← Book details Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 42

Sashe 13

Laifina Nane Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Https://mobile.Facebook.com/intelligent-writer's-Association-35077435465066/insight's/
*MRS ABUBAKAR A GASKIYA BAZAN 'BOYE MAKI BA*
*WALLAHI ni Mrs sadeeq na gode sosai da karramawar ki a gareni tabbas ke kin cika mar'atussaliha ce ina roqonAllah ya biya maki buqatunki na alkhairi Allah ya baki 'Yan uku masu albarka na gode sosai naji da
in karramani da kikayi
ina roqon Allah yabar zumunci*
*page 51-55*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Muna gama wayar na kashe ina tunanin idan mukaje funtua jibi aka cire cikin shikenan zan rabu da Dr sageer zan manta dashi zanyi rayuwa ta ni ka
ai danni yanzu tsoron maza nakeyi,
Harga Allah A yanzu banason tarayya ta da Dr sageer saboda na lura ba sona yakeyi ba jiki na ne kawai yake so,
Abunda yake damuna A yanzu shine cikin dayake jikina, nidai A gaskiya banason kowa yasan inda cikin banason mama tasan cewa ni ba budurwa bace banason mama tasan cewa ina
auke da cikin shege,
Wallahi danasan yanda ake zubar da ciki da bazan 'kara Kula mugun nan ba , amma na
aukar ma raina cewa koda munje funtua bazan ta6a yarda dashi A karo na biyu ba, duk da cewa ya rantse babu abunda zai shiga tsakanina dashi amma har yanzu ina jin tsoro,
Babu yanda zanyi dole zan bishi indai har inason in rabu da cikin shegen jikina saboda zaman da zanyi dashi akwai matsala sosai,
Haka na wuni a
aki ni ka
ai in sa'ka wannna in kwance wannan kuka kuwa nayishi kamar raina zai fita, Ina nan kwance sai jin nayi alamar massage ya shigo a waya na,
Dubawa nayi sai naga Dr sageer ne ya rubutamun cewa, wai kar in tayar da hankali na in saki jikina indai har banason mama tagane daga jibi zan rabu da cikin jikina,
Hakan da naga ya rubuta mun sai naji hankali na ya kwanta,
Fita nayi cikin
akina naje
akin mamanmu Naga tana barci aiko naje inda kayan ta suke wa
anda na wanke mata naje na
auko Ayon nafara goge mata kayan ta,
Lokacin da zata tashi kuwa harna da
e da goge mata kayan na kama wani aiki,
Aiko datashi saita hauni da fa
a cewa meyasa banida lafiya nake wahalar da kaina inda ace lafiya nake Amma banida lafiya yakamata in huta,
Bance mata komai ba dan nasan inda tasan abunda yake damuna da saitafi kowa tsana ta cikin 'karfin hali nace mata" Mama Ai naji sau'ki sosai tunda naci abinci nasha magani sai najini garau",
Dariya tayi cikin tausayina tace" Ai kece bakijin magana kullum sai nayi maki fa
an kici Abinci Amma saiki'ki ci kamar wata 'yar yaye"
A cikin firan ne nake ce ma mamanmu dan Allah idan tanada ku
i tabani dubu
aya da
ari biyar inason in siya anko babbar 'kawata
zatayi aure ,
Duk da cewa Amma batada ku
i hakan bai hanata cewa bazata bani ba amma dai tace in bari gobe idan anyi mata cinikin zo6o zata bani dayake tana saida zo6o, harda cewa tayi kema Allah ya nuna mun naki auren Fatima ,
Du'kar da kaina nayi 'kasa jin tace itama Allah ya nuna mata nawa auren sai naji zuciya ta, ta karaya nan take jiki na yayi sanyi saboda nasan ni yanzu duk namijin daya aure ni bazai kalli iyaye na da mutunci ba haka kuma bazai kalleni da mutunci ba,
Da haka mukayita shan firanmu da mamanmu a cikin firan ne take tambaya ta wacece wannan 'kawar tawa wadda zatayi aure har nakeson inyi anko ni kuma cewa nayi
" 'yar islamiyyar muce to abunda yasa baki Santa ba saboda ba'a nan garin ta zauna ba A sokoto ta zauna Amma anan za'ayi bakinta dan har tazo tun shekaranjiya kuma sunce daga jibi an rufe ansar ku
in ankon wai sai mutum yaje kano",
Jin haka mama tace"Allah ya kaimu jibin zan baki kinga idan kika siya saiki
an la6a aisha itama ayi mata ko doguwar riga ",
To kawai nace mata sannan natashi nakoma
akina ina shiga na fashe da kuka saboda irin 'karyar danayima mama sannan kuma zan rabata da ku
in ta cikin kakkausar murya nace ya ka kawo mun
auki ,
Kamar yanda mukayi al'kawali da Dr sageer cewa zamuje funtua jibi toga ranar tazo, Dan haka nashirya cikin riga da zani NASA hijabina har 'kasa naje wajen mama,
Bansha wahala wajen yima mama wayon fita ba saboda nariga nayi mata 'karya tun shekaranjiya dan haka ta
auko dubu
aya da
ari biyar tabani tace tana gaishe da amarya,
Wannan karon a *lalan* munka ha
u da Dr sageer Dan koda nazo lalan shi harya da
e da zuwa,
Ina zuwa nashiga motar shi yayi saurin yi mata key wai bayason aga shiga ta motar shi,
Lokacin da muke cikin mota kuwa Dr sageer ya dameni da masifa wai meyasa nasaka wannan qaton hijabi haka,
Nikam ce mashi nayi babu ruwanshi da sutura ta,
Tafiyar awa
aya mukayi daga gusau zuwa funtua saboda mugun gudun da Dr sageer yayi damu a cikin mota ni har saida naji tsoro,
Muna isa sai naga Dr sageer yayi saurin yin gaba yana cewa injira shi anan yaje ya siya
aki,
Ina nan tsaye harya dawo yace inzo muje aiko banyi mashi musu ba nabishi har
akin daya kama mana,
Muna shiga
akin sai nayi saurin cewa " kayi sauri kacire mun cikin inason in koma gida ",
Kallo na yayi yace ba yanzu zai cire ba saiya huta, nikam naji haushi sosai saboda banason ya 6ata mun lokaci , Dana matsa mashi akan cire cikin sai naga ya kwanta a gado yace
" zo kiyimun tausa duk na gaj
Ba qaramin haushi naji ba aiko cikin tsiwa nace mashi " bazanyi ba Allah ya sauwaqe ",
Tasowa Naga yayi daga kan gadon yazo inda nake ya ri'ke mun kunne yace" teema na WALLHI ki kiyaye ni ba'ayi mun tsiwa kuma ba'a sani abound banyi niyya ba ",
Shiru nayi da baki na sai naji ya daka mun tsawa yace " zakizo kiyimun tausa ko kuwa bazakizo ba",
Murya na tana rawa alamun kuka nace" wallahi bazanyi ba ",
Murmushi naga yayi sai naji yace Fatima yau zanyi maganin wannan taurin kan naki,"
Ban ankara ba sai naji ya cire mun hijabi ni kuma cikin fushi nace " kabani hijabina gida zan koma bazan tsaya ka cuce ni ba Ashe daman dan ka cuceni yasa kace muzo Allah ya isa tsakani na dakai ",
Ban ankara ba sai naji ya bugemun baki wai saboda nayi mashi Allah ya isa sannan yace" cire ciki kikeso ko ?

To banga damar cirewa ba, ke Naga ina lalla6aki Amma baki gani ko ?
Chapter 13 · 0% Book details