Sashe 31
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mommy da Fahad tuni sun ƙaraso zaune suke a falon Mommy sai hira sukeyi ana dariya, kowa ya gansu yasan suna cikin farin ciki.Indo tun lokacin da taji buɗewar gate da shigowar mota tayi tsumu kamar wacce aka zarewa laka. ta shi tayi ta ɗauki litattafanta da dadduma ta nufi gurin karatunta, amma ga wanda zai ƙarewa yanayin Indo kallo zai fahimci irin tashin hankalin da take ciki, ko da aka zo yi mata lesson ɗin ba abinda take fahimta. Suna gama karatun ta wuce cen garden sai dai abu ɗaya ne ya ɗan faranta mata rai Assignment ɗin da malamin ya bata ta cinye su duka, yadda malamin yake ƙara ƙarfafa mata gwiwa ba ƙaramin birgeta yake ba, lokacin da ta ƙarasa garden zama tayi tana kallan tsuntsayen da suke gurin. Tana nan zaune sama-sama ta fara jiyo magana daga bayanta da alama waya akeyi cikin wayar taji ana cewa, "Ok, amma waɗannan kayan na riga da nayi signing akansu kar abari su fita batare da sani na ba" da sauri ta juya, hango shi tayi tana tafe yana waya abinsa hankali kwance, har ya kusa ƙarasowa gurinta sannan ya kammala wayar, tasowa tayi da murmushi ta ce, "Ya Yaseer kaga na cinye Assignment ɗin jiya kasan dai kamun alƙawarin Chocolate" ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa littafin Lesson ɗinta, watsa mata muguwar harara yayi a zafafe ya fisgi littafin ya keta shi gida biyu sannan ya watsa mata a fuska, dogon tsaki ya ja sannan ya juya ya bar gurin.
Indo kamar gunki haka ta daskare agurin take gabanta ya faɗi ƙirjinta ya hau bugawa, wannan karan neman hawayen tayi ta rasa zuciyarta har ɗaci take saboda ɓacin rai, take zuciyarta ta bata wannan Fahad ne ba Yaseer ba. Tattara takardunta tayi ta wuce cikin gida daga cen bayanta taji anƙwalla mata kira, tana juyawa ta hango shi fuska ɗauke da murmushi takowa yayi ya ƙaraso ya ce, "Da naso naui fushi da ke amma zuciyaya ta azalzaloni naji ba zan iya ba, su Mommy sun zo amma ko kizo ki gaishe su" sai a lokacin Indo ta tabbatar wa da zuciya cewa lallai wancen ne Fahad, murmushin ƙarya ta ƙirƙiro ta ce, "Haba Ya Yaseer ya za'ayi naƙi zuwa na gaishe su bari nayi su huta kasan sun sha hanya suna buƙatar hutu" Hankali da sanin yakamatan Indo na matuƙar birgeshi murmushi yayi ya ce, "Eh haka ne, amma yanzu kizo muje ku naji Momma ma na tambayarki agun Lubna" gaban Indo ne ya yanke ya faɗi ta tattaro nutsuwarta ta ce, "Ok, bari na kai littafina ɗaki" sai a lokacin ya kai idanunsa kan yagaggun littafin Indo da mamaki ya ce, "Humaira ya akayi littafinki yayi haka" rasa abin cewa tayi, dabara ce ta faɗo mata ta ce, "Ina zauna a garden ƙadangare ya faɗo to garin zan gudu bansani ba na gaya littafin" gyaɗa kai yayi ya ce, "Ki dinga lura sosai, ki je ki ajiye ina jiranki" Indo wucewa tayi kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki taje ta ajiye ta dawo suka wuce ɓangaren Momma. Suna shiga kan Indo a ƙasa ta tsugunna ta gaishe da Mommy, Mommy kallanta tayi cikin murmushi ta amsa daga cen gefe Fahad ta hango yana danna waya, har ta miƙe Yaseer ya ce, "Humaira baki gaishe da Brother ɗina ba" Indo na ɗago kai suka haɗa ido da Fahad ya watsa mata harara, cikin daburburcewa ta gaisheshi kamar bazai amsa ba murya cen ciki ya amsa da, "Lafiya" Indo miƙewa zatayi Momma ta dakatar da ita da faɗin, "Ina zaki Humaira bakya ganin ga Lubna nan a zaune ki zauna mu ci abinci mana" Indo komawa tayi ta zauna banda gumi babu abin da takeyi, Lubna dake gefe sai watso mata harara take. Shiru Indo tayi su Mommy sai hira suke cikin hirar ne taji Mommy na gayawa Momma a cikin satin za'a kai kuɗin aure da sa rana na Fahad gidan su budurwarsa Rufaida, sosai Momma taji daɗi cikin farin ciki tace, "Ai ni kuwa Mommy tuwona mai na zanyi saboda Yaseer ya gayawa Daddy shi Humaira yake so idan ta gama karatu" Zaro idanu Lubna tayi cikin tashin hankali, kafin Mommy tayi magana tuni Fahad ya ce, "What? Momma kina nufin wannan abar zai aura?" Canza fuska Momma tayi ta ce, "Fahad bansan ka da wannan ɗabi'ar ba, bawa baya taɓa gujewa ƙaddararsa kasancewarta ƴar gudun hijira bazai hana mu haɗa zuri'a da ita ba" Indo gabanta sai dukan uku-uku yake, gabaɗaya tayi zuru-zuru. Fahad ne ya watsa mata wulaƙantaccen kallo ya ce, "Kiyi haƙuri Momma ba rashin kunya xanyi miki ba, amma gaskiya bana bada goyan bayan Yaseer ya auri wannan ƴar kunamar, kai ni inada shakku akan ingancin lafiyarta sabo..." cikin ƙaraji Yaseer ya ce, "Stop! Bana buƙatar ƙarajin waɗannan miyagun kalaman naka" murmushin takaici Fahad yayi ya ce, "Ok, banyi mamaki ba saboda soyayya ta rufe maka ido" Mommy sai a lokacin ta ce, "Fahad wai ko itace maganar da ka ce idan mun zo zamuyi?" Momma da kanta ya gama kullewa ta ce, "Fahad kasan wani abu akan Humaira ne?" Fahaf gyaɗa kai yayi ya ce, "Indo ake kiranta a garinsu ba Humaira ba..."
ALLURA ZATA TONO GARMA🤒🤒🤒🤒
FATAN ALHERI GAREKU SAI NAJI COMMENTS🥰
WATTAP KUYI HKR SBD RASHIN REPLAY NA COMMENTS ƊINKU😉😉
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[12/08, 18:11] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
DAN GIRMAN ALLAH DUK WACCE TA KARANTA SHAFIN NAN TA BI WANNAN LINK ÆŠIN👇ðŸ»ðŸ‘‡ðŸ» TA DANGWALAWA *MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)* SAI KUYI *SUBMIT* SHIKENAN, DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA MASOYAðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSfU5hK-9VjsISvD_EeweRZj-ivTJBN-qNJFmVU3Y8N0uWe51g/viewform
57&58
Maganar Fahad ce tayi dai-dai da ɗagowar kan Indo, cikin tashin hankali ta kafeshi da dara-daran idanuwanta da suka kaɗa sukayi jawur. Mommy da sauri ta kalli Fahad ta ce, "Indo kuma Fahad? A ina kasan yarinyar nan ba yan ance iyayenta ba ƴan nahiyar nan tamu bane?" murmushin takaici Fahad yayi ya ce, "Ta dai yaudare ku ne da haka amma Indo shine ainihin sunan da ake kiranta" Yaseer ne ya furzar da Iska mai zafi cikin takaici ya ce, "Ka ga dan Allah karka wargaza mana gida, idan ka san babu abinda ka sani game da Humaira ka ja bakinka ka tsuke" Tamke fuska Fahad yayi zaiyi magana Momma ta ɗaga hannu tana faɗin, "Bana buƙatar hayaniya ko cecekuce, Fahad kaji tsoron Allah ka sani idan ka ɓoye mana bazaka ɓoyewa ubangijinka ba. Ka sanar da mu abin da ka sani, amma ina ƙara sanar da kai muddin na bincika naga ƙarya kake ranka zaiyi mummunan ɓaci"
Fahad jinjina kai yayi ya ce, "Momma nayi tsammanin farat ɗaya ke da Mommy zaku gasgata abin da na faɗa, sai gashi na ga shakku a cikin idanuwan ku" Mommy cikin tsuke fuska ta ce, "Fahad ina tsammanin nida Momman ku babu abokin wasan ka, ƙarin bayaninka muke nema ba dogon sharhi ba" Lubna dake gefe zuciyarta fes taji cikin sigar zuga ta ce, "Ni dama wallahi tun ranar da na fara ganinta jikina ya bani bata da gaskiya munafuka mai ƙwala-ƙwalan idan..." a hargitse Yaseer ya watso mata tsawa take ta tsuke bakinta tana watsawa Indo harara. Fahad ne ya ci gaba da cewa, "Yarinyar nan sunanta Indo kuma ƴar garin Kura ce acen take zaune da iyayenta" Mommy da sauri ta ce, "Kura fa kace fahad?" Fahad gyaɗa kai yayi sannan ya ce, "Kema kin santa Mommy sai dai wataƙila baki gane ta bane, zan kira Kawu yanzu a gaban ku ya jadaddar da abinda nake faɗa muku" Fahad na gama faɗa ya ciro wayarsa ya kira lambar Maigari, kiran farko da yayi ba'a ɗauka ba sai a kira na biyu Maigari ya ɗauka bayan sun gaisa Fahad ya ce, "Kawu dama tambayarka zanyi anga yarinyar nan kuwa Indo wacce ka ce mun ta ɓata kwanaki?" Maigari ya ce, "Ina fa Fahad har kwanan gobe bamuji labarinta ba, kai tsohuwar da take riƙonta ma ta koma cikin garin Kano gurin ƴaƴanta, kasan yarinyar nan hatsabibiya ce yanzu haka tana cen ta shiga duniya tana addabar wasu, mudai tun da Allah ya rabamu da alaƙaƙai taje cen ta ƙarata" murmushin gefen baki Fahad yayi ya ce, "To Kawu an same ta" da sauri Maigari ya ce, "Kai yaron nan banasan shaƙiyanci, yau sama da wata nawa da ɓatan wannan sheɗaniyar yarinyar sai yanzu zaka ce mun an ganta" Fahad ya ce, "Kawu kasan bana maka irin wannan wasan, wallahi anganta" tattaunawa suka cigaba da yi daga ƙarshe sukayi sallama.
Mommy kafe Indo tayi da kallo sosai take ganin yanayin kamar tasan kamanninta, Momma ce ta kalli Fahad ta ce, "Dan ka kira waya wannan bazai tabbatar mana da cewar ita ce wacce kuke magana akanta ba" Fahad tamke fuska yayi ya kalli Indo ya ce, "Ke ki buɗe baki kiyi magana kece Indo ko ba ke bace?" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi bata ce komai ba, buga mata tsawa Fahad yayi ya ce, "Ba magana nake miki ba?" Indo fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya.