← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 76

Sashe 75

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Marduska ya cigaba da cewa, " Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amar dake bibiyar jinin zuri'ar sarki Aminullahi "

Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, " Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? "

Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, " Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta "

Abin duniya gaba É—aya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faÉ—in, " Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaÉ—ai na dogara "

Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, " Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya..."

Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, " Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita..." katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, " Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki " sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, " Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka "

Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, " Akwai wasu ɓoyayun al'amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan " Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.

" Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri "

Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, " Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. "

Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, " Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba "

Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, " Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne "

Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, " Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira " Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, " Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. "

" Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani " Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.

Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, " Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu " yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.

Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, " Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba " rissunawa Jakadiya tayi ta ce, " Ina ankare ya shugaba ta "

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

👹JARIRINA👹

LABARI DA RUBUTAWA
AMEERA ADAM

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

GARGAÆŠI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

1&2

Fuskar Halifa ɗauke da damuwa yace, "Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaɗan banasan tayi nesa dani, na shaƙu da matata banasan ko nan da cen taje" Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar ƴaƴan zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karɓe zancen da, "Kaji mun yaro da sabuwar salawaitun fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki" Inno ta ce, "A'a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haɗa kafaɗa da mu, tunda ya kusa ajje ɗa kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama ɗaya da shi, fitsararre mai idanun marasa ɗa'a dubi yadda yake fiƙi-fiƙi saboda ɗiban albarka" Nusaiba da ke gefe ta zumɓuri baki gaba ta ce, "Ni dai gaskiya Inno ku ƙyaleni anan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun"

Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, "La'ilaha'illallahu Muhammada ɗan Abdullahi, Inno kinji ɗibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaɓi miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?" Halifa ya ce, "Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin ɗumunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wankan gida kuna kwashe mana albarka."

Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, "Tir da wannan halin naka na rashin ɗa'a amma dai Halifa na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin ɗa'a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba'in bazatayi ba ka nuna rashin ɗa'a mujita da wani cikin ko?" Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba ƙaramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, "Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne?'

Inno daƙuwa ta watsa masa ta ce, "Ubanka Salisu shine me matsala" tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zasu hau sama da su.

Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti.
Chapter 75 · 0% Book details