← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 76

Sashe 23

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da suka ƙarasa gida Jamilu haka ya dinga tausarta yana bata baki, harta fara tsagaitawa da kukan sai da ya lura ta fara dawowa nutsuwarta sannan ya ce, " Baba Huwaila dan Allah ki kwantar da Hankalinki kinsan fa kina da hawan jini yanzu idanzu Kawu suka ji labarin halin da kike ciko bazasu ji daɗi ba, ki kwantar da Hankalinki ni zan je Kano na nemo miki ita " da sauri Baba Huwaila ta dafa ƙafar Jamilu ta ce, " Sai dai mu tafi tare idan angano ta mu dawo tare " cikin dabara ya ce, " Haba Baba Huwaila idan muka tafi tare ai bazan nemota lungu da saƙo ba tunda kinsan dai Kano girma gareta, a gidan Kawu zan sauka duk yanda ake ciki zaki zan kiraki a waya " Baba Huwaila gyaɗa kanta tayi cikin jindaɗi tace, " Jamilu idan kayi mun haka ka gama mun komai Allah yayi maka albarka " Tausayin Baba Huwaila ne ya kamashi cikin zuciyarsa yake mamakin irin ƙaunar da Baba Huwaila take wa Indo, gani yake da Goggo na raye haka ta faru baisan me faru ba,ɗagowa yayi ya ce, " Ameen ya rabbi Baba Huwaila " wani hawayen ne ya ƙara zubo mata gefen mayafinta tasa ta goge ta ce, " Allah ya jiƙan Aminiyata da tana raye bansan wane hali zata shiga ba, Allah ya bayyana mun ke Indo incika Alƙawarin da na ɗauka " Jamilu amsawa yayi sannan ya tashi ya shiga ɗakinsa, saman katifa ya kwanta yana tunanin halin da zai ɓullowa Baba Huwaila dan ya lura idonta rufe gashi ya ce zai je ya nemo Indo, afili ya furta, " Yanzu da nace zani Kano nemanta ta ina zan fara? " shi kaɗai ya zauna yana jerowa kanta tambayoyin da rasa amsoshinsu.

Indo tana zaune tana ƴan kalle-kallenta har Honourable ya sauko sanye da dakakkiyar shadda ruwan toka, tunda ya fara takowa ƙamshin turerensa ya mamaye cikin falon, yana ƙarasowa wani kwarjini ya yiwa Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta, yana ƙarasowa ya ce, " Cutie na Afuwan kina ta jirana ko? " Indo girgiza kai tayi bata masa komai ba, hanyar waje ya nufa ya ce, " Zo mu wuce inajin sai mun biya ta Resturant munci abinci ko? " Indo bata ce masa komai ba yana gaba taba biye dashi a baya, mota ya buɗe mata ta shiga tana shiga shima ya zagaya ya shiga ya figi motar tuni dama Maigadi ya riga da ya buɗe masa gate.

Kai tsaye Tarauni suka wuce Resturant ɗin HINDAT CHIPS&CHEKEN RESTURANT haɗaɗɗen gurin cin abinci ne na ƴan gayu da masu kuɗi, Honourable yana gaba Indo na biye da shi, ɗan siririn mayafinta saƙale yake akan kafaɗarta suna shiga kujera suka ja suka zauna, Indo a fakaice take ƴan kalle-kallenta List aka kawo musu Honourable ya zaɓi abinda za'a kawo musu.

Sanye yake cikin ƙananan kaya waɗanda suka ƙara fito da zallar kyawunsa mai ɗauke da zallar haba da kamalarsa, kamar kullin fuskarsa babu walwa zaune yake yana latsa wayarsa, a hankali wayarsa ta fara ringing tana fitar da amo mai sanyaya zuciya, sai da wayar ta kusa katsewa sannan da ɗauka cikin murya zaratan maza, da sauri Indo ta juya tana kallan mai amsa wayar saboda muryarda ba ƙaramin amsa kuwwa tayi mata cikin dodon kunnenta ba, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa kallonsa take har ya ƙarasa wayar, Hanourable kallanta yayi ya ce, " Cutie na ga abinci ankawo mana " adai-dai lokacin ya ƙarasa waya ɗagowar da zaiyi karaf idanunsu suka haɗu da juna, kauda kansa yayi kamar bai ganta ba, Indo juyawa tayi ta fara cakalar abinci amma rabin hankalinta yana kan kyakykyawan saurayin, lokacin da ya lura da indo ta daina kallansa ɗagowa yayi ya zuba mata sexy eyes ɗinsa yana ƙare mata kallo,kansa ne ya kulle gani yake kamar yasan fuskarta amma a yanda yasan waccen bata kai wayewar wannan ba, to me haɗinta da wannan mutumin da yake kiranta da Cutie, yana ganin zata ɗago ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar bai damu da abinda sukeyi,Kiran wayar Honourable akayi har lokacin Indo tana kallansa saurayin take tantama take wai wanda ta sani ne ko kuma wani me kama da shi suna haɗa ido ya tsuke fuska yana watsa mata harara, Haonourable tashi yayi ya ce, " Humaira bari naje na amsa waya na dawo " Honourable har yayi gaba Indo tace, " Honey nidai kazo mu tafi " rass gaban Fahad ya faɗi, jiki a sanyaye ya ɗago kai yana kallon Indo saboda yanda yaji muryarta farin sani, Honourable juyowa yayi ya ce, " Cutie karki damu yanzu zamu tafi " gyaɗa kai Indo tayi tana sunkuyar da kai ƙasa,Fahad tashi yayi zai fita wayarsa ce ta faɗi ya tsugunna ya tattarata, har ya wuce cikin sanyin murya Indo tace, " Fahaaaad " har yayi gaba ya tsaya cak ɗan juyowa yayi kallon tsana ya bita da shi yana ƙarewa shigar jikinta kallo, wucewa yayi yana jin zuciyarsa na masa wani irin zafi, yana fita motarsa ya shiga wayarsa ya ɗauko ya nemo lambar Maigari, saving ɗinta yayi da Kawun kura kira yayi tana shiga ya ɗauka.

WHATSAPP FANS COMMENTS YAYI ƘARANCI☹️☹️

WATTPAD KU CIGABA DA GASHI🌚🌚

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

[17/07, 17:59] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

45&46

Da sallama Maigari ya ɗauka fuska a sake, Fahad gaida Maigari bayan sun gaisa cikin dabara ya ce, " Kawu dama wata makaranta akesan buɗewa ta kangararrun yara marasa ji, to hukuma ta bada umarnin a ɗauki list ɗin adadin yaran, amma yara mata kawai suke ɗauka shine nace a nan Kura ko kuna da yarinyar da ta fitineku ko yara mata? " Maigari kamar jira yake ya ce, " Allah ya yanke mana wannan masifar Fahad dama yarinya ɗaya ce ta addabemu kuma mun wayi gari ta ɓata, wata yarinya na nan doguwa da ka taɓa marinta bayan zuwanku " Fahad wata hargitsatstsiyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, " Shikenan Kawu nagode..." da sauri Maigari ya katseshi, " Amma Fahad babu wani alheri da zamu iya samu bayan wannan? Nufina ko ɗan wani hasafi haka " Fahad fuska ba walwala ya ce, " Gaskiya babu Kawu agaida mutanen gidan " bai jira cewar Maigari ba ya kashe wayar gaba ɗaga, yana gama wayar Honourable ya hango zai giftashi wata wayar ce ta ƙara shigo masa ɗauka yayi ya fara magana, bayan sun gaisa da wanda ya kira wayar suka shiga hira cikin hirar tasu yake faɗin, " Kai Abokina ina zaka gani Allah ya ne yayi mun gyaɗar doguwa na haɗu da wata baƙauyiyar yarinya, ai ko zaka ganni sai na gama sha'anina yanzu haka yau Abuja zamu wuce da ita " amsa aka bashi daga cen ɓangaren sannan suka cigaba da magana ba jimawa sukayi sallama,duk wayar da Honourable yake yi akan kunnen Fahad yayi ta zuciyarsa na wani irin zafi ya kunna motarsa ya bata wuta da gudun gaske ya bar gurin,Honourable gyara babbar rigarsa yayi ya shiga ciki a lokacin tuni Indo ta gaji da zama, bata wani ci abincin kirki ba shima ko rabin plate bai ci ba ya sallami masu resturant ɗin sannan suka wuce, Indo sai wurga Idanu take ko Allah zai sa ta ga Fahad amma ko mai yanayinsa bata gani ba, kai tsaye Mustafa ya kira a waya yace su haɗu a Airport yaje ya karɓi motarsa shi kuma zai wuce Abuja.

KURA

Shirye yake tsaf cikin shigarsa ta Shadda coffee agogon hannunsa yake ɗaurawa,Baba Huwaila na daga tsaye tana ta yi masa fatan samun nasara da dacen ganin Indo,Jamilu sallama ya yiwa Baba Huwaila ta rakoshi har ƙofar gida tana yi masa Addu'a, tana ganin yayi nisa ta share hawayen idanunta ta juya cikin gida, Jamilu motar Kano ya tara tafiya suke amma gabaɗaya acikin tunani yake da nazarin ta inda zai ɓullowa lamarin ɓatan Indo.

ABUJA
Chapter 23 · 0% Book details