← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 76

Sashe 37

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba Huwaila ita wannan Safna da kika ji muna maganar ta Ƙanwata ce ita take bi na uwar mu ɗaya ubanmu ɗaya, ni na riƙeta da hannuna har muka aurar da ita, duba da yanayin da kike ciki ba lallai ki amince da abin da na faɗa ba, amma akwai hotunanta a wayata idan kina buƙatar gani sai ki duba ki gani da ta jikin wannan hoton da kika bamu" Daddy ya ce, "Baba Huwaila Shi wannan Khaleel da muke magana, Ƙanina ne uwar mu ɗaya Ubanmu ɗaya kamar yadda kika ji Momman yara ta faɗa nima ahannuna na riƙeshi, kasancewar tare muka riƙesu har suka shaƙu suka fara soyayya, bayan sun haɗa kansu aka tsaida magana mukayi musu aure, amma ki yarda da mu baza mu ƙirƙiri abinda va haka bane" Baba Huwaila jikinta ne yayi sanyi, cikin sanyin murya ta ce, "Idan kuwa haka ne nafi kowa murna da bayyanar Iyayenki Indo, Allah na gode maka aikuwa har garin Kura sai naje, ki nuna mun waɗanda suka yi miki gorin iyaye." Shiru Baba Huwaila tayi sannan ta ci gaba da cewa, "Sai dai nasan ba lallai su bar min ke ba Indo,hakan kuwa ba ƙaramin ciwo zai mun ba" Yatsuna fuska Fahad ya yi ya ce, "Daddy nifa gaskiya ina da ja ya za'ayi a ce Aunty Safna ce ta haifi wannan abar, yarinya kamar ƙanwar Ifritu..." Mommy ce ta watsa masa daƙuwa tana katse shi ta ce, "Gidan ku Fahad wai me yarinyar nan tayi maka ka tsangwameta haka ne? Zan ɓata maka rai idan na kuma jin bakinka" taɓe baki yayi yana ɗauke kai gefe Indo ɗagowa tayi ta ce masa, "Idan ni ƙanwar Ifritu ce sai dai idan kaine Ifritun" Yaseer binta yayi da kallo ganin yadda take kwaɓe baki kamar ba ita ba, uwa uba mamakin tsiwarta yake. Aikuwa kamar ta watsawa Fahad ruwan zafi a hassale ya ce, "Mommy kunji ko wallahi kika bari na kama kinsai na karyaki biyu" Indo miƙewa tayi ta koma ce lungu kusa da Baba Huwaila tana watsa masa harara ta kalli Jamilu ta ce, "Ya Jamil wallahi ka ja maka kunne, ya kuma cewa zai karyani wallahi sai na kuma sa masa mage a riga, matsoracin mage" Su Daddy dariya suka saka Mommy ta ce, "Humaira ya akayi kikasan Fahad na tsoron mage naga gidan Moma babu mage" wata dariya Indo ta bushe da ita sannan ta ce, "Lokacin da kuka zo Kura ranar da zaku tafi nina haɗa masa tarko da gafiya Mage ta maƙale masa a wuya" gabaɗaya ɗakin babu wanda bai sa dariya ba banda Yaseer da yake cika yana batsewa, Maigari murmushi yayi yana riƙe baki ya kalli Indo ya ce, "Sarƙa amma dai ke anyi shakiyyar yarinyar ashe baƙo ma baki bari ba, wallahi lokacin da kika tafi kunne na shiru da kawo ƙara" Jamilu ne ya kalli Fahad da ya tamke fuska saboda abinda Indo ta faɗa ya ce, "Kabi a sannu nasan har yanzu baka san wace Indo ba, ina baka shawara karka shiga harkar ta bana shiri da duk wani mai shiga sabgarta dan ya takura mata" Lubna da ke gefe wani yawu ta haɗiya musamman da ta tuno shaƙar da ta yi mata a ɗakinsu, sai dai wani abu da ya tsaye mata arasa wacce za'a ce ƴar Uncle Khaleel ce sai wannan banzar yarinyar? A fakaice take kallan Indo tana watsa mata harara, tana jan ƙwafa ƙasa-ƙasa.

Momma ce ta ciro waya Daddy ya kalleta ya ce, "Me zaki yi?" Momma ta ce, "Zan kira Safna nayi mata albishir" girgiza kai Daddy yayi ya ce, "Karki gaya mata, kawai ki ce mata daga Kano zamu biyo ta Kaduna mu gaisa da su" Momma amsa masa tayi sannan ta kira wayar Mahaifiyar Indo, daga cen ɓangaren aka ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa Momma ta ce, "Idan mun gama da Kano zamu biyo ta Nan Kaduna mu gaisa" cikin murna ta amsa mata sannan sukayi sallama.

Bayan Momma ta gama waya Daddy ne ya kalli Alhaji ya ce, "Alhaji idan babu damuwa ko zamu zo mu wuce saboda yanayin gari kar lokaci ya ƙure mana" Alhaji ya ce, "Amma da ku bari ku ci abinci mana" Momma cikin zumuɗi ta ce, "Ai mun riga da munci a gidan Yaya" Daddy ya ce , "Alhaju bamu da yunwa amincewar ku kawai muje jira." Alhaji ya kalli Baba Huwaila ya ce, "Baba zaki bimu ko mu je mu dawo" Baba Huwaila tayi karaf ta ce, "Haba Ɗan nan yanzu ko cewa nayi bazani ba ai ka tursasani, ai ƙafara ƙafar Indo" gabaɗaya Falon aka kwashe da dariya.

Su Baba Huwaila shiryawa sukayi sannan suka ɗunguma suka ɗauki hanyar Kaduna, Alhaji ne ya ɗauki Baba Huwaila da Indo sai Jamilu, baƙin cikin duniya ne ya cunkushe Yaseer, saboda ya ɗauka Indo motar sa zata ƙara shiga. Har buɗe mata ƙofa yayi amma tayi wucewarta ko kallan gurinsa batayi ba. Lubna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta wuce ta buɗe gaban motar ta shige, Yaseer tun da suka tafi yake tsaki itama Lubna ganin yanayinsa babu walwala yasa taja bakinta ta tsuke, dan ta san gab yake da ya sauke mata kwandon masifa a kanta. Daddy tun a hanya ya ja kunnensu akan koda sun je abi komai a sannu banda garaje dan so yake yayiwa su Aunty Safna suprise.

BAYAN WASU AWANNI

Suka ƙarasa cikin garin Kaduna, a katafaran wani ƙofar gida suka tsaya suna Horn. Ba'a ɗauki lokaci ba Maigadi ya leƙo ganin Daddy yasa ya buɗe ƙofar da sauri yana musu sannu da zuwa, Su Baba Huwaila sai bin gidan suke da kallo, kallan Jamilu tayi ta ce, "Jamilu anya mutanen nan ba yaudarar mu sukayi ba dan su kawo kawunan mu nan gidan ba, gaskiya akwai lauje cikin naɗi wannan gida kamar ba a ƙasar nan ba" Indo dariya tayi ta ce, "Baba Huwaila wallahi bazasu sayar da mu ba, gidan su Momma ma fa haka yake baki ganshi ba me kyau" Alhaji ya ce, "Haba Baba Huwila da ganin mutanen nan nagari ne bazasu aikata haka ba, ko da yanayin shigar su kika lura ai kinga masu aiziƙi ne." Jamilu watsawa Indo Idanunsa yayi yana mata murmuahi, wani irin nauyinsa ta ji. Take ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da zaren mayafinta, tuni sun shiga cikin gidan Jamilu bai sani ba. Sai da Alhaji ya ce,"To ku fita muje" yana gama faɗa ya buɗe ƙofar ya fita, sannan Baba Huwaila ta buɗe ta taka da ƙyar ta fita saboda yadda ƙafarta ta mata tsami, Indo na ƙoƙarin fita Jamilu ya ce, "Ayusher!" Indo dakatawa tayi ta ɗan waiga dan ganin ko akwai wacce Jamilu yake wa magana, amma bata ga kowa ba. Sai dai maganar sa ta ratsa har jinin jikinta saboda yadda ta ji muryarsa ba haka ya saba magana ba, sunkuyar da kai Indo tayi ta ce, "Ya Jamil dani kake magana?" Jamilu shiru yayi yana kallan Indo, jin yayi shiru ya sa Indo ta ɗago da kai, karaf suka haɗa ido ya sakar mata wani malalacin murmushi. Sannan ya ce, "Ayusher shi ne kika tafi kika barni, bakiyi tunanin zan iya shiga damuwa ba?" Indo ɗagowa tayi tana mamakin jin kalaman Jamilu, sannan ta sunkuyar da kai ta ce, "To Ya Jamil ai gashi na dawo" Jamilu murya a sanyaye ya ce, "Ba gashi zaki ƙara tafiya ki barni ba, kinsan yadda nayi kewarki kuwa?" Indo zuciyar ta ɗaya ta ce, "Ya Jamil dama kana sona amma kake dukana?" Jamilu ya kwaikwayi muryar ta ya ce, "Bakiji bahaushe me yace ba, kaza na taka ɗanta ba dan bata sanshi ba..." Indo na shirin magana Jamilu ya ɗan tsuke fuska ya ce, "Wai ya kuke da waɗancen samarin naga suna min wani gani-gani" Indo zata buɗe baki tayi magana suka ga Yaseer ya tsaya ta bakin murfin motar, fuska a tsuke ya zuro kai ya ce, "Ke Humaira ki fito mu ƙarasa ciki" Indo yunƙurawa tayi zata fita Jamilu ya tsuke fuska ya ce, "Ayusher! Na baki umarnin tafiya ne? Indo komawa tayi ta zauna. Cikin jin haushi Yaseer ya ce, "What? Kai wai kai waye ne naga sai wani zaƙewa Humaira kake?"

🤗🤗🤗🤗 LAMARIN ZAI FARA ƊAUKAN HAZO FA🧐🧐🧐🧐🧐

KUYI HAKURI DA RASHIN REPLAY NA COMMENTS ƊINKU ARADU DUK NABI NA GANI INA GDY😘😘😘😘😘😘😘 ALLAH YA BAR ƘAUNA🥰🥰🥰🥰🥰 MU HAƊE A COMMENTS.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

*ÆŠAN ÆŠANO DAGA LITTAFIN SIRRIN MU*

Yadda kake tunanin rayuwa ba haka take ba,da lokota da dama kana iya gane SIRRIN wasu, Amma wani lokaci naka SIRRIN dake bibiyar Rayuwarka wahalar gane masa kake,Yau Uban daya haifesa ya kawosa Duniya shine da gansa ya masa sharri,Shi ne ya saka za'a kai shi gidan yari,Matar da yafi so fiye da komai nasa,wacce ta zame masa Uwa,Uba,Yaya,Ƙanwa,Aboki yau itace Mahaifinsa ya kwanta da ita har ta ɗauki cikinsa,Kuma yanzu shine ake cewa shi yay mata CIKIN,da me zaiji? Da nakasar da take damunsa?ko kuma da BAƘON YANAYIN daya tunkaro sa?Wannan SIRRIN MU ne bai kamata ace kowa ya jishi ba,SIRRIN MU ne nida mahaifi na,SIRRIN MU ne nida Matar da nakeso, SIRRIN MU ni da Aljanun da suke tare da ita.

_JAMA'A WANNAN MARUBUCIYAR CE DAI WACCE TA NISHAƊANTAR DAKU A LITTAFIN *MOON* DA *UNCLE NE* GA KUMA *THE NEW EMIR* SBD NIN DAƊIN MASOYA YASA SAI TA GAMA PART ONE ZATA FARA SAKINSA WANDA ZATA NA BAWA ƳAN *VIP* POSTING 2 KULLUM A RANA ƳAN *NRML GRP* KUMA POSTING ƊAYA A RANA NASAN KUSAN *NIMCYLUV* TAURARUWAR MARUBUCIYA MAI TASHE😂

ZAKU IYA PAYMENT TA WANNAN ACCOUNT ÆŠIN

0116886423
Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616

400 for nrml grp
600 for vip

Nima AMEERA ADAM na shiryar tsaf domin karanta littafin *SIRRIN MU*
[20/08, 19:44] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_
Chapter 37 · 0% Book details