Sashe 10
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan la'asar liƙis wajen doshin magriba wata danƙareriyar mota baƙa wuluk da gilashinta baƙi baka iya gane wanda yake ciki ce tayi parking a ƙofar gidan Mai gari, daga bayan motar aka fara buɗewa a hankali, wata dattijuwar mata ce ta zuro ƙafarta sanye da wani tsadajjen takalmi ruwan zaiba da ɗigon ja, kafin ta ƙarasa fitowa wani matashi ne ya buɗe wajen mazaunin Driver, tun kafin ya ziro ƙafarsa kamshin turarensa ya fara zagaye harabar gurin, cikin nutsuwa ya dai-daita ƙafarsa yana sannan ya sauko da ita bisa doro ƙasa, Mahaifiyarsa ce ta fara fitowa tana ƙarewa yanayin garin kallo, murmushi ta saka musamman da ta kalli wata kwatuwar bishiyar Mangwaro dake kallan gidan Maigari, tunowa tayi da ƴanmatancin su da irin gararanbar da suka sha, wasu ƴan mata biyu ta hango a ƙasan bishiya sun ɗaga kansu sama da alama kallan mai ciro musu mangwarn suke suna jiran faɗowarsa, Fahad dafa murfin ƙofar yayi ya fito daga cikin motar yana kallan yanayin tsarin garin yana ɗan yatsina fuska.
Daga cen gefen su Zualai ne ke wa Indo magana saboda ganin ta shanyasu tun tsayuwarsu mangwaro biyu kawai ta jefo musu.
" Sarƙa tun ɗazu fa muke jiranki wallahi munsan dama sai kinsha kin ƙoshi zaki jefo mana " Indo siɗe ruwan mangwaron hannunta tayi cikin masifa ta ce, " Wallahi Saude ke da mayya ce da sai dai aga gawata ta faɗo " cikin jin haushi Saude ta ce, " Amma ai ba haka mukayi da ke ba "
Fahad kallan gurin yayi yana ƙarewa ƴanmatan kallo yana ɗan yamutsa fuska, jin maganar Indo yasa shi ɗan ɗaga kai ya kalli gurin amma ko alama baiga mai maganar ba, Mahaifiyarsa ce ta kalleshi ta ce, " Fahad kaga yanda ƴanmata nan suke tsinkar magwaro muma fa haka mukayi muna ƴan mata "
Jinjina kai yayi yace, " Mommy meye abin birgewa dan Allah a hawa bishiya " murmushi tayi ta ce, " Kai rainon birni ne bazaka gane ba, mu ƙarasa gurunsu Yaya " ta ƙarasa faɗa tana wucewa gaba.
Indo sai da ta kusa shanye Mangwaron ta wurgoshi tana cewa su Zulai, " Zulai ku taɓa wannan wallahi kamar Binta siga kunji zaƙin tsiya kuwa? " saukowar Mangwaro yayi dai-dai da tahowar Fahad take faɗo jikinsa, ruwan mangwaro duk ya ɓata gaban farar shaddar Fahad " Ko kaɗan su zulai basu lura mangwaro kan Fahad ya sauka ba sai ganinshi sukayi ya tsaye yana kallan bishiyar, cikin ƙasa da murya Saude ta ce.
" Sarƙa sakko kiga wani wasu ƴan Birni harda motarsu wallahi irin ta cikin shirin kallon kaset ɗin nan da muka gani a gidan kallo " Indo ta gefen wani reshe ta leƙo da kanta aikuwa tana ganinsa ta saki baki dan ganin kawun saurayin, da sauri da dirgo tana kafeshi da kallo, shi ɗinma cikin takaicin yake binta da kallo tun daga ƙafarta da babu takalmi har zuwa kayan jikinta da suke kowanne kalarsa daban, takalmanta ta dake saƙale a gwiwar hannunta ta ciro tana kaɗesu ƙurar takalmin sai baɗe fuskar Fahad take, bata ma bi ta kansa ba ko me Indo ta tuna sai kuwa ta juya aguje tana cewa.
" Jama'a kuzo wallahi ƴan wasan kwaikwaiyo ne suka sauka a gidan Maigari " su Zulai najin haka suma suka rufa mata baya saboda irin shigar da suka ga waɗannan baƙin sunzo dashi dole sai ƴan wasan kwaikwaiyo tunda agunsu suke ganin irin wannan ƙatuwar motar.
Fahad takaicin duniya ne ya isheshi yama rasa abinda zaiyi tun tuni ya nunawa Mommy bayasan zuwan ƙauyen amma ta takura masa sai gashi tashin farko ga abinda ya biyo baya, Mommy kallan ɗan nata tayi taga yanda ya kwaɓe fuska kamar zaiyi kuka ta ce.
" Sorry My Son kasan fa yaran karkara sai a hankali ba lallai ma sun lura da abinda sukayi ba, baka ji ma me suka tafi suna faÉ—a ba " yana shirin magana ya hango zugar yara sunyo caaaa sun tunkaro gurinsu suna faÉ—in, " Yau zamuga su Ali Nuhu da Adam A Zango "
_TOFA WANNAN KARAN ZAN ƘOƘARTA NAYI LITTAFIN SOYAYYA DUKDA NAYI GUDA ÆŠAYA A BAYA *TSANTSAR BUTULCI* INA MASU MUN GORIN LITTAFIN ALJANU NAKE YI🤣🤣🤣 KO ZAI BADA CITTA KUWA? ƘILA KUJI SHI DABAN DAN NI NAFI GANE LITTAFIN SU *MARWAN*👽 da *ASEELA*👹 AMMA YANXUN MA A KAFTA🤸ðŸ¼â€â™€ï¸ðŸ¤¸ðŸ¼â€â™€ï¸ðŸ¤¸ðŸ¼â€â™€ï¸ MEYE HARSASHENKU AKAN FAHAD DA INDO MAI GAYYAR JAMA'A._🤣
*ASEELA FANS YAU KU ZAN BAWA HAƘURI BANIDA CAJI*ðŸ¤
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
23&24
Mamaki ne ƙarara ya bayyana akan fuskar Fahad cikin ɓacin ran jin kalmomin da suka faɗa ya kalli Mommy yace, " What Mommy kina jin me suke faɗa kuwa? Do i look like Hausa actor? Wai wannan wanne irin ƙauye ne haka " Mommy dariya ce fal bakinta amma gudun karta ƙara tunzura ɗan nata tace, " Haba Son don't mind them na gaya maka su fa yaran ƙauye suna da tazara mai nisa tsakaninsu dana birni, So mind your Business inba haka ba su maida kai abun tsokana " tana ƙarasa faɗa ta wuce gaba ta shiga gidan Mai Gari, fuska a haɗe shima yabi bayanta saboda bashida wani zaɓi.
Da sallama suka shiga cikin gidan Maigari alokacin Mai gari na kwance abakin bishiya anyi masa shimfiÉ—a yana ramakon bacci, salamarsu su Fahad ce ta tashe shi kamar a mafarki haka ya riski muryar Æ´ar uwar tashi.
Cikin murya ya tashi zaune yana faɗin, " Yau manyan baƙi garemu haka wa nake gani kamar Mejidda? " murmushi ɗauke akan laɓɓanta ta amsa, " Yaya ba gizo bane nice nake tafe tare muke da Fahad " Juyawa yayi ya kalli Fahad dake cika yana batsewa yace, " Kai ƙaniyarka Fahad ne ya girma ya zanƙale haka? Zo nan mana kake wani raɓewa sai kace wani baƙo " Fahad yaƙen dole ya aro ya yafawa fuskarsa ya ƙarasa gefen Maigari ya zauna sannan yace, " Ina Wuni? "Maigari da kallan mamaki ya kalleshi yace, " Mejidda wai yaron nan ba shine ɗan ƙanƙanin nan da mukaje lokacin Magajiya nada tsohon ciki ba? " Kallan Fahad tayi taga yanda ya kuma tsuke fuska ta ce, " Eh shine Yaya lallai baka manta fuskarsa ba "
" Haba ya za'ayi na mantashi ja'iri muskili amma halin nashi ya ragu ko" cewar Maigari.
" Yaya ay Fahad sai abunda ya ragu dan miskili ne kaganshi nan yanxu ma wasu ƴan mata ne daga zuwanmu suka ɓata masa jiki da mangwaro " Inji Mommy.
Murmushi Maigari yayi yace, " kaga kazo a sa'a daga zuwa har ka samu matar aure " da sauri Fahad ya É—ago da kansa ya wurgawa Maigari mugun kallo.
Su Magajiya ne suka ƙaraso cikin murna suna lale marhabun da sannun da zuwa, suna zama kamar ance su kalli bakin ƙofa gaba ɗaya sai gani sukayi yara cunkushe a bakin ƙofar gidan Maigari wasu daga cikin yaran har kokawa suke, da mamaki Maigari ya kallesu ya buga musu tsawa yace.
" Kai meke tafe daku lafiya? "
Kallon kallo suka farayi a junansu daga cen baya Sahabi ya kutso ya fito gaba yace, " Allah ya taimakeka Sarƙa ce tace mana ƴan wasan kwaikwayo sun kawo ziyara gidanka shi ne muka zo ganinsu, ance harda na namiji hine muke musu da Ɗayyabu shi yace Ali Nuhu ne nikuma nasan ba mai zuwa gurinka sai Adam A Zango "
Maigari tsuke fuska yayi yace, " Kai banasan shashancin banza da wofi ku tafi ku bamu guri " Indo dake shigowa soron gidan Maigari batasan me ake ciki ba, tana shiga Lami ta ce, " Amma Sarƙa ki sake hali ashe babu wasu ƴan Wasan kwaikwayo "
Cikin jin haushin ƙaryatata da Lami tayi Indo ta shiga tsakar gidan Maigari tana faɗin, " Ke Lami angaya miki kowa maƙaryaci ne kamar ke, idan ba ƴan wasan kwaikwayo ba su waye suke zuwa a wannan hirgegiyar motar, ba gasu agefen Maigari ba ko waɗannan kece a zaune? " tunda ta fara magana kan Fahad na sunkuye a ƙasa saboda gaba ɗaya ransa yakai maƙurar ɓaci, Indo duk wannan masifar da takeyi hannunta riƙe da wani makeken Magwaro da bata jima da fara sha ba, ƙudaje sai zagayeta suke yi amma ko ajikinta.
Indo dan ganin sai ta tabbatar da gaskiyarta yasa ta ƙarasa kusa da Fahad tana cewa.
" Dan Allah Ɗan dirama ka gaya mata ziyara kuka kawowa Maigari tunda hine hugabanmu, ƙarasowar Indo gurun Fahad yasa Ƙufaje suka biyota suka kuwwa, cikin kyankyami, jin haushi da ɓacin rai Fahad ya fisgo tattararren hujabinta, aikuwa ji kake daɓass tayi zaman ƴan bori a gabansu, Indo na shirin magana Fahad ya kifeta da wani zafaffen mari cikin ƙunan rai ya fara mata magan.
" U r very stupid, ke wacce irin Dabba ce mara hankali? "
Indo kafeshi tayi fa ido tana kallonsa saboda gaba ɗaya ranta yayi mugun ɓaci, tunda take acikin Garin gangare babu wanda ya taɓa mata abinda yayi mata a yanxu, cikin jin haushinta ya tsartar da yawu gefe sannan ya miƙe tsaye ya cukwikwiye Indo acikin hijabinta ya ƙarasa bakin ƙofa, sauran yaran na ganin ya dunfarosu kowa ya ranta ana kare saboda marin da yayiwa Indo ba ƙaramin tsorasu yayi ba, sai da yaje bakin ƙofa ya wurga Indo kamar wata kaza ya juyowarsa ko ta kanta baibi ba.
Yana shigowa ya hangi butar Maigari ya ƙarasa ya ɗauka sannan ya wanke hannunsa ya koma ya zauna yana huci, kallansa Mommy tayi ta fara faɗa, " Kai Fahad maiyasa ka fiye zafin zuciya ne? ko me yarinyar nan tayi aisai kayi mata uzuri baka ganin da ƙarancin shekaru atattare dasu, wallahi abu ɗaya ne yasa ban tsawatar maka agabansu ba saboda na tabbata suka ga na maka faɗa ko ƙofar gida ka fita ka zama abun tsokana agurinsu, bare kuma ka fita zaga gari "