← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 76

Sashe 53

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutanen da suka ɗauki Indo wata hoda suka shaƙa mata, nan take jikinta ya saki ta faɗi ƙasa ba numfashi. Tafiya suka yi me ɗan nisa kamar zasu bar garin, sannan suka shiga cikin wani ƙasurgumin daji, basu wani shiga cen ciki ba sukayi parking ɗin motarsu. Zuwan su babu jimawa Indo ta fara farkowa, Ɗaukkota sukayi kamar wata ƙaramar yarinya, a ƙasa suka wurgar da ita zafin buguwar da taji yasa ta ƙarasa wartsakewa. A zabure ta miƙe zaune tana ja da baya nan take ta tuna abinda ya faru da ita, idanunta ne suka ciko da ƙwallah, haɗa hannuwanta biyu tayi cikin roƙo ta ce, "Ku dubi girman Allah kuyi haƙuri karku cutar dani" Hadari dake cen gefe da yake ƙarewa Indo kallo, ji yayi ta matuƙar birgeshi har zuciyarsa, takowa yayi har gabanta ya tsugunna a gabanta yana ƙarewa laɓɓanta kallo, tana ƙarasa magana yasa ɗan yatsansa a laɓɓanta, sannan ya ce, "Yarinya kwangila aka bamu mu kashe ki, daba dan haka ba dana ƙyaleki amma ba wannan alƙwari, na yaba da kyawunki ƙwarai." Indo girgiza kai ta farayi ta ce, "Duk wanda ya baku wannan kwangilar bansan me na tsare masa ba, tun ina jaririya yake farauta rayuwata ashe har yanzu baza'a barni na huta ba?" Sunkuyar da kai tayi ta ce, "Ku kashe ni kawai, saboda nasan ko baku kasheni yanzu ba dole zasu kasheni. Amma dan Allah inasan idan kun kasheni, ko da da daddare ne ku kai gawa ta ƙofar gidan Mahaifina ayi mun sutura, karku barni dokar daji dan Allah" Indo ta ƙarasa faɗa cikin karaya.

Hadari jikinsa ne yayi sanyi ba yau ya saba irin wannan aikin ba, amma lokaci ɗaya yaji tausayin yarinyar ya kamashi, ganin yanayinsa yasa ɗaya daga cikin yaransa ya ce, "Haba Megida karfa ka ɓata mana harka... " tun kafin ya ƙarasa magana Hadari ya sakar masa harbi a ciki take ya faɗi ko shurawa baiyi ba. Indo zaro ido tayi tana rushewa da kuka, Hadari hannu yasa ya tayar da Indo tsaye yace, "Bazamu kasheta ba zamu tafi da ita ƙasar nijar tunda a cen zamu yada zango, ni zan aureta..." be kai ga rufe baki ba suka ji motar ƴan sanda, suna shirin shiga mota su gudu suka fara sakar musu harbi, mutum biyu ne suka gudu aka kama mutum uku, amma a cikin wanɗanda aka kama harda Hadari.

Indo banda kuka babu abin da take yi, kamata sukayi suka saka a mota, suma su Hadari aka tasa ƙeyarsu zuwa Headquarter ƴan sanda. Alhaji Khalili bai sanar da Mahaifiyar Indo ba saboda yasan nan da nan hankalinta zai tashi, idan ba'ayi sa'a bama hawan jininta yana iya tashi. Sai dai ganin su Indo basu dawo ba yasa ta kira wayar Musty amma a kashe, wayar mijinta ta kira ta sanar dashi, a lokacin nuna mata yayi kamar bai san me yake faruwa ba, ya ce mata zai kira Director makarantasu. Bayan ƴan mintuna ya ƙara kiranta ya ce mata akwai abinda aka zaunar da ɗalibai ake musu, jikinta a sanyaye ta amsa amma wani tsagi daga cikin zuciyarta ya kasa amincewa da maganar mijinta, sai dai batasan ta ƙaryata shi yasa bata musa masa ba. Amma tasan idan har akwai wani muhimman abu da za'a tsaida ɗalibai tun kafin ranar Director yake buga takarda, kowanne ɗalibi ya kaiwa iyayensa. Fahad ne yazo ya same ta cikin jimami bayan ya tambayeta take sanar da shi abinda yake faruwa. Mukullin motarsa ya ɗauka ya nufi makarantar su Indo, domin ya ji ba'asin da za'a zaunar da yara har doshin magriba batare da sanin iyayensu ba. Sai dai yana zuwa ya samu makatarantar a rufe ko megadinta baya nan, da sauri ya kira lambar Kawunsa a nan yake sanar da shi abinda yake faruwa, tare da jan kunnensa akan karya sanarwa da Mahaifiyarta abinda ya faru.

Kai tsaye Fahad cen Headquarter ƴan sandan shima ya wuce hankali a tashe, Su Indo kuwa sai wajen ƙarfe takwas na dare suka ƙarasa Headquarter, lokacin da mahaifinta ya ganta ba ƙaramin farinciki yayi ba, ita kanta Indo rungume shi tayi ta rushe da kuka, cikin kuka ta ce, "Daddy wai me nayi musu da basa so na? Meyasa basa san suga ina rayuwa da Iyayena? Daddy me na aikata masu ne?" kukanta ne ya tsananta fuskarta tayi jawur, tausayinta ne ya kama Fahad saboda ya rasa me ta tsare musu da tun tana cikin tsuma take fuskantar barazana daga garesu, sai dai babban farin cikin da yayi da Allah yasa aka kamasu, yasan ko ba komai zasu faɗi wanda ya sasu wannan mugun aikin. Mahaifinta ƙara riƙeta yayi idanunsa na cikowa da ƙwalla, yasan shi dai duk tsawon rayuwarsa bai taɓa aikatawa wani mugun abun da zai yi masa sakayya da irin wannan abun ba.Godiya ya yi wa Allah, da Allah yasa aka kama waɗannan masu mugun aikin kuma a yanzu ne zai san waye wannan babban maƙiyin nashi.

Kallan Indo ya yi ya ce, "Ina Musty fa?" Indo ta ce, "Tun kafin su tafi dani suka harbe shi" A razane ya ce, "Yana ina yanzu?" Bata bashi amsa ba yaji ankirashi a waya, yana ɗauka aka sanar dashi asibitin da Musty yake da halin da yake ciki. A hanzarce yasa Fahad ya wuce da Indo gida, sai dai razanar da tayi yasa taƙi sakin Mahaifinta dan yanzu ma gani take idan sun tafi wani abu zai iya faruwa dasu. Ya lura da halin da Indo take ciki, cikin lallashi ya ce, "Humaira ba abinda zai faru kinji, kinga ankama su kuma in sha Allah ƙarshen matsalar tazo." Bakin ta na rawa ta ce, "Daddy a gabana suka harbi Musty, kuma a gabana suka kashe ɗan uwansu, nima fa sunce kasheni zasu yi" Fahad ne ya riƙo hannunta cikin tausayi ya ce, "Bazasu kashe ki ba kinji, zo mu wuce gida." Indo kamar wata ƙaramar yarinya, haka ta bishi suka shiga mota sai juye-juye take har suka ƙarasa gida.

Lokacin da Daddy yaje asibiti Musty bacci yake saboda Alluran da akeyi masa, ansamu nasarar ciro harsashin kuma har angyara ƙafar annaɗe da bandeji. Duk abinda ya kamata Alhaji Khalil ya biya sannan ya kira Ƙanin Mahaifin Musty ya sanar dashi, kasancewar Musty maraya ne. kafin wani lokaci ƴan uwan Musty sun cika asibitin.

Bayan kwana biyu jikin Musty yana ƙara samun sauƙi sosai, Da farko Mahaifiyar Indo cewa tayi sai dai Indo ta haƙura da zuwa makarantar, bayan da Daddyn Indo ya gaya mata abinda ya faru. Sai dai Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta ɗan samu nutsuwa, duk ranar da Indo take da Jarrabawa Fahad ne yake kaita, ya jira ta gama ya dawo da ita gida.

Su Hadari fir suka ƙi faɗar wanda ya saka su Kashe Indo sai da suka ji wahala tukunna suka faɗa, a lokacin Alhaji Khalil na gida Kwamishina ya kirashi zuwa cen Headquarter. Bayan yaje ya saurari abinda su Hadari suka faɗa a razane ya ce, "Hajiya Safiya fa? Hajiya Safiya dai matar ɗan uwana?" ana cikin haka Ɗan uwansa Yaya Haruna tare Ɗansa Muhsin suka zo, Ɗan uwan nasa na zuwa ya ce, "Khalil kace mun sun faɗi wanda ya tura su waye dan Allah? Wanne azzalumin ne?" Alhaji Khalil kunyar Yayansa yake yace matarsa ce, Kwamishina ne ya karɓi zancen da, Sunce Hajiya Safiya ce ta sasu kuma har Video lokacin da take basu kwangilar suka nuna mana, tare da kwanan watan ranar da taje ta same su a mazauninsu, Kwamishina ya ƙarasa faɗa yana nuna masa bidiyon wayar Hadari. A razabe Mahaifin Lubna ya ce, "Safiya tawa kai ƙarya ne, a rasa wa za'ayiwa sharri sai Iyalina? Gaskiya da sake bazai yuwu ba."

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

83&84

Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon.

Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu.
Chapter 53 · 0% Book details