← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 76

Sashe 19

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda suka fara tafiya matar da taji ana kira da Aunty take ta ɗan jan Indo da hira, amma Indo sai dai tace Ummm ko uuummmm-uuummm, tafiya sukayi me ɗan nisa suka ƙarasa Medile, Auntyn Preety ce ta tsaida ɗan sahu suka sauka itama Indo sauka tayi ta miƙa masa ɗari biyu ya bata hamsin, akan Idonta su Preety suka tsallaka titi suka shiga wani layi, awannan lokacin ne taji anfara kiraye-kirayen sallar Azahar, Indo banda kalle-kalle ba abinda takeyi juyawa tayi ta fara tafiya batasan inda take jefa ƙafarta ba, tafiya tayi Mai nisa sannan ta nemi bakin wata bishiya ta zauna tana hutawa,wata me wake da shinkafa ta hango kiranta tayi ta sayi ta nera ɗari saboda yanda taji cikinta yake mata ƙugi, kafin wani lokaci tuni ta cinye tas.A cen nesa ta hango famfo ƙarasawa tayi ta tara hannunta ta sha sannan ta ɗaura alwara ta shinfiɗa ɗan kwalinta tayi sallah, tana nan zaune ita kaɗai take nazarin inda ta dosa, bata taɓa tsammanin haka a rayuwarta ba wata irin ƙwallah ce ta zubo mata da ta tuno Baba Huwaila, yanda take nan-nan da ita akan taci abinci amma wai yau ita da kanta ta nemi abinci har ta siya da kuɗinta, hawayen fuskarta ta goge ta tashi ta karkaɗe ɗan kwalinta ta ɗaura aka sannan ta cigaba da tafiya.

Indo tun tana tafe tana hutawa ta gabatar da sallah har ta fara gajiya ga duhun dare ya farayi, daga Medile zuwa Tukuntawa Indo tayi zaryar hanyar yafi sau biyu, gabaɗaya ta galabaita ga gajiya ga tunanin inda ta dosa a haka tana tafiya har dare ya tsala, wani shago ta hango arufe da alama Provision ne, ƙarasawa tayi ta shiga cikin rumfar ta zauna a gefe ta takure guri ɗaya, gabaɗaya idonta ya bushe babu alamar bacci acikinsa, banda kukan karnuka babu abinda yake tashi, tana nan tsugunne ta ga wasu matasa su Biyu sun fito daga wani layi dake kallan gurin da take a tsugunne, hasketa ɗaya yayi da fita ɗayan yace, " Kai Boss wa nake gani kamar cika agurun cen " wanda aka kira da Boss yace, " Ai ba kama bace Uzee wata ƴar shilar muka samu " suna gama magana suka ƙarasa cikin rumfar, Indo na ganinsu jikinta ya hau tsuma miƙewa tayi tsaye, ɗaya daga cikinsu ne yace, " Ƴan mata ke kuwa lafiya me kikeyi da tsohon daren nan agurin nan? " Indo jiki a sanyaye tace, " Daga Kura nake ni baƙuwa ce " Kallan juna sukayi zuciyarsu ƙal sanna Boss yace, " Zamu taimaka miki tunda kina mace zaman gurun nan bai kamace ki ba" Indo sam bata yarda dasu ba duba da yanayin shigarsu, girgiza kai tayi ta ce, " A'a nagode zuwa safiya zan nemi gurun zama " Kallan juna suka ƙarayi suna ƙifta ido da sauri Uzee ya fisgi hannun Indo, ganin haka yasa ta ƙwalla ƙara domin neman taimako, a zafafe Bosa ya kifa mata mari kafin ta ɗago ya ƙara kifeta da wani marin, hannunsa ya sa ya shaƙi wuyanta har sai da ta fara kakarin amai idanunta sun firfito, sakinta yayi ya zaro wata wuƙa a ƙugunsa yana nuna mata sannan yace, " Idan kika kuma yimun Ihu sai na kasheki na kashe banza a gurun nan "

WAYYOOOOOO JAMA'A KUJE KU CETO INDO, MAMAN NASEER INDONKI NA CIKIN WANI YANAYI🥴🥴🥴🥴🥴

NASO NAYI MUKU YAFI HAKA BANA SAMUN CAJI SOSAI NE☹️

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[14/07, 13:56] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

41&42

Indo wani irin yawu ta haɗiya na wahala Uzee ne yake janye da hannunta suna gaba Boss na biye dasu a baya, Indo jikinta banda karkarwa babu abinda yakeyi gumi ta ko'ina sai keto mata yake, tafe take tana ɗan waigen Boss a tsorace gudun kar cutar da ita, wannan karan ma juyowa tayi cikin kuka ta ce, " Dan Allah ku taimaka kuyi haƙuri karku cutar dani wallahi ni marainiya ce " daga bayanta Boss ne ya buga mata uwar tsawa yace, " Allah sa ke ƴar wahainiya ce ba maraniya ba idan kika ƙara magana sai na sa miki kaifi " daga haka Indo bata ƙara magana ba tafi sukayi ɗan nisa sannan suka hango ƙyallin fitila wasu mutane ne suke tunkaro su da alama kamar ƴan bijilanti ne, da sauri suka faɗa wani lungu Uzee ya ce, " Ga wasu mutane cen idan kika sake kikayi abinda zasu gane kina gurin kinga waccen wuƙar sai mun huda wuyanki da ita " Uzee na gama magana Boss ya sawa Indo wuƙa a wajen wuyanta, Indo ba magana banda gyaɗa kai babu abinda takeyi.Suna nan tsaye har mutanen nan suka zo suka wuce a lokacin Indo ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta tashi, banda ruwan hawaye babu abinda takeyi.

Sai da ƴan bijilantin nan sukayi nisa sannan su Boss suka fito daga lungun suka cigaba da tafiya, basu ƙara tafiya mai nisa ba suka fita kan titi tsallakawa sukayi suka shiga wani layi a bakin wani ƙaramin gida suka tsaya, Boss ne yasa mukulli ya buɗe gidan ya fara wucewa, Uzee jan hannun Indo yayi zasu shiga cikin shammata ta gantsara masa cizo a hannu, yana jin azaba ya saketa yana ɗan kwalla ƙara, da gudu Indo ta juya ko kallan gabanta batayi bisa tsautsayi tana fita titi wata mota ta kawo kai ta bigeta, atake Indo ta sulale ta faɗi a gurin tana sauke numfashi da kyar, su Boss da suke biye da ita a baya suna ganin haka suka dakata da sauri suka koma dan gudun asirinsu ya tonu.

Mutanen dake cikin motar mace da namiji ne, da sauri suka fito daga motar da ganin wacce suka bige, Indo dukda tana cikin mawuyacin hali yunƙurin tashi take tana nuna musu hanya, jini na ɗiga daga goshinta murya a hankali take faɗin, " Dan Allah ku taimaka mun zasu cutar dani " Namijin ne ya kalli gurin da Indo take nunawa amma sam baiga komai ba, macen ce ta kama hannun Indo ta ce, " Sannu kinji " Namijin ne yace, " Dear ya zamuyi da yarinyar nan? " wacce ya kira da Dear ta ce, " Ɗaukanta zamuyi Sweet dan bazamu barta acikin wannan halin ba, da alama tana cikin firgici tunda har yanxu ba ta jikinta take ba " wanda aka kira da Sweet yace, " Bari na ɗaure mata kanta da ɗan kwalin nan ko jinin ya rage zuba, da sauri ta janyo ɗan kwalin Indo ta fara ɗaure mata kai, tana gamawa suka ja hannun Indo zasu sa ta a mota, tirjewa Indo tayi ta ce, " Dan Allah karku cutar da ni wallahi ni marainiya ce " da mamaku suka kalli juna macen ta ce, " Look at this gal, munyi miki kalar macuta ne? Idan bakyasan taimakanmu you can go " ta ƙarasa magana tana buɗe murfin motar sannan ta cigaba da cewa, " Sweet zo mu wuce " kallan Indo yayi yace, " Kinfi san mu barki agurin nan " Indo girgiza kai tayi kwalla na zuba daga idonta, buɗe mata kofar baya yayi jiki ba ƙwari Indo ta shiga ya rufe shima ya shiga sannan ya bawa motarsa wuta.

Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka shiga wani layi, a wani madaidaicin gida sukayi parking, jakarta ta zuge ta ɗauko mukulli sannan ta fito ta buɗe gidan, dawowa tayi ta buɗewa Indo mota sannan ta leƙa ta ce masa, " Sweet bari na shiga da yarinyar nan sai muji ya za'ayi da ita " leƙo kansa yayi ya ce, " Ok Dear, amma ina ganin ko asibiti zamu kaita " Yatsina fuska tayi ta ce, " A cikin duhun daren nan wane asibiti zamu kaita? kasan dai ko mun kaita asibiti sai sun ce mu taho da Police, tunda dai jinin ya tsaya da zuba mu bari zuwa safiya sai mu kaita ayi mata check up " murmushi yayi ya ce, " Ok Allah ya kaimu " yana gama magana bata jira cewarsa ba ta wuce gaba Indo na biye da ita a baya.
Chapter 19 · 0% Book details