Sashe 28
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lokacin da Jamilu ya gama zayyanewa Baba Huwaila yadda suka yi a kano kuka ta fashe masa da shi, sai da tayi mai isarta ya lallasheta sannan ya sanar mata da sauyin aikin da ya samu. Tayi murna ƙwarai daga baya kuma tayi tsalle ta dire, tace atabau sai dai su ɗunguma su koma kano.
Jamilu mamaki yayi sosai, shi dai a saninsa Su Kawunsa sun jima suna yaƙi akan Baba Huwaila ta koma gurinsu da zama amma ta shafawa idonta toka taƙi yarda, a yanzu rana tsaka ta ce su koma Kano, da farko kamar ya yi mata maganar amma da ya tuna a wannan lokacin ta zama hukuma sai rarrashi sai kawai ya share maganar. Wayarsa ya ɗauka ya kira Kawu ya sanar da shi yadda sukayi da Baba Huwaila, farin ciki sukayi sosai sannan suka ce su haɗa kayansu zasu taho da mota su ɗauko su gabaɗaya.
BAYAN SATI BIYU
Indo ta murmure ta murje ta zama ƴar gida, har wata ƴar ƙiba tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa, tun tana baƙunta tana jin nauyin su har ta saki jikinta da su. Daddy ne ya ɗauko mata mai koya mata karatun islamiyya da boko, Momma ce ta kawo wannan shawarar acewarta idan aka saka Indo a ba tare da lesson ba zai yi wuya ta dinga fahimtar karatu cikin sauƙi.Wani ustaz aka ɗauko yake zuwa yana koya mata karatun addini da safe sai wani Teacher da yake zuwa bayan sallar la'asar yana koya mata karatun boko.
Indo ta fahimci Yaseer sun sha matuƙar bambam da Fahad, mutum ne mai barkanci da fara'a uwa uba sauƙin kai. haka zai biye mata kamar ƙaramin yaro suyi ta hira Indo na bashi tatsuniya, wani lokacin idan yaga Indo tayi zuƙuɗum tana tunani dan ya kawar mata da damuwa har ɗaukanta yake su tafi stores suyo siyayyar tarkacen kayan zaƙi dangin su alewa chocolate da sauransu.
A wannan lokacin abu É—aya zuwa biyu ne yake damun Indo, wani lokacin haka zata zagaya cen Garden ta sha kukanta san ranta, wani lokacin kuma cikin dare idan Baba Mariya na bacci, abu na farko idan ta tuna rashin asalinta shi yake É—aga mata hankali domin takan zauna ta dinga gayawa kanta wannan kalmar ta, "KAYAN ARO BAYA RUFE KATARA" duk jindaÉ—in da zaka samu indai za'a ce baka da asali na banza ne domin ko ba daÉ—e ko ba jima ALLURA ZATA TONO GARMA.
Abu na biyu su Baba Huwaila ita da Jamilu, kodayaushe tana tunanin halin da Baba Huwaila take ciki wani lokacin idan kewarsu ta dameta sai dai ta fashe da kuka, wata rana tana garden a durƙushe tana kuka Yaseer ya tsaya yana sauraron yadda take rera kuka, sai da tayi mai isarta sannan ya zauna a gefe yana tambayarta abinda yake damunta.
Sai da ta share hawayenta sannan ta ce, "Ba abinda yake damuna kawai Iyayena na tuno" tausayinta ne ya kama shi har cikin ransa ya shiga lallashinta daga nan ya fara aikin nasa na barkwanci, lokaci É—aya ya mantar da Indo damuwar da take ciki. Tun daga ranar yake samar musu lokaci yana suna zama shi da ita yana bata labari ita kuma ta yi masa tatsuniya.
Ya ma Indo ta fito daga ɗakinsu lokacin yamma tayi, cen garden ta nufa saboda ta duba filin motsa jikinsa bayana nan, ta san indai bayacen a wannan lokacin yana garden a zaune. Kamar yadda tayi tsammni hango shi tayi ta bayansa a kan kujera da alama waya yake dannawa kuma yayi zurfi cikin abinda yake yi, Indo tsinken tsintsiya ta zaro ta tafi a hankali tana zuwa, ta fara zana masa a cikin kunnensa. Da sauri ya zabura a tsorace har yana jefar da wayar hannunsa ta faɗi cen gefe, Indo ƙyalƙyalewa tayi da wata iriyar dariya irin ta tsokana tanayi tana tafi da hannunta, batayi aune ba taji ya kifeta da wani irin azababben mari har sai da ta kusa faɗuwa, da sauri ta dawo cikin nutsuwarta tana dafa jikin bango. Da mamaki ta ɗago ta kalleshi hannunta riƙe da kumatunta, tana shirin yin magana ya nuna ta da ɗan yatsa fuska a tsuke ya ce, "Ki shiga nutsuwarki banasan hauka da rashin hankali irin naki idan ba haka ba zan banbance miki aya da tsakuwa wawiya, ko cikin karnuka ke shashar karya ce" yana gama faɗa ya tsugunna ya ɗauki wayarsa ya fice daga gurin ya bar Indo riƙe da kumatu.
TO FA FANS KU KAFTA🤸ðŸ»â€â™€ï¸
*KUMUN AFUWA NA JINA KWANA BIYU DA KUKA YI INSHA ALLAH NA DAWO DA ZAFINA AMMA GOBE BAZAKU SAMU POSTING BA, KU TAYANI DA ADDU'A INA DA EXAMS GOBE IDAN ALLAH YA KAIMU.*
KUMA INA JIRAN NAJI RUWAN COMMENT🤓
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[10/08, 17:26] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
53&54
Indo tsaye tayi kamar wacce aka zarewa laka a jiki, jiki a sanyaye ta juyo tana bin hanyar da ya nufa da kallo, gangarowar hawayenta zuwa kan tafin hannunta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, sautin muryarsa ce ta cigaba da yi mata amsa amo cikin dodon kunnenta, maganarsa ta ƙarsh ita tafi tsaya mata a rai, "Ko cikin karnuka ke shashar karya ce" da gudu ta fice daga gurin kai tsaye ɗakinsu ta wuce, tana shiga ta faɗa kan gado ta rushe da wani irin matsanancin kuka.
Sai da tayi mai isarta ta goge hawayenta a fili ta fara magana kamar zautacciya, "Ya Yaseer meyasa zaka yi mun haka? Kasan ba haka halinka yake ba zaka yaudare ni da barkwancinka?" kamar an tsikareta ta miƙe tsaye a zabure take wani tunani a faɗo mata haɗe da tsoro a fili ta ce, "Ina tunaninki ya tafi da zaki sakankance masa ko kin manta halinsa lokacin da yaje garinku?" sai kuma ta zauna gefen katifar tana cewa, "Kenan Fahad yaudarata yayi? Me nayi da zai kirani karya?" take ta tuno haɗuwarta da shi a kano a gurin cin abinci. Cikinta ne ya karta tsoro ya kamata afili ta ce, "Nashiga uku yanzu idan ya gayawa Momma ya zata ɗauki abun" sai kuma ta ce, "Amma ai na gaya mata yanda muka haɗu da Alhaji" ɗayar zuciyar ta ce, "Idan ya sanar da su asalinki fa" a nan indo tayi shiru kanta ya kulle ta rasa bakin magana, amma gaba ɗaya tsoro ya addabi zuciyarta a kowanne lokaci tsammanin kiran Momma take, a gefe ɗaya kuma taci alwashin fita daga sabgar Yaseer indai ba gaisuwa ce zata haɗa su ba.
Yana fita daga gurin ɗakinsa ya wuce yana huci da ƙarfi ya banka ƙofar, yana shiga ya dunƙule hannunsa ya kaiwa bango duka yana furzar da iska mai zafi. Wani tunani yayi da sauri ya fice daga ɗakin ya wuce ɗakin Momma, yana shiga ya fara ƙwala mata kira. Da sauri ta fita a hargitse saboda jin kiran da yake mata tasan ba na lafiya bane, tana fitowa ta ce, "Son lafiya wannan kiran haka" fuskarsa murtuk babu walwala ya ce, "Momma magana akan waccen yarinyar ne" Momma zama tayi akan kujera ta nuna masa gefe ta ce, "Zauna nan, me Humairan tayi maka?" zama yayi yana sauke ajiyar zuciya yace...
Da daddare su Indo na zaune a ɗakinsu Momma ta shiga, cikin girmamawa Indo ta rissina ta gaishe da Momma, Zama tayi a bakin gadonsu ta ce, "Humaira yayanki ya kawo mun ƙararki wai kinyi masa rashin kunya, banasan raini kuma banasan ya ƙara kawo mun ƙararki nan gaba" Tun da Momma ta fara magana jikin Indo yayi sanyi cikin zuciyarta take faɗin, "Meyasa Yaseer zaiyi mun haka? Dama lumbu-lumbu yayi mun? Aikuwa anyi ɗaya babu ƙari indai nice" a fili Indo ta ce, "Insha Allah Momma haka bazata ƙara faruwa ba zan kiyaye" murmushi Momma tayi ta ce, "Yauwa Humairan Momma" ta faɗa tana ɗora hannunta akan kafaɗar Indo sannan ta tashi ta fice daga ɗakin, Indo ta jima tana jin ranta babu daɗi daga ƙarshe ta yanke shawarar yanke alaƙarta da Yaseer.
Washegari da yamma bayan angama yiwa Indo lesson tana zaune agurin tana duba abinda aka koya mata, daga bayanta taji kamar an jefo mata ƙaramin dutse a tsorace ta juya, ganin babu kowa yasa ta ci gaba da harkar gabanta. A karo na biyu taji ankuma jefo mata dutsen miƙewa tayi ta fara haɗa takardunta, ta nufi hanyar falon batayi aune ba ta taji ya ce, "Kamota nan" Indo ihu ta saki tana watsar da takardun hannunta, saboda tsoro jikinta sai karkarwa yake. Dariya Yaseer yayi yana nuna ta da ɗan yatsa ya ce, "Matsoraciya! matsoraciya! Nima na rama abin da kika mun rannan" Indo tsuke fuska tayi ta ce, "Ya Yaseer dan Allah ka bari bana so" tana gama faɗa ta kwashe takardun ta shige falon. Da mamakin abin da tayi masa ya bita da kallo amma sai yayi wani tunani yake ganin kamar ko tana cikin yanayin da bata buƙatar haka, amma ko kaɗan ransa bai so haka ba. Ya jima a tsaye sannan ya wuce ɓangarensa fuska ba walwala.