Sashe 2
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga Baba Huwaila har Indo babu wanda yabi ta kan Mai Gari shima kuma ganin a yanayin da suke yasa bai wani jira jin ta bakinsu ba ya wuce gaba Maƙarrabansa na take mai baya, kai tsaye cen gidansa ya wuce domin adana takardun daya karbo.
Da sallama ya shiga cikin gidan har zuwa lokaci Baraka bata huce da haushin Indo ba shiyasama da yayi sallamar sama-sama ta amsa masa shima kuma dake zuciyarsa fes take bai tsaya jin mai ya ɓata mata rai ba ya wuce cen turakarsa ya buɗe ƙasan akwati ya ɗaga wata babbar rigarsa ya tura ciki sannan ya fito ya shaida musu rasuwar Goggon Indo, Baraka taɓe baki tayi ta ce, " Allah ya jiƙan musulmi " daga haka sabgar gabanta ta shigayi shima ya fice daga gidan.
Kafin wani lokaci tuni rasuwar Goggo ta karaɗe ko'ina kasancewar Goggo mutuniyar kirki ce bata da matsala da kowa idan kaji ta da wani kuwa sai dai idan Indo ce ta yo tsokana, ita kuwa ƙara goma idan za'a kawo mata bazata taɓa bawa Indo laifi ba, amma idan ka cire wannan babu abinda yake haɗata da kowa, hasalima mace ce mai yawan kyauta ko kaɗan abin hannunta bai rufe mata ido ba hakan ne ma yasa koda ɓarna Indo taje tayiwa mutum yana zuwa idan ya faɗa a take zata ɗauki kuɗi ta biya shi abinsa.
Wannan ne ya bawa Indo dama take cin karenta babu babbaka take shuka tsiyarta yanda take so tare da ƙawayenta, Zulai, Karime da Saude saboda sunsan muddun da Indo suka shuka tsiyarsu babu wani hukunci da za'a iya yi musu koda su kaɗai suka yo tsokanar suna sanarwa Indo take uwa tai makarɓiya masifar Indo ma kaɗai ta ishe ka.
Ƙofar gidan Goggo cike yake da mutane kowa na jimami da ta'ajibi, daga cikin gida kuma maƙota da abokan arzikin Goggo da ƙyar suka cire Indo daga jikin Goggo saboda irin gursheƙen kukan da take yi, duk wanda yake gurun babu wanda bai tausayawa Indo ba duba da irin soyayyar da ke tsakanin Indo da Goggo, wasu daga cikin matan lokaci-lokaci suke share ƙwallar idanunsu saboda tausayinta, a haka har akayiwa Goggo wanka aka fitar da ita aka sallace ce aka miƙa ta gidanta na gaskiya.
Baba Huwaila da ƴan uwanta sune suka zauna a ɗakin Goggo suka cigaba da karɓar gaisuwa har aka yi sadakar bakwai, tun ranar da Goggo ta rasu Indo ta zama wata shiru-shiru maganar kirki ma batayi daga ummm sai a'a, ko abinci ma sai Baba Huwaila ta matsa mata take iya shan kunu ko koko ko kayan sadaka bata iya sa komai abakinta, zuwa lokacin da akayi sadakar Bakwai Indo duk ta fige ta rame ta lalace kamar wacce ta kwanta ciwo idan ta ƙeɓe guri ɗaya sai dai taita share ƙwallah musamman idan ta dubi kayan sawar Goggo.
Washe garin sadakar bakwai Baba Huwaila ta haɗawa Indo kayanta tsaf acikin jaka da wasu daga cikin kayan Goggo, sauran kayan danginsu gado kwanuka da dai sauransu, Sailu dillaliya tasa aka kira mata gaba ɗaya aka saida su aka bata kuɗin, Indo lokacin da zata bar gidan su tayi kuka kamar ranta zai fita ayanda takeji kamar bazata iya barin gidan ba danma tana tuno wasiyyar da Goggo tai mata amma da ko ƙasa da sama zata haɗe babu inda zata ta gwammace tayi rayuwarta ita kaɗai.
Cen wani ɗakin ajiyar shirgi Baba Huwaila ta sa Jamilu ya gyara aka shinfiɗawa Indo tabarmar kaba da ƴar katifarta da ta taho da ita, daga bayan ƙaure ta ajiye jakar kayanta ta koma kan katifar ta rafka tagumi ta zubda hawaye.
Ganin haka ba ƙaramin damuwa yasa Baba Huwaila ba, zama tayi a kusa da ita ta dinga lallashinta har ta samu ta shawo kan Indo tai shiru daga ƙarshe har suka ɗan fara taɓa hira.
*BAYAN WATA UKU DA RASUWAR GOGGO*
Har zuwa lokacin Indo ba ruwanta da sabgar kowa gaba ɗaya ta koma wata saliha da ita hakan ne yasa wasu daga cikin mutanen garin suke murba har suna ganin kamar rasuwar Goggo shi ne silar shiryuwarta bisa shaiɗancin da take shuka musu a baya, wasu kuma sai suka samu ƙofa da kafar yiwa Indo wulaƙanci da cin zarafi yanda suke so.
Wata rana Indo na zaune ta gama cin ɗumamen tuwo su Zulai ne sukayi sallama Baba Huwaila na tsakar gida bayan sun gaisheta suka ce, " Baba Huwaila Indo zata ɗiban ruwa? " karaf Indo ta amsa tana fitowa daga ɗakin, " Eh zani zulai, Karime ga bokitina cen ɗauko mun mu tafi " ba musu Karime ta ƙarasa gindin tukwane ta ɗauko bokitin Indo na ɗiban ruwa, saboda gaba ɗayansu babu wanda Indo zata bawa umarni ya tsallake, haka suka jera suna tafe suna ƴan waƙoƙinsu haɗe da hirarraki.
A hanyarsu ta zuwa ɗiban ruwa suka haɗu da Lantan da zuwaira su Indo ne a gaba su Lantan na baya, suna cikin tafiya Lantan ta take takalmin Indo aikuwa lokaci guda igiyoyi biyu na jikin takalmin suka tsinke Indo har tana tuntuɓe bisa tsautsayi ta faɗa kan wani dutse ta gurje hannu, cikin jin zafi ta dafe gurin tana faɗin, " wash Allah hannuna " da sauri su Karime suka rufa kanta suna mata sannu, ganin Lantan ta ɗauke kai ko ajikinta yasa Indo ta kalleta cikin jin haushi ta ce, " Ke Lantan bakya ganin abinda kika mun ko sannu bazaki mun ba "
Lantan sai da ta kalli Indo sama da ƙasa sannan taja tsaki ta ce, " Hanya kika tare mun nikuma naga bazan iya ba na ƙara miki sauri " tana gama faɗa ta wuce abinta, Indo bin Lantan tayi ta kallo zuwa cen kamar wacce aka tsikara sai ji sukayi ta fashe da dariya, ita kanta Lantan sai da ta juyo tana mamakin jin dariyar Indo, lokaci guda ta tsuke fuska ta yunƙura ta tashi da ƙyar sannan ta nuna Lantan ta ce, " Ni Indo Sarƙa kika gayawa haka, wato sanyin da nayi na wasu ƴan kwanaki yasa har za'aci kashi a kaina, Lantan karki manta ko kura ta rame tafi ƙarfin gawurtattun karnuka " Lantan bata bi ta kan Indo ba ta juya tana mata waƙar habaici ita da Zuwaira suka cigaba da tafiya.
Indo iya ƙarfinta ta zage ta tafi da gudu ta baya tai tsalle ta ɗane wuyan Lantan ( _kasancewar Lantan irin dogayen nan ne sosai babu jiki_ ) Lantan ba tai aune ba sai jin Indo tai akanta duk yanda taso sauko da Indo abun ya faskara gashi ta ko'ina duka take kaiwa Lantan, ganin abun bana ƙare bane yasa Zuwaira tai kukan kura ta fara kaiwa Indo duka, su Zulai na ganin haka suka fisgo Zuwaira suna duka nan da nan faɗa ya rabu gida biyu, da ƙyar da suɗin goshi Lantan ta samu ta janyo Indo kasa kusan tare suka faɗi rigija kowa sa maida numfashi yake, Lantan na niyyar kaiwa Indo duka Aykuwa Indo ta ɗau bokin Saude na ƙarfe ta rafkawa Lantan a goshi.
Cikin tsananin azaba Lantan ta ƙwala ihu tana dafe gurin har jini ya fara zuba, ihun Lantan ne yaja hankulan su Zuwaira suka dakata da nasu damben cikin zaro ido suke kallon Lantan, ita kuwa Indo ko ajikinta miƙewa tsaye tayi ta fara karkaɗe jikinta ta koma ta ɗebo tsinkakkun takalmanta ta kunto ɗan kwalinta ta ɗauresu ta ɗaura ɗan kwalin ta saƙalosu ta wuyanta, bokitinta ta ɗauka ta kalli su Zulai ta ce, " Inzaku taho kuzo mu tafi inkuma jinyarta zaku zauna shikenan. " tana gama faɗa tayi gaba abinta.
Jiki a sanyaye su Saude suka É—au bokitansu suka marawa Indo baya kai tsaye burtsaten ÆŠan Iliya suka wuce.
Bayan fitar Indo dama Baba Huwaila shiri take akan zata je gidan Mai Unguwa dan ta same shi da maganar dukiyar Indo dan tunda Goggo ta rasu bai taɓa tunkarar Baba Huwaila da zancen yanda za'ayi da takardun gurinsa da Goggo ta ce araba biyu ba.
Lokacin da Baba Huwaila ta ƙarasa gidan Mai Gari cikin sa'a ta same shi a gida, yana ganin Baba Huwaila ya tsuke fuska yana faɗin, " Baba Huwaila ce ke tafe " mamaki ne ya kamata ganin sauyin Mai Gari amma sai ta basar ta ce, " Allah ya baka nasara ni ce dama nazo muyi wata magana ne ni da kai " ɗauke kansa gefe yayi sannan ya ce, " Faɗi inajinki "
Baba Huwaila kallan tsakar gidan tayi ta ce, " Allah ya taimakeka amma da mun É—an zauna ina ganin zaifi "
" Bama buƙatar zama saboda akan hanya muke yanzu haka fada zamu aka tsaida mu, faɗi meke tafe dake? " kasancewar Baba Huwaila nada matsalar ciwon ƙafa yasa ta janyo wata kujera ƴar tsugunno ta zauna sannan ta ce, " Dama naxo ne game da gadon Indo waɗannan takardun na gurinka, tunda dama marigayya kan ta rasu ta ce araba biyu abani rabi nayi ɗawainiyar Indo dasu, nikuma na duba naga koda nayiwa Indo wani abu da dukiya ta ba faɗuwa nai ba domin ko nice na faɗi na mutu Maryo zata kulamun da baya na, dan haka na yanke shawarar saida ƴan gonakin da akace abani intura Jamilu gidan Ƙanina dake birni suje ayi ciniki asaiwa Indo gida azuba ƴan haya duk shekara ana karɓar mata kuɗinta, inyaso sauran gonakin gurinka sai acigaba da yi mata noma ana ƙara siya mata kadarori dasu kaga kafin nan da ta samu mijin aure andaɗa tara abun arziki "
Mai Gari wata uwar harara ya watsawa Baba Huwaila sannan ya ce, " Kin gama? To ni ban lamunci wannan tsarin da kika zo da shi ba, hasalima ko takardar tsire bazaki samu daga gurina ba bare wata takardar gonaki, ke tsohuwa abinda baki sani ba wannan takardun sun shiga Asusun mabuƙata wai kin ɗauka bansan babu wata alaƙa tsakanin Indo da Goggo bane? Kinzaci banda tarihin Goggo tsinto Indo tayi tun tana jaririya ne? To wallahi maganar nan ma idan ta sake ta kuma fita daga bakinki sai na ƙulla miki baƙin sharrin da sai kinji kamar kibar garin nan " yana gama faɗa ya kaɗa babbar rigarsa yayi gaba ya bar Baba Huwaila zaune mamaki ya mamaye ta.