,
Shi kuma kallo na yakeyi fuskar nan tashi kamar anyi mashi bushara da mutuwa,
A hankali naje na zauna na du'kar da kaina 'kasa bansan lokacin da hawaye suka fara wanka mun fuska ba,
Dr kam kallo na yaci gaba dayi daga nan ko tausayi nabashi komene oho sai yace" meyake damunki?
Chapter 2 · 0% Book details