Sashe 17
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana hanyar shiga staff room yaji wasu ɗalibai sun ce, " Kunga Malam Jamilu da bireziya " suna gama faɗa suka kwashe da wata irin dariya,Jamilu sarai yaji abinda suka faɗa fuska a tsuke ya juyo gurinsu ya ce, " Me kuke faɗa? " Kunya ce ta kamasu haɗe da tsoro dukda sun san bashi da yawan dukan ɗalibai amma yana da matuƙar kwarjini a idon ɗalibai, cikin jin tsoro suka ce, " Babu komai Malam " fuska ba walwala ya ce, " Ku wuce Class " tun bai gama rufe baki ba suka juya sumi-sumi suka wuce, gabaɗaya Jamilu jinsa yake wani iri shi kaɗai yaji duk ya tsargu musamman yanda yaga anatayi masa dariya, cikin Staff room ya shiga gaisawa sukayi da sauran Malaman sannan ya nemi kujera ya zauna, maganganun ɗaliban nan ne suka fara dawo mai aka dudduba jikinsa ya farayi ko zai ga abinda yaji ɗaliban sunce amma ba abinda ya gani, yana nan zaune wani ɗalibi ya shigo, cikin ladabi ya tsugunna ya ce, " Malam lokaci ya shiga " gyaɗa masa kai kawai yayi, jiki ba ƙwari Jamilu ya miƙe zai nufi hanyar fita da sauri Malam Sani yayi farat ya ce, " Malam Jamilu dakata meye wannan a bayan rigarka? "
Gaban Jamilu ne ya yanke ya faɗi da sauri ya juyo ya ce, " Malam Sani wani abu ka gani? " Malam Auwalu sai a lokacin ya ɗago da kansa ya ɗagowa yayi tozali da Bra ajikin rigar Jamilu, Malam Sani tasowa yayi ya dafa kafaɗar Jamilu ya fisgemasa yaƙunanniyar Bireziyar da Indo ta manna masa, nuna masa ita yayi sannan ya ce, " Kai kuwa Malam Jamilu ya akayi haka ta faru? Saurin me kake baka lura ba har ka saƙalo da wannan tsummar abar " Jamilu zaro idanu waje yayi yana ƙarewa Bra kallo, Malam Sani miƙo masa yayi yana cewa, " Gaskiya Allah ya taimakeka da baka shiga da wannan abar ajikinka ba da na tabba sai sun saka maka suna " Jamilu ɗagata yayi cikin ƙyanƙyami cikin suɓutar baki ya furta, " Indo ce tabbas Indo ce da wannan iskancin " Malam Sani da mamaki ya ce, " Wace Indo kuma? Kana tunanin saka maka akayi " gyaɗa kai yayi yace, Ɗakina ni kaɗaine ko Baba Huwaila sai tayi kwana da kwanaki bata shiga ba bare Indo, lafiya kalau na shirya to kana ganin a ina zan samu wannan a jikina? " shiru Malam Sani yayi sannan ya ce, " To kai wacce hujja gareka da zaka ce ita ce " shiru Jamilu yayi yana jan guntun tsaki sannan yace, " Bani da wata hujja amma nasan ta yanda zan ɓullowa lamarin " Yana gama magana ya wurgar da ita agefe zai fice da sauri Malam Auwalu yace, " Dawo Malam Jamilu ka sauyawa abarnan guri, kasan halin yaran nan yanzu ɗaya na zuwa idan ya gani zai je ya gayawa sauran sai kaji sun ƙirƙiri wani zancen daban " Jamilu ƴan yatsu biyu yasa a ɗauketa wata leda ya gani a gefe a ɗauka yasa aciki ya ɗaure ya wurgar ta window, yana wurgarwa ya sa kai ya fice kai tsaye aji shida ya nufa dan gabatar musu da darasin turanci.
Lokacin da Indo ta fice daga gidan dariya take harda riƙe ciki, kai tsaye ɗiban ruwa ta tafi tana tafe tana ƴan waƙe-waƙenta har ta ƙarasa bakin rijiyar, lokacin da taje bakin rijiyar ba mutane sosai Mutum biyu ta samu agurin, gefe ta koma ta zaune kamar mutuniyar kirki haka ta tsaya a gefe har suka gama ɗiba itama taje ta ɗibata bar gurin, kai tsaye gidan Maigari ta nufa da sallama ɗauke a bakinta ta shiga babu wanda ta yiwa magana Indo ta juye ruwa acikin garwar ruwa,haka Indo ta dinga ɗiban ruwa tana kaiwa har ta kusa gamawa, a sawunta na ƙarshe harta juye zata juya ta fita Baraka ta ƙwala mata kira da Indo kamar bazata amsa ba Maigari da ya shirya tsaf ya fito ya ce, " Ke Sarƙa ba kiranki akeyi ba? " Fuska a haɗe Indo ta juye ta cewa Baraka, " Gani meye kike kirana " Baraka zuciyarta ƙal ta kalli Maigari ta ce, " Malam dama wankin kayan yaran nan ne da nawa ya taru nace ko inhaɗa mata taje bakin rijiya ta wankesu " tun kafin Maigari yayi magana Indo tace, " Ƙundun ubancen wallahi babu uban da ya isa ya sani wanki ai ni ba baiwa bace " Maigari daƙuwa ya yiwa Indo yace, " Ƙaniyarki Indo rashin kunya zakiyiwa mutane? " Baraka ce ta karɓe maganar tana cewa, " Rashin tarbiyya zata nuna mana kasan sai mutum ya samu tsatso mai kyau yake tasowa da tarbiya, ƴar iskar yarinya mara tarbiyya " Maigari na shirin tsawatarwa Baraka Indo kayi karaf ta ce, " Wallahi ni ba ƴar iska bace sai dai ke " Baraka batayi wata-wata ba ta ɗauke Indo da mari, Indo na jin zafin mari ta cukumi wuyan Baraka suka fara kokawa, Maraka ta girmewa Indo nesa ba kusa ba shiyasa ta kusa yiwa Indo dukan tsiya, jin zafin duka ne yasa Indo ta gantsarawa Baraka cizo da sauri baraka ta saki Indo cikin jin azaba.
Gabaɗaya huci suke kowanne ya galabaita, Baraka cikin kumfar baki ta cewa Indo, " Ai dama duk inda shege yake sai ya nuna hali, shiyasa duk cikin ƙauyen nan kika fita zakka kinfi kowa sheɗanci wayasan irin tsiyar da aka shuka kafin a kawoki duniya " Indo cikin jin haushi ta ce, " Nice shegiyar? " Baraka har tuntuɓen harshe take ta ce, " Ƙwarai idan kina tantama kije ki tambayi waccen tsohuwar, ki tambayeta alaƙarki da Goggo zata gaya miki yarinya kamar ƙanwar a
sheɗan daga wannan sai wannan " Jikin Indo ne yayi sanyi tana shirin magana Maigari ya rufe Baraka da faɗa, " Ke Baraka baki da hankali ne wayace ki gaya mata wannan maganar kuma..." Baraka katse shi tayi, " Malam Ƙarya nayi idan ƙarya nayi taje ta tambaya waye Ubanta? Su waye iyayenta? Dama ai tsintacciyar mage bata mage "
Indo jiki ba kwari ta juyo ta fito kai tsaye gida ta wuce tana tafe tana nazari sai yanzu wasu daga cikin maganganun mutane suke faÉ—o mata arai, sautari idan sukayi faÉ—a da wasu suna jefa mata kalmar Tsintacciyar Mage..."
Tana tafe tana hawaye har ta ƙarasa gida kamar mara laka a jika haka ta nemi bakin ƙofa ta zauna tana rafka uban tagumi, Baba Huwaila ta lura da yanayin da Indo ta shigo da shi itama gefe ta samu ta zauna ta ce, " Sannu Indo na kinji wallahi nasan wannan aikin da Maigari ya ɗebar miki ya miki yawa amma kiyi haƙuri komai lokaci ne " hawaye ne ya ƙara gangarowa Indo sanna ta kalli Baba Huwaila ta ce, " Baba Huwaila su waye Iyayena? Wane ne Babana? " Baba Huwaila jin maganar Indo tayi kamar saukar aradu, cikin duburburcewa ta ce, " Bangane ba Indo wani abu akace miki " Gyaɗa kai tayi ta ce, " Gayamun akayi kuma nasan tunda maganar ta fito akwai wata a ƙasa " Baba Huwaila dakewa tayi cikin zuciyarta tanajin ba daɗi amma gudun kar Indo ta fahimci wani abu ta ce, " Iyayenki Allah yayu musu rasuwa tun kina jaririya " Indo zuwa lokacin zuciyarta ta bushe banda wani ɗaci ba abinda take ji a zuciyarta ta cewa Baba Huwaila, " A ina dangin mahaifana suke " take wani tunani ya ziyarci zuciyar Baba Huwaila tabbas dama tasan dole wata rana allura zata tono garma shiyasa tun Goggo na da rai taso agayawa Indo matsayinta, ajiyar zuciya Baba Huwaila ta sauke sannan ta ce, " Indo ko gajiya kikayi da zama agurina shine kike mun waɗannan tambayoyin " Indo ba alamun wasa a tattare da ita ta ce, " Ko ɗaya Baba Huwaila, inasan ki gayamun tsakaninki da girman Allah su waye Iyayena kuma a ina dangin Mahaifana suke, ko da baki gayamin yanzu ba nasan duniya zata gayamun tunda a yanzu ma anfara yimun bita "
Tausayin Indo gaba ɗaya ya mamaye zuciyarta take taji hawaye na niyyar zubo mata, fakar idon Indo tayi ta goge hawayenta sannan ta ce, " Indo girman Allah yafi komai, tsakanina da Allah Indo bansan su waye Iyayenki ba bansan kuma dangin Mahaifanki ba, abinda na sani Goggo tazo dake cikin garin nan tun bakifi wata biyu ba, ita kuma Goggo ƙawata ce tun muna ƴan mata aure ne ya rabamu daga baya kuma bayan mijinta ya rasu ta dawo cikin ƙauyen nan, ta cemun ta tsinceki tun kina jaririya a bakin wata kasuwa dake cikin garin da take, kasancewar bata taɓa haihuwa ba yasa ta ɗaukeki ta sanar a gidan Maigarin garin, daga baya ta ɗauki ruƙonki ya dawo hannunta gaba ɗaya, lokacin da tazo da ke garin nan kowa yasan ke ba yarta bace saboda a shekarun Goggo ta wuce haihuwa, kuma nan garin da kike gani shine garin Iyayenmu gabaɗaya, shine babban dalilin da yasa kowa yasan ke ba jininta bace saboda duk munsan Goggo bata taɓa haihuwa ba, amma Allah ya sani Goggo tana ƙaunarki har cikin zuciyarta kamar ita ta haifeki " Baba Huwaila dakatawa tayi ta goge hawayenta ta cigaba da cewa, " Indo amma ban gaya miki wannan maganar saboda ki sawa ranki damuwa aranki ba " Indo hawayen Idanunta ta goge ta ce, " Baba Huwaila a ina dangin Goggo suke? " wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce.
A yanzu daga ni har ita ba wasu shaƙiƙanmu da suke raye kusan duk sun mutu, sai wani ɗan uwanta da yake cikin garin kaduna wanda suke ɗan maza zar shima tun shekaru biyu baya na daina jin labarinsa, dama kuma agurinta nake jin Labarinsa " Indo miƙewa tsaye tayi ta ce, " Baba Huwaila a taƙaice dai bani da kowa wanda zan nuna na ce wannan shaƙiƙina ne? "