Sashe 45
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fahad kallan tsaf ya yiwa Indo yadda ya karanci fuskarta, ya tabbatar da abinda ta faɗa ba shine abinda ta furta ba. Murmushin gefen baki yayi ya kauda kansa gefe, Mommy sai a lokacin tayi magana, "Safna dan Allah ku ƙyalemun yarinya ta sarara keda ɗanki kunsa min ita a gaba, banda aikin da ya sata sai faɗa kuke mata. Aunty Safna ta ce, "Wallahi yarinyar ce na lura nema take ta raina Fahad" Ita dai Indo wucewa tayi hanyar da Fahad ya nuna mata tana zuwa wata ƙofa ta gani, a hankali tasa hannu ta murɗa kofar ta shiga. Tana shiga wani daddaɗan ƙamshi ne ya doki hancinta har sai da ta Lumshe ido, bayan wasu ƴan sakanni ta buɗe su ta ƙarasa cikin ɗakin tana ƙarewa ɗakin kallo. A fili ta furta, "To banda Iyayi me za'a gyara anan bayan ɗakin komai ya gyare yake" Ajiye jakar tayi a gefe ta zuba wani uban tsalle ta faɗa kan katifar, kamar wata ƙaramar yarinya haka ta dinga tsalle tana watsi da kayan dake kan gadon.
Ta jima tana tsalle-tsallenta sannan ta dakko ta nufi bakin kan mudubi, tsayawa tayi tana ƙarewa kayan kai kallo, wani ɗan ƙaramin akwati ta gani da sauri ta janyoshi ta buɗe, wasu takardu ta gani buɗewa tayi amma sam bata fahimci ko takardun meye ba. A zuciyarta ta ayyana koma dai na meye tasan masu muhimmanci ne, ɗaga rigarta tayi ta soke su ta mayar da rigarta ta saki. komawa tayi ta gyara gadon da ta ɓatashi. fita tayi daga ɗakin taje ta ɗakko mofa. Lokacin da zata wuce su tafiya takr sumi sumi tana sunne kai ƙasa kamar wata ta kirki, komawa tayi ta goge iya abinda zata iya gogewa ta fice daga ɗakin zuciyarta fes, dan tasan ko a iya haka ta tsaya sai Fahad ya kusa kuka. Ballantana taci alwashin yanda ya tasota a gaba sai ta ƙure masa lamba. Lokacin da ta gama babu kowa a falon dan haka ta wuce bakin gate, lokacin Fahad ya fice daga gidan. Tana ƙarasawa bakin gate bancin Baba Maigadi ta gani, zama tayi akai lokacin ya shiga banɗaki.
Yana fitowa ya samu Indo zaune akan benci, murmushi ɗauke akan fuskarsa ya ce, "Hajiya barka da fitowa" Indo ɗan waigawa tayi sai ta tuno da yadda maigadinsu na cen Kaduna yake bata girma, acikin zuciyarta ta ce, "Wayyo Allah! Ina ma su Zaliha na kusa suga yadda nake cin karena babu babbaka" a fili kuma murmushi tayi ta ce, "Yauwa Baba, Dan Allah Baba anan unguwar a ina zan sami kifi soyayye?" Ɗan jim yayi sannan ya ce, "Gaskiya Hajiya da ƴar tafiya sai anje cen titi" kuɗi Indo ta miƙa masa tace, "Gashi na ɗari biyu nake so" juyawa yayi hagu da dama sannan ya ce, "Tuba nake Hajiya amma a ƙa'ida banine me cefane ba, Hashimu Driver ne" Indo bata damu ba ta ce, "To ina Hashimun yake?" Baba maigadi ya ce, "Baya nan sai yamma yake shigowa" ganin zata ɓata lokaci yasa ta ce, "To bari kawai naje na dawo, amma duk wanda ya tambayeka ni kace baka ga fita ta ba" Zaro ido waje yayi saboda jin kalaman Indo, yana shirin magana Indo ta zare sakata ta fice" Indo tafiya ta dinga ti har sai da ta je titi ta siyo kifinta ta dawo, kuma koda ta dawo ta samu babu wanda ya neme ta.
Lokacin da ta shiga falon sanɗa ta dinga yi kamar munafuka, wajen ɗakin Fahad ta nufa tana waige-waige. Sama-sama taji muryarsa yana waya yana cewa, "Kinsan dai nace miki ki daina kirana a waya idan har bani na nemeki ba, har yanzu abinda baki fahimta ba nifa ba maganar aure a gaba na yanzu, sai nan da ɗan wani lokaci" yana zuwa nan ya katse wayar. Ji tayi alamun ya shiga Toilet amma dan ta tabbatar sai ta fita ta zagaya ta windown ɗakin sa ta leƙa, da sauri ta koma ta tura ƙofar a hankali ta fara damƙar kifin tana wurgashi guri-guri har bakin gadonsa dan so take yana fitowa yayi arba dashi, wani kan kifi ta ɗauka ta jefa masa kan gado. A hankali ta lallaɓa ta fice daga ɗakin amma sai ta ɗan bar ƙofar ɗakin abuɗe, a bakin ƙofar ɗakinsa ma jajjefawa tayi har zuwar bakin ƙofar shiga falon, wani ta kuma ɗan damƙa a hannunta ta nufi cikin kitchen ta wurgar dasu guri-guri.
Leda da takardar kifin ta yayyaga gutsi-gutsi ta wurgata bakin kantangar da tankin gidan yake kai, da yake nan ne kawai babu wayar shocking a jiki. Da sauri ta ƙarasa bakin famfo ta wanke hannunta, tana gamawa ta shiga ɗakin da aka bata wanda shine take kwana, banɗaki ta faɗa tayi wanda ta sako wasu riga da wando fari da baƙi, rigar ta saukar mata har gwiwa sai baƙar hular da ta ɗora akanta, tayi kyau sosai dukda ba wani make up tayi a fuskarta ba. Sabuwar wayarta da aka siya mata ta ɗauka ta fito Falo a ɓangaren dianning ta samu Mommy a zaune tayi mata barka da hutawa, ta wuce kitchen kamar me ɗaukan wani abu. Tana shiga ta fito tana ya mutsa fuska ta ce, "Mommy kuna da mage a gidan nan ne?" Mommy zaro ido tayi ta ce, "Wa? Rufa mun asiri! Ni da Fahad yake tsoronta, tun ina sha'awar kiwonta har na haƙura" Indo da sauri ta fice zuwa bakin windown Fahad, maƙale murya tayi ta fara kukan mage har da ɗan irin gurnanin nan da sukeyi, musamman idan suna faɗa. da sauri taji Fahad ya buɗe ƙofa zai fita itama tayi maza ta koma ciki tana cewa Mommy, "Aikuwa wallahi Mommy inajin mage ta shigo gidan nan, ɗazu na siyo kifi fa na kai kichen wai daga zuwa wanka kinga banganshi ba, kuma gana duk gashi nan an zuzzubar a ƙasa..." Tun bata rufe baki ba suka ga Fahad ya fito daga shi sai gajeren wando, jallabiyarsa maƙale a hammata yana ihu yana cewa.
"Mommy! Mommy kina ina wallahi mage ta shigo mun ɗaki dan Allah kisa a fitar mun da ita" Indo dariya ce taso ƙwace mata amma sai ta maze ta ce, "Kai amma Yaya Fahad wallahi ka bani mamaki namiji da kai kana tsoron wata mage" harara ya watsa mata, bai tanka mata ba Mommy ta ce.
"Ashe kuwa da gaske ne yanzu fa Humaira take gayamun ta siyo kifi bata ganshi ba" da sauri Fahad ya ce, "Wallahi ta kaishi ɗakina, har kan kifi na gani a kan gadona" Wannan karan saida Indo ta murmusa sannan ta ce, "Muje ka nuna mun daga ina kaji motsinta dan ni bana tsoron wata mage" Indo ta ƙarasa faɗa tana wucewa hanyar ɗakin nata, kamar wani yaro haka Fahad yabi bayanta yanayi yana ɗan miƙa wuya gaba, suna zuwa Indo kanta tsaye ta tura ƙofar ta shiga.
Juyowa tayi ta ce, "Daga wajen ina take?" Fahad na maƙale ya nuna ɗan yatsa wajen bakin window yace, "Ta nan haka na ji kuka da motsinta"
Indo ɗan tsuke fuska tayi ta ce, "Amma fa sai ka shigo ka ɗan riƙen labulen yadda zan kamata ta ruwan sanyi" Fahad cikin sanɗa ya tako ciki har ya haye kan gadon yaja labule ya riƙe, Indo sunkuyawa tayi tana leƙa ƙasan gadon, wata uwar ƙara ta saki ta nufi bakin ƙofa, kafin ta kai ga fita taji Fahad ya fusgota gefe ya zuba a guje.
MASU COMMENTS INA GDY ILOBIYU LODI-LODI😘🥰😘😘😘😘🥰🥰
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[19/09, 18:32] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
81&82
Indo faɗuwa tayi shi kuwa Fahad tuni ya daɗe da barin gurin, kwanciya tayi tana dariya harda riƙe ciki. Sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin a guje, kamar wacce ta ga wani abun tsoro, lokacin da ta zo falo Mommy ta hango a ƙofar kitchen, Indo tsayawa tayi tana haki ta ce,"Mommy Ina Ya Fahad ne" Mommy ta ce, "Na ga ya fito da gudu yayi ɗakinki, wai magen ce ta biyoku ne? Humaira Idan bazaki iya ba ki kira Baba Maigadi ya fitar da ita." Indo ta ce, "Haba Mommy magen ce zata gagareni, muna shiga Ya Fahad ya ɓatamun shiri ta shige ƙarƙashin gado, shine ya zubo a guje." Indo ta faɗa tana bin hanyar ɗakinta.