← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 76

Sashe 65

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwan Daddy Fahda da Mahaifin Indo biyu kowanne zuwa zasuyi sai sun taho da sha tara ta arziki, hakan ba ƙaramin daɗi su Baba Huwaila suka ji ba. Satin Jamilu biyu da dawowa daga asibiti Baba Huwaila ta ce su tarkata su koma gidansu, Indo sam ba haka ta so ba dan ta sakankance a gidan Baba Huwaila, ba yadda ta iya wata ranar Juma'a Baba Huwaila da Alhaji suka shirya suka ɗauki Indo da Jamilu a mota suka wuce unguwar tukuntawa.

Jikin Fahad ya samu sauƙi sosai saidai har zuwa lokacin yana cikin damuwa, ya rame sosai ya ƙara tsayi ga wani haske da yayi sosoi, kallo ɗaya Aunty Safna tayi masa ya bata tausayi duk yadda taso Fahad ya tafi gidanta fir yaƙi, dan dole haka Mommy ta ɗauki Fahad ta wuce dashi gida. A ɓangaren Yaseer shi ɗinma kusan hakan take, tunani shine ya zama abokin hirarsa a duk lokacin da soyayyar indo ta addabeshi sai ya ɗaga waya kamar ya kirata, sai ya gargaɗi zuciyarsa akan tsoron Allah domin yasan koshi ne aka kira matarsa sai inda ƙarfinsa ya ƙare, idan haka ta faru da shi ya gwammaci ya ɗauki mota yayi ta zaga gari, Lubna lokaci-lokaci take kiransa a waya amma yawanci daga gaisuwa shikenan abinda yake haɗasu, wani lokacin ma idan ta kira baya ɗauka tun abin na damunta har ya daina damunta idan ta tuna da abinda ya faru da shi da Indo.

Lokacin da su Baba Huwaila suka raka su Indo gidansu nasiha sukayi musu mai ratsa zuciya, Indo tunda aka fara shirin tahowa ta fara ruwan hawaye haka lokacin da zasu tafi rungume Baba Huwaila tayi tana kuka, da kyar ta raba jikinta dana Indo tayi mata sallama suka tafi. Bayan sun tafi Jamilu ne ya dawo gurin Indo ya zauna cikin lallashi ya fara magana.

"Ayusher bana jin daɗin yadda kike zubda hawayenki" hannunsa ya ɗora akan fuskarta ya fara goge hawaye, ya cigaba da cewa. "Dan Allah ki daina mun asarar hawayen..." wata uwar harara ta watsa masa lokaci guda taji wani irin haushinsa ya kamata, tunowa tayi da irin lallashin da Yaseer yake mata musamma idan yaga tayi fushi, ƙamshin turarensa ne ya faɗo mata a ɗan ƙaramin ƙyallen da yake bata duk lokacin da ya kawo mata ziyara, guntsun tsaki ta saki ta miƙe ta wuce ɗakin gadonta ta banko ƙofa ta faɗa kan gado tana sakin wani irin kuka.

Shima Jamilu take yaji idanuwansa na kawo masa ƙwallah, baiyi aune ba yaji ɗigar hawayensa a kan hannunsa. Dafe zuciyarsa yayi yana cewa, "Me yasa kika mun haka meyasa zaki cutar dani? Me yasa zaki so abinda bashi yake muradinki ba? Tabbas bakimun adalci ba kin cutar dani kin yaudareni yaudara me tsananin mai matuƙar wahalarwa. Allah ka kawo mun mafita Ya Allah kana gani bani na tursasawa kaina ba, Allah ka karkato mun da hankalin matata akaina" haka ya cigaba da surutai idanunsa na zubda hawaye, duk abinda yake faɗa Indo na jinsa ko kaɗan bataji ɗigon tausayinsa ba bare taji zata iya ƙaunarsa a zuciyarta.

Sai da ya jima a zaune har yaji zuciyarsa ta ɗan zafin da take masa, tashi yayi ya fice daga gidan a lokacin har magriba ta fara kawo kai. Sai da ya gabatar da sallar magriba sannan ya biya Dadin kowa suya spot dake tsalleken titin unguwarsu, ya siyo musu kaji manya guda uku ya shiga shagon saida drinks ya siyo musu hollandia da fresh milk da sauran lemuka, hannunsa cike da ledoji ya nufa gida. Har ya kusa shiga gida ya ga wani babban provision sanin da ya yiwa Indo na shan zaƙi, yasa ya shiga shagon ya kwaso mata tarkacen alawoyi dasu chocolate, yana zuwa ƙofar gidan yasa mukuli ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, lolacin da ya shiga falon tana zaune duk tayi wani zuru-zuru da alama a tsorace take na rashin ganin dawowarsa. A cikin zuciyarsa yake mamakin yaushe Indo ta fara tsoro yarinya da take bin dare tana haura katanga, wani tunani yayi ɗayar zuciyar ta ce, "Karka manta wancen karan aida ƙuruciya akanta yanzu kuwa tasan ciwon jikinta." kauda tunanin yayi ya zaune tare da zube ledojin ya ce, "Ayusher je kitchen ki ɗauko mata plate" wasa ta cigaba da yi da watarta kamar bata ji shi ba, kallanta yayi ya ƙara maimata abinda ya faɗa sannan ta miƙe ta nufi hanyar kitchen ɗin ya bi bayanta da kallo.

Ta canja kayan da tazo da su da riga da siket ne a jikinta yanzu kuma wasu riga da siket ne ƴan kanti a jikinta, da alama basu da nauyi dan ko a gida yana daga ɗaki yanajin Baba Huwaila na mata faɗa, akan ta dinga yawaita saka atamfa a gidan mijinta dan sam Indo bata san kaya masu nauyi shiyasa yawancin kayanta dogayen riguna ne, riga da siket ɗin na roba ne masu baƙi da rashin ruwan madara ba ƙaramin kyau sukayi mata ba, sai hular lilo baƙa ta saƙa da ta sawa kanta irin mai raga-ragar nan. Ba ƙaramin kyau tayi masa ba wani irin tunani ya faɗa wanda har taje ta ɗauko baisan dawowarta ba, baisan lokacin da yayi suɓutar baki ya ce, "Ina ma tana ƙaunata" Indo taji abinda ya faɗa sarai da ƙarfi ta ajiye masa Plate ɗin dan da alama ta lura ya zurma cikin kogin tunani, a zabure ya sauke ajiyar zuciya ya sauke ya janyo ledar kajin ya turawa Indo ya ce. "Ki zuba mana" hannu tasa ta karɓa a dai-dai lokacin hannunsu ya sarƙe da juna, a kasalce ta janye hannunta ta zuba musu dai-dai wanda zasu ci ta ajiye sauran. Tana ajiyewa Jamilu ya ce, "Kai mana sauran cikin firji" Wannan karan a ɗaɗɗare ta miƙe cikin tsarguwa dan ta lura da biyu ya ƙara aikenta, dawowa tayi ta zauna ya ɗauka wata tsoka yayi bismillah tare da miƙawa Indo baki, wani kallo ta watsa masa ta ce, "Meye haka ne wai" tsuke fuska yayi ya ce, "Abinda kika gani, Malama buɗe baki ki ci ina lura dake tun jiya da akace miki zamu tare baki ci abinci ba, inaji Baba Huwaila na miki faɗan cim abinci" murguɗa baki tayi ta ce, "Bazan ci ba dole ne sai naci cikina ko naka dan Allah Malam ka rabu dani banasan..." ƴan yatsunsa biyu yasa ya ɗalle bakinta ya ce, "Kisan irin kalmomin da zaki dinga gaya mun banasan rashin kunya" idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Wai me nayi maka ne Ya Jamil meyasa ko yaushe bakasan farinciki, ka raboni da mai sona kazo zaka dinga azabtar dani wallahi sai Allah ya saka mun" Jamilu yaji ɗacin abinda ta faɗa, tsuke fuska ya ƙarayi ya ce.

"Eh naji duk abinda zaki faɗa ki faɗa amma sai kinci abinci" kamar me jira ta fashe da kuka ta ce, "Wallahi bazan ci ba banaci" a yadda yasan Indo da kafiya indai ta kafe kan abu to bazaka taɓa juya ta ba, tausasa murya yayi ya ce, "Nasan bakya sona Ayusher amma dan Allah karki azabtar da kanki da yunwa, banasan Ubangiji ya kamani da haƙƙinki" wani irin kallo tayi masa na ka raina mun hankali, cikin jin haushi ta ce, "Shiga haƙƙi na nawa? kana tunanin yanzu daka sa aka kawo nan ba haƙƙina ka shiga ba?" tana gama faɗa ta rushe da wani irin kuka.

Jikinsa ne yayi sanyi nan take nadama ta shige shi, tabbas shi zai isar da saƙon rabo da masoyi tunda ya shiga irin wannan damuwar a kwanakin da ya gabata, tausayinta ne ya kamashi ya miƙe tsaye ya taka zuwa gurin da take zaune. Ɗagota yayi yana riƙe da kafaɗunta yaja da baya ya zauna akan kujera, fuskarta ya ƙarewa kallo nan take ya rungumeta yana bubbuga bayanta kamar wata ƙaramar yarinya, jikinta banda rawa babu abinda yake yi ƙirjinta na bugawa har Jamilu na iya jiyo bugun ƙirjinta, mutsu-mutsu take tana niyyar ƙwacewa amma tsam ya riƙeta yana goge hawaye, sai da yaji ta tsagaita da kukan ya saketa ya ce. "Ayusher me kike so?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "Amma da sharaɗi sai kinci ki ƙoshi duk abinda kike so zanyi miki" Indo juyawa tayi ta kalli plate ɗin jiki ba ƙwari ta ƙarasa gurin ta tsugunna tasa hannu ta fara ci.

Murmushi Jamilu yayi ya koma ya zauna suka cigaba da ci babu mai yiwa kowa magana kamar kurame, sai da suka ci sukayi ƙat sannan ya buɗe hollandia ya miƙa mata, babu musu ta karɓa ta fara sha nan take ta shanye shi tas. Jamilu ya hira ya fara sakowa Indo amma sam fuskarta ba walwala, har ya gama maganarsa bata tanka masa ba. Suna nan zaune aka fara kiraye-karayen sallar Isha'i, miƙewa sukayi shi yayi alwala ya fice zuwa masallaci ita kuma ta ɗaura alwala ta shiga ɗaki dan gabatar da sallah.

Jamilu bayan sun idar da sallar isha'i ya samu limamin ya gabatar da kansa a gurin nan suka ƙara gaisawa tare da sauran mutanen da ke gurin , Bayan ya dawo ƙofar gidansa nan ya sa akayi masa sallama da wasu maƙotansa bayan sun gaisa duk ya gabata da kansa agurinsa, musabaha suka ƙarayi sukayi masa Allah sanya alheri tare da fatan alheri, hira suka fara yi Musa maƙocin Jamilu na hannun dama ya ce, "Ango maza wuce ka wuce amarya na jiranka mu nan duk tsofaffun hannu ne" gabaɗaya dariya suka saka Jamilu yayi musu sallama ya shiga gida, yana shiga ya sakawa gidan sakata.
Chapter 65 · 0% Book details