Sashe 18
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Huwaila itama miƙewa tsaye tayi ta dafa kafaɗar Indo tace, " Kina da kowa mana tunda kina dani " girgiza kai Indo tayi ta ce, " Baba Huwaila bansan gawar fari ba idan aka wayi gari babu ke fa " Jim Baba Huwaila tayi tabbas tasan maganar Indo akan hanya take da sauri ta cewa Indo, " Ga Jamilu nasan zai riƙeki har abada " Indo girgiza kai tayi ta ce, " Baba Huwaila wannan ba hujja bace, a yau basai gobe ba zan shiga duniya innemo dangina, idan ma ni shegiya ce shikenan zan cigaba da rayuwa acikin mutanen sa basusan asalina ba " Baba Huwaila kuka ta fashe dashi ta ce, " Indo dan Allah karki mun haka, akan Idonki Goggo ta bani amanarki idan kika mun haka zan kalli kaina amatsayin maciya amana " Indo murmushin yaƙe tayi ta ce, " Karki damu baba Huwaila duk inda zanje bazan aikata wani abun muni ba kina nan insha Allah wata rana zan dawo gareki, idan kuma shirun yayi yawa to ƙila ta Allah ta kasance " Indo na gama magana ta sa kai ta nufi hanyar waje Baba Huwaila fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[13/07, 19:21] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
39&40
Indo jin kukan Baba Huwaila take har cikin zuciyarta, runtse idanunta tayi tana jin wani iri acikin ranta, bayan Goggo babu wacce ta shaƙu da ita take jin ƙaunarta har cikin zuciya kamar Baba Huwaila, shashsheƙar kukan Baba Huwaila ne ya dawo da ita daga ɗan guntun tunanin da ta shiga, juyowa tayi ta ɗan kalleta take guntun hawayen da take maƙalewa ya gangaro saman kumatunta, jiki a sanyaye ta sa kai ta fice daga gidan, Baba Huwaila na ganin fitar Indo ta fashe da wani irin matsanancin kuma mai taɓa zuciya, Baba Huwaila yunƙurawa tayi da ƙyar ta ɗan ɗingiso ta fara takowa zuwa ƙofar gida, dube-dube ta shiga yi babu Indo babu alamarta.
Wani sabon kukan ne yazo mata haka ta cigaba da share hawayenta, wani tunani ne ya faÉ—o mata kai tsaye ta wuce gidan Maigari tana tafe ko kallan gabanta bata yi, tana shiga cikin gida ko sallama ta kasa furtawa saboda yanda take sauke ajiyar zuwa, Magajiya ce ta tare da tambaya jin an ambaci sunan Baba Huwaila yasa Maigari fitowa saboda yasan dama za'a rina..."
Maigari ganin yanayin Baba Huwila ba ƙaramin sanyaya masa jiki yayi ba, jiki ba ƙwari Maigari ya fara watso mata tambaya, " Lafiya Baba Huwila me yake faruwa " Baba Huwaila majina ta fyace sannan ta ce, " Allah ya baka yawan rai suna korar mun Indo, ta tafi ta barni bansan inda ta tafi ba " da mamaki Maigari ya ce, " Su waye suka koreta kuma ina ta tafi? " Baba kwashe yanda sukayi da Indo tayi sannan ta ɗora da cewa, " Ba yanda banyi da yarinyar nan akan ta sanar dani waɗanda suka gaya mata maganar nan amma taƙi dan Allah ka taimaka ka baza mutane a nemo min ita yanzun nan ta fito daga gida amma na nemeta sama ko ƙasa na rasa " wata gwauruwar ajiyar zuciya Maigari ya sauke cikin zuciyarsa yake hamdala da Indo bata sanar da Baba Huwaila Baraka ce ta gaya mata ba, nunfasawa Maigari yayi sannan yace, " Ashsha gaskiya lamari baiyi daɗi ba amma bari na fita nasa su Ado su fita ciki da wajen ƙauyen nan Insha Allah zasu dawo da ita, karki ɗaga hankalinki Baba Huwaila wannan ba abin damuwa bane kinsan shaƙiyancin Sarƙa yanzu haka ma gwada ki kawai takeyi " girziga kai Baba Huwaila tayi ta ce, " Kai gaskiya jikina yana bani Indo ba wasa take mun ba tunda duk abin Indo bata taɓa gwada mun irin wannan wasan ba " Maigari ya ce, " Insha Allah yanzu zasu nemo ta " kusan tare suka fito da Baba Huwaila tare suka ƙarasa fadar Maigari inda su Ado suke, sanar da su akayi abinda yake faruwa take suka ɗauki ƙananan lasifiku suna shelar ɓatan Indo.
Indo na fitowa gyara wuyan hijabinta tayi ta kunto bakin zaninta dubu ɗayan da Mommy ta bata ta ciro, da sauri ta fara tafiya kai tsaye hanyar tasha ta nufa, tana tafe tana duba mota kowacce tazo acike take har ta kusa ƙarasawa bakin tasa taga wata motar Bus ta taho, da sauri Indo ta tsayar da ita tana faɗin, " Kano ne? " da sauri kwandastan ya ce, " Kano mukayi ƴan mata " buɗe mata murfin ƙofar akayi Indo ta kama mota ta haye, tana hayewa Driver ya bawa motarsa wutasuka wuce kai tsaye motarsu ta wuce garin Kano.
Baba Huwaila na komawa gida sai a lokacin ta tuno da wayarta da sauri ta ɗauki wayar ta shiga gidan Malam Musbahu, Ɗan wajen Malam Musbahu ta bawa wayar ta sashi ya nemo mata lambar Jamilu ya kira mata, karɓa yayi ya kira mata tana fara shiga ba jimawa Jamilu ya ɗauka.
Ko amsa sallamarsa batayi ba cikin tashin hankali ta fara magana, " Jamilu kana ina maza kazo Indo ta ɓata dan Allah kazo yanzun nan " murmushin takaici Jamilu yayi ya ce, " Haba Baba Huwaila kawai saboda kinsan yarinyar nan acikin zuciyarci sai kuma ta dinga ɗaga miki hankali, ba gaira ba dalili. Kinsan dai shaiɗancin Indo sarai ba wanda baisan halinta ba kima kwantar da hankalinki kina zaune zata dawo saboda..." Cikin hassala Baba Huwaila ta katse shi, " Jamilu idan ban isa da kai ba shikenan ina nuna maka gabas kana rintse ido kafin sanin wacece Indo ne? Idan bazaka zo ba shikenan " Baba Huwaila na gama magana bata jira cewar Jamilu ba ta kashe wayar gabaɗaya.Jamilu kira ya ƙarayi amma Baba Huwaila bata ɗauka ba sallama tayiwa matar Malam Musbahu ta koma gida jiki ba ƙwari.
Su Indo basu jima da tafiya ba wasu fasinja suka tsayar da motar mutum biyu ne suka hau sunna shiga suka ga Indo zaune akan kujera, da mamaki suka kalleta Malam Bala ya ce, " Sarƙa yau kece a mota ina zuwa haka ina kuma kika baro Baba Huwaila? " Indo ta fahimci su Malam Bala basu fahimci komai game da ita ba, ɗauke kai gefe tayi tace, " Aikena akayi birni " cikin mamaki Lauwali yace," Birni fa Sarƙa Ina Jamilun da Baba Huwaila zata turaki har Kano? " hararara Indo ta watsa mai tace, " Ni ɗin bazan iya zuwa ba kenan ina kano ina Kura, kudai bakwa gani ku ƙyale " gaba ɗaya baki suka ja suka tsuke saboda sun san idan suka biyewa Indo sai ta tsinka su agaban mutane, motar ce tayi tsit ba magana suka cigaba da tafiya.
Jamilu sanar da Principal yayi kiran da akayi masa na gaggawa daga gida, sanin Jamilu mai himma ne kuma baya wasa ko kaɗan a ɓangaren aikinsa yasa yana tambaya Principal bai tuhumeshi ba, tafe yake yana sauri kamar zai tashi sama har ya ƙaraso gida, yana zuwa gida Baba Huwaila ta fashe masa da kuka tana bashi labarin yanda sukayi da Indo, dukda ba wani shiri suke da Indo ba amma maganar ta matuƙar girgiza shi, takalmansa ya shura ya fice daga gidan domin nemo Indo.
Tafiya sukayi mai nisa sannan suka shigo cikin garin kano, motarsu na zuwa Unguwa uku su Lauwali suka sauka, Bala ne ya juyo ya cewa Indo, " Sarƙa kina ganin Hanya ko? Kinsan fa cikin gari daban yake da karkara " Gyaɗa masa kai kawai Indo tayi saboda tun lokacin da ta fahimci sun shigo cikin gari gabaɗaya taji zuciyarta ta ƙara mata ba daɗi, ji take kamar ta dakatar da motar ta koma garinsu, tana ta tunane-tunane har motarsu ta ƙarasa Kano line, yawancin mutanen da Indo ta samu da wanda suka sameta aciki duk sun sauka, Kwandastan ne ya kalli Indo yace, " Ya ƴan mata har yanzu ba'a inda zaki sauka bane? gaskiya sai dai mu saki a mota dan bazamu ƙarasa Ƴan kura ba " Indo muzurai ta farayi tana ƴan dube-dube bata bashi amsa ba, Kallanta Kwandastan yayi ya ce, " Sakko ga mota cen Ungo Talatin ki basu zasu ƙarasa da ke " Jiki ba ƙwari Indo ta karɓi kuɗin ta sauka tana sauka kuwa suka bawa motarsu wuta.
Indo tsaye take motoci da ƴan Adaidaita sahu sai wucewa suke, wasu suyi mata horn wasu kuma su wuce, tsaye take kusa da wasu mata ɗaya tana ƴan shekaru dan Aƙalla zatayi shekara arba'in da uku ba, ƴar matashiyar budurwae batafi shekara ashirin ba, suna nan tsaye wani Mai Napep yazo ya tsaya a gabansu, babbar macen ce ta ce, " Medile " gyaɗa kai yayi ya ce, " Ku duka ukun? " Matar ce ta kuma cewa, " A'a mu biyu ne amma bansani ba ko ita cen tayi " tana magana tana taunar cingam ƙas ƙas ƙas, Mai Adaidaita sahun ne ya kalli Indo yace, " Kema cen kikayi? " Indo samun kanta tayi da gyaɗa kai, Mai Adaidaita sahun ya ce, " Kuɗinku ɗari da hamsin-hamsin " ba ko tantama matar tace, " Preety shiga muje " wacce aka kira da Preety shiga tayi Indo na ƙarewa yanayin shigarta kallo, matar ce tabi bayan Preety sannan Indo ta shiga.