Sashe 34
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maigari daƙuwa ya yiwa Indo ya ce, "Kinci gidanku ja'ira mara lissafi. Ashe har yanzu kina nan da wannan halin naki na rashin ɗa'a? Haka kuke zama da ita tana shuka muku tsiya? Rabona da ɗaga murya kamar haka har na manta" Mommy murmushi tayi ta ce, "Yaya ai yaran namu sai addu'a" Daddy ne yayi gyaran murya ya ce, "Yaya dama wata muhimman magana ce tafe damu kamar yadda aka fara yi maka ita a waya" Maigari gyaɗa kai yayi ya ce, "Na fihimta dangane da Sarƙa ko" Yaseer kallan Maigari yayi ya ce, "Kawu wane irin Sarƙa Humaira dai" Maigari wani kallo ya watsawa Yaseer ya ce, "Kai bana iya da wani ƙaƙalallan suna ba, ni da Sarƙa muka san Indo ba wani Humaira" Daddy ya ci gaba da cewa, "Mun zo nan gabaɗaya ne domin mu miƙa yarinyar nan hannun maruƙanta" Maigari ya ce, "Ehto! Wani hanzari ba gudu ba, ita fa wannan mariƙiyar tata ta koma birni da zama gidan ɗanta" Indo a zabure ta ɗago, tana kallon Maigari. Cikin faɗuwar gaba ta rushe ta kuka tana faɗin, "Ranka shi daɗe dan Allah ina suka koma yau na shiga uku" Maigari haushi Indo ta bashi a hassale ya ce, "Kinci ƙafar gidanku, da kina san nasu kika gudu kika barsu, kaji ja'ira mu zaki gwadawa kinibibi?" Daddy ne ya ce, "Allah ya huci zuciyarka Yaya yanzu ya za'a mu gana da ita wannan baiwar Allah?" Maigari ya ce, "Akwai wani yaro Hafizu Abokin Jamilu ne sai dai insa a kirawo shi ya yi mana jagora" Ajiyar zuciya Indo ta sauke tana jin sauƙi a zuciyarta, saboda ko ba komai ta san zatayi samu kwanciyar hankalinta ta huta da zaman gidan su Yaseer.
Maigari tashi yayi ya leƙo tsaka gida ya aiki Ɗansa Saminu, sannan ya koma ya zauna. Zama sukayi gurin yayi shiru kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyaraa, bayan wani lokaci sai ga Hafizu ya dawo tare da Saminu.Sai da ya gaishe da su Daddy sannan ya ce, "Allah ya taimakeka ance kana kirana ina fatan dai ba wani laifin nayi ba?" Maigari gyara zama yayi ya ce, "Kano zakayi mana jagora gidan da Baba Huwaila ta koma, waɗannan bayin Allahn sune suka dawo da Sarƙa. Zamu kaisu su miƙata a hannunta" da sauri Hafizu ya ɗago yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, har ya kai ga Indo dake zaune cikin doguwar rigar jar atamfa ta yane kanta da jan mayafi, cikin mamaki ya bin Indo da kallo ya ce, "Ranka shi daɗe Sarƙa ce ta koma haka, Allah ya baka yawan rai karadai ace Indo yawon duniya ta shiga..." da sauri Yaseer ya buga masa tsawa ya ce, "Kai Malam ka iya bakinka kayi abin da ya kawo ka kawai" Hafizu sosa kai yayi ya ce, "Ayi haƙuri nayi mamakin yadda Sarƙa da ganɗame rana ɗaya, naga ta murje shar kamar..." Maigari ya katse shi, "Kai Hafizu ka manta a inda kake ne?" da sauri Hafizu ya ce, "Tuba nake ranka shi daɗe" shiru ne ya biyo baya Daddy ya katse shirun da, "Yaya idan ba damuwa ko zamu iya tafiya yanzu?" Maigari ya ce, "Eh zamu iya tafiya tunda ga Hafizu, kai Hafizu ina fatan baka da wani uzuri yanzu" Hafizu gyaɗa kai yayi sannan suka tashi gabaɗaya suka fito daga gidan Maigari.
Su Maigari mota suka shiga gabaÉ—aya suka É—unguma suka nufi hanyar Kano wajen su Baba Huwaila.
BAYAN AWA ÆŠAYA
Tiryen-tiryen haka Hafizu ya dinga kwatantawa su Daddy hanya har suka ƙarasa unguwar Hotoro, a ƙofar wani madaidaicin gida sukayi parking sannan suka firfito su Momma ne suka fara shiga cikin gidan da sallama, wata mata ce ta tarbesu wacce batafi sa'ar su Mommy ba ta musu barka da zuwa. Ɗaki ta shigar da su bayan sun gaisa Mommy ta ce, "Ba mu kaɗai bane muna tare da baƙi suna waje, munzo da wata muhimmiyar magana da so samu ace Maigidan yana nan" Matar mai suna Hajiya Usaina ta ce, "Eh yana ciki amma shiryawa yake bari ayi masa magana, amma ina fatan babu matsala saboda bangane fuskokinku ba" Momma ta ce, "Mu tafe da yarinya Humaira wacce Baba Huwaila take riƙon ta a baya, mun dawo mata da ita ne kuma mu tattana a tsakaninmu" da sauri Hajiya Usaina ta ce, "Kardai ku ce mini Indo? Kai amma yau Baba Huwaila da tayi farinciki, bari nayi mata maga..." kafin ta rufe baki taji Mai gidanta ya shigo yana magana, gaishe shi su Mommy sukayi sannan Hajiya Usaina ta sanar da su dalilin zuwan su Momma.
Farinciki sosai yayi da sauri ya fita ƙofar gida wajen su Maigari yayi musu Iso zuwa babban falonsa, Hajiya Usaina fita tayi ta nufi ɗakin Baba Huwaila ta sanar mata da zuwan su Mommy, Baba Huwaila saboda sauri har kusan faɗuwa tayi. tana shiga falon ta fara dube-dube amma bata ga Indo ba, kallan Hajiya Usaina tayi ta ce, "Usaina bantaɓa zaton zakiyi mun irin wannan wasan ba, ina Indona take..." da sauri Indo ta taso ta rungume Baba Huwaila cikin shagwaɓa ta ce, "Baba Huwaila wai ni ɗin ce baki gane ba?" Baba Huwaila ɗagowa tayi tana ƙarewa Indo kallo ta ce, "Indo kece kika koma haka? Indo Allah sa ba wata rayuwa kika sauya ba kika zama uwar mata haka? Yanzu Indo dama zaki iya tafiya ki barni kullin cikin tunanin halin da kike nakeyi" Momma murmushi tayi ta ce, "Baba Huwaila ki zauna zaki samu duk bayanin da kike tambaya a gurinmu" Kafin Baba Huwaila tayi magana Alhaji ya shigo ya ce, "Yauwa ki shigo da su cikin falona muna cen gabaɗaya" yana juyawa Hajiya Usaina ta yiwa su Mommy jagora har cikin falon Alhaji, Baba Huwaila riƙe take da Indo tsam kamar wani zai kwace mata ita.
Zama sukayi a karo na biyu suka ƙara gaisawa, Baba Huwaila sai a lokacin ta lura da Maigari. Gaisawa sukayi tare da tambayar mutanen garin Kura, ruwa da lemuka aka zuɓe musu kala-kala. Indo na lafe a jikin Baba Huwaila ita kuwa Lubna sai yatsina take tana watsawa Indo harara a fakaice, kamar wacce aka zabure ta da sauri Indo ta ɗago ta ce, "Baba Huwaila ina Ya Jamil?" Baba Huwaila ido ta zubawa Indo tana mamakin yadda Indo ta iya magana cikin nutsuwa, daɗi sosai taji tayi murmushi ta ce, "Yayanki Jamilu yanzu ya fita amma ba jimawa zai dawo" Indo cikin wata irin muryar shagwaɓa ta ce, "Wallahi nayi kewarsa Baba Huwaila ni kaɗai idan na zauna sai nayi ta tunaninsa, wai har yanzu yana nan da muguntar sa?" Gaban Yaseer ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, saboda yadda yaji Indo ta ambaci sunan Jamilu har ji yayi ransa na masa wani irin ɗaci" Baba Huwaila ta ce, "To Indo bakya nan wa zai zalinta dama ai iya shegensa yasa yake zalintarki, shima bayan tafiyarki baki halin da ya shiga ba" Indo zuciyarta ɗaya ta ce, "Allah sarki Ya Jamil ashe haka yake sona sosai? Wallahi har ja matsu na ganshi" Baba Huwaila ta ce, "Muna nan zaki ganshi" Yaseer fesar da iska yayi mai zafi yana sunkuyar da kai ƙasa.
Daddy ne ya gabatar da kansu sannan ya sanar dasu dalilin zuwansu, da abin da suka sani akan Indo da yadda ta basu labarin tarihinta da asalin da duk abinda Baba Huwaila ta sanar da ita.
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce, "Lallai Allah ya taƙaita wahala kuma Addu'a tayi tasiri, mun godewa Ubangiji da yarinyar nan ta faɗa hannu na gari. Allah ya tsare ya ƙara shirya mana zuri'a, tabbas Indo tayi ƙuruciya amma mungode Allah, da Allah ya kawo lamarin cikin sauƙi. Kai kuwa Fahad Allah ya saka maka da mafificin alheri, tabbas kayi ƙoƙari kuma hakan da kayi shine dai-dai" su Daddy ba ƙaramin daɗin maganganun Alhaji suka ji ba, Baba Huwaila ce ta kalli Fahad ta ce, "Amma kuwa wannan yaro Allah ya saka maka da mafificin alheri da kayi sanadiyyar dawowar Indo ta, tabbas duk abinda Indo ta sanar da ku gaskiya ne kuma nima yanzu yan ƙara muku haska akan abin da ta sanar da ku" Baba Huwaila na zuwa nan Jamilu yayi sallama yana shigowa cikin falon. Cikin girmamawa ya gaishesu ƙur Yaseer ya kafeshi da kallo, har ya juya zai fita Baba Huwaila ta ce, "Jamilu ina zaka zo nan kaima ayi da kai man, kaga ƙanwarka Indo ta dawo" Zaro Ido Indo yayi yaja wani irin numfashi sannan ya sauke shi da ƙyar cikin wata Irin murya ya ce, "Indo ina kika tafi kika barmu" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wata irin dariya sannan ta ce, "To Ya Jamil ba gani andawo dani ba" Maganar Indo har tsakiyar kansa ta riskeshi mamaki ne ƙarara bayyane akan fuskarsa jin yadda Indo take magana, wai yau har shi take cewa Yaya. Koma yayi ya zama cen jikin bango yana fuskantar Indo, A fakaice Yaseer sai watsawa Jamilu harara yake yana jin wani irin haushi a zuciyarsa.
Baba Huwaila ce ta cigaba da cewa, "Tun ranar da Indo ta so tafiya nayi niyyar nuna mata wani abu da bata san da shi ba, wanda Goggo ta bani saura kwana biyu ta rasu. Ta ce mun kar insanarwa da Indo matsayinta har sai bayan Aurenta kuma a lokacin ya dace na ɗauko wannan abun na damƙa mata shi da ƙarin bayani. A lokacin da ta nunamin zata tafi na ɗauka wasa take mun saboda bata taɓa mun irin wannan maganar ba, lokacin da ta fita nayi niyyar na kiranta na miƙa mata kayan da Goggo ta bani, daga nan mu ɗunguma zuwa gidan Maigari domin mu san abinda zai aiwatar ga wanda ya tono da wannan maganar sai dai ban sameta ba" Baba huwaila janye Indo tayi daga jikinta ta ce, "Bari na je na kwaso muku kayan na saukewa kaina nauyi, saboda ban sani ba ko ina da ikon ganin lokacin auren Indo ko akasin haka, tun da daga ni babu wanda yasan da wannan kayan ko Jamilu bai san da su ba" Baba Huwaila na gama faɗa ta fice daga falon, gabaɗaya shiru sukayi banda ƙarar fanka babu abinda yake tashi a ciki.