← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 76

Sashe 68

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mugun tashin hankali Maryam takalli sandar data tsaya a kusa da ita wasu zafafan hawaye suka zubomata lokaci ɗaya jikinta yashiga tsuma ta ɗaga kai taga kowa ita yike kalla ƙasa tayi da kanta ba zato taji muryar Sultan yace"kifito ".
saurin ɗaga kai tayi idanunta yafaɗa kan na Ummanta dake hawaye gani tayi ta ɗagamata kai alamar ta fita jiki a saluɓe ta riƙa jefa ƙafa harta isa gaban Sultan da Kiriyanu ta zube murya na rawa tace"gani".
"Jakadiya ayimata wankan madara da safe kafin isowar sarkin gobe a kawota turakata".
"toh ranka shidaÉ—e godiya take".
nan ya wuce bayan tafiyarshi Maryam ta rungume Ummanta suka fashe da matsanancin kuka mutane sauran kuyangi ko sun É—auka kukan farinciki suke hakan yasa aka watse aka barsu daga Jakadiya Khadija Ummanta cikin kuka Maryam tace"Ummah na shikenan rayuwata tagama lalacewa zanzama bani da wata daraja anrabani da Muhsin".
shafa bayanta Ummanta tayi taja hannunta suka nufi ɓangarensu sosai take kuka kamar ranta zefita sosai tabasu tausayi Ummanta da daurewa kawai takeyi ce tace"Maryam kidena kuka insha Allahu Allah zefitomana da mafita kidena kukannan insha Allahu sekin auri burin ranki".
"taya Ummah ai nikuma tawa ta ƙare wannan wacce irin masarauta ce Allah dangirmanka ka kawomun ɗauki daga wannan iftila'ih daya faɗomun".
taƙarasa zancenta tare da ƙara fashewa da matsanancin tashin hankali nansu jakadiya suka shiga lallashinta.

Washe gari tana kwance akan tabarmarta taji muryar Jakadiya tana cewa"Harira ina ganin lokaci yayi da zaki sanar da Maryam sirrin da muka daɗe muna ɓoyewa".
"a'ah Jakadiya abinda baze taɓa yiwuwaba kenan dan haka kibar zancennan".
"to ai shikenan bara na tasheta nasan masu shiryata suna can suna jira".
"toh shikenan".
Maryam dake kwance tana jinsune a zuciyarta tace"toh wannan wanna irin sirrine da ba'aso nasani dole ko nasani ".
tana cikin wannan zancen taji Jakadiya akanta tana cewa"Maryam tashi muje a shiryaki".
miƙa tayi kamar me bacci tace"toh Ummah".
nanta ta buɗe idanunta da suka ɗan kumbura saboda kuka ta miƙe tafara tafiya jiki a sanyaye har zasu fita daga ɓangarensu sega Khadijat zata shiga itakuma tsayawa Maryam tayi hawaye nabin kuncinta tace"Khadijat dan Allah abinda nikeso dake duk yadda za'ayi ki haɗu da Muhsin ki sanar dashi halin da nike ciki dukda yanzu nasan yaji".
"toh shikenan insha Allahu zan faÉ—amishi".
tafaɗa tana hawaye saurin yin gaba Maryam tayi saboda kukan daya tahomata suka nufi wani ɓangare.

Wani ƙayataccen ɓangare aka kaita wanda yagaji da haɗuwa suna shiga Kuyangin da zasu shiryata suna shiga Jakadiya ta umarcesu dasu shiryata zataje ta dawo nan ta tafi sukuma suka shiga haɗa ruwan wanka kala-kala na alfarma tashiga tayo wanka tana fitowa suka ƙara haɗamata wani ruwan seda tayi wanka biyar sannan tana fitowa aka bata wani haɗaɗɗen turaren busar da laima ta shafa sannan suka shafeta da mayuka sannan aka shiga tsaramata kwalliya aka sakamata wasu tsadaddun kaya na alfarma sannan aka mayarmata da wata farar alkyabba me ratsin ja wata Kuyanga tace"ranki shidaɗe kalli kanki a madubi".
ɗagakai Maryam tayi taga lokaci ɗaya ta canza kamar ba ita dukda tana cikin ɓacin rai hakan be hanata ganin mugun kyan da tayiba tashiga duniyar tinani Jakadiya ta shigo riƙe baki tayi tare da ƙarasawa inda take tace"kai Masha Allah ɗiyata kinga yadda kikayi kyau kuwa".
wasu hawayene suka zubowa Maryam dafata Jakadiya tayi tare da cewa"haba ɗiyata karki ɓata kwalliyarman kitaso mutafi".
tafaɗa tare da sharemata fuska da tissue Maryam data zama kamar kurmace ta miƙe Jakadiya ta kama hannunta suka nufi ɓangaren dayafi kowanne kyau a cikin masarautar dukda tana cikin ɓacin rai haka taita bin guraren da kallo har suka isa bakin wata katafariyar ƙofa datafi kowacce kyau a ƙofofin da suka wuce suna niyyar shiga aka busa alkyabbar shigowar Aliyu gadanga ƙusar yaƙi masarautar .

Lokaci ɗaya gaban Maryam yayi wata muguwar faɗuwa Ashraf na niyyar fitowa suna niyyar shiga wuceshi sukayi binsu yayi da wani shu'umin kallo tare da lace leɓensa kamar baƙin maye yace!!!!!!!

*Dan Allah idan kin karanta ki daure ki tayani share fisabilillwh badon niba.*

Votes and Comments
Plz share

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_✍️
[02/10, 19:40] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_Ina masoyan Real eeshow na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna *KARAGAR MULKI* cikin farashi mafi sauƙi #300 ta wannan account number 2411022356 aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko transfer credit Mtn ko Airtel ta wa'innan numbers ɗin 08108362334 & 08087971440 sena jiku._

97&98

Ido É—aya ya kashe mata ta murtuke fuska ta ce, "Ka bari pls bana so, Yauwa game da abinda ka tambayeni ne" Murmushi yayi ya ce, "Ok, wai tambayar da nayi miki? Ai baki bani amsa ba me kike so nayi miki?" Indo kanta tsaye ta ce, "Kawai ka sakeni" ta faÉ—a batare da wata damuwa ba.

Kallanta yayi yaga ko a jikinta har zuciyarsa yaji ba daÉ—i sai ya danne ya ce, "Haka kike so?" da sauri ta amsa da, "Eh! Shikenan" ya jefo mata tambaya, "Saboda bakya sona ko?" shiru tayi bata bashi amsa ba.

Ya kuma cewa, "Idan na sakeki wa zaki aura Yaseer ko Fahad" idanunta ne suka ciko da ƙwallah bata bashi amsa ba ya ce,"Yanzu yaushe kike so na sakeki" a zabure ta miƙe zaune ta ce, "Ko yanxu ma"

Ƙura mata ido yayi yana kallonta kamar bazai magana ba sannan yace, "Ayusher idan na sakeki a yanzu kina ganin na miki adalci, ashe ƙiyayyar da kike mun har ta kai haka? Nasan Yaseer kike so amma bantaɓa tunanin zaki nemi saki da kanki ba tunda Allah S.W.A ya haramta haka"jikin Indo ne yayi sanyi bata ce dashi uffan ba ya cigaba da cewa, "Amma ba damuwa ki bari akwai lokacin zan ɗiba wanda zan baki takardarki, wannan kawai kike so?" shiru Indo tayi batare da ta furta masa komai ba, daga haka juya mata baya yayi, ya fara karanto addu'o'in kwanciya bacci, Indo itama gyara kwanciya tayi ta kwanta sai dai gabaɗaya kowa da abinda yake saƙawa zuciyarsa, daga haka kuma bacci yayi awon gaba dasu.

Washegari da safe Jamilu ne ya fara tashi ya haɗa musu breakfast, sai kusan ƙarfe tara Indo ta tashi kai tsaye banɗaki ta faɗa tayi wanka sannan ta shiryo cikin doguwar rigar atamfa Ja, ba wata kwalliya tayi ba amma ba ƙaramin karɓarta atamfar tayi ba. Lokacin data fito falo a lokacin shima ya shigo daga shi sai t-shirt da gajeren wando, Indo basarwa tayi kamar bata ganshi ba ƙamshi take jiyowa daga kitchen tana nan zaune ya ji ya kwaso musu kayan karin kumallo, wayarta ta ɗauka ta shiga whatspp tana duba saƙwannin da suke shigo mata, duk lokacin data buɗe data sai ta dinga baza ido ko zata ci karo da saƙon Yaseer amma ko makamancinsa babu, kashe datar tayi ta shiga cikin lambar Yaseer tun daga farkon tsohon chart ɗinsu take karantawa, sai zabg murmushi take hankalinta yayi nisa sosai, lokacin da Jamilu ya gama kawo musu kayan karin su shayi ya haɗa musu sannan ya ce, "Ayusher ba gaisuwa?" sam bata sanma yanayi ba hankalinta yayi nisa sai da ya ƙara maimaitawa amma ko gezau bata motsa ba, a shammace ya fisgi wayarta ya ce, "Wai wane irin wulakanci ne ina magana kina jina?" yana gama faɗa ya sauke idanunsa akan wayarta yaci karo da wani saƙon Yaseer da ya ce, "I really miss u dear ko bacci bana iya yi sai naji sautin muryarki" Ƙirjin Jamilu ne ya buga ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, wani irin kallo ya watsawa Indo ita kuwa ko ajikinta ta ce, "Malam ka bani wayata" wata razananniyar tsawa ya daka mata yace, "Bazan baki ba, Uban waye ya baki damar yin hira da wani banza kina ɗauke da aurena akanki" haushi ne ya kamata a hassale ta ce, "Ya Yaseer ɗinne banza wallahi karka ƙara gaya masa haka..." a hargitse ya katse ta, "Na gaya masa daga yau sai yau na kuma ganin wayar a hannunki" yana rufe baki ya buga wayar akan tayals lokaci ɗaya wayar tayi kwatsa-kwatsa ta tarwatse, wani irin abu ne ya soki zuciyar Indo take ta fashe da kuka tana faɗin, "Allah ya isa wallahi kuma bana sanka bana ƙaunarka wallahi sai ka sakeni mugu azzalumi kawai" Kan kujera Jamilu ya koma ya zauna ya dafe kansa wanda yake sara masa kamar zai tsage gida biyu, wani irin zafi yake ji a zuciyarsa ga wani irin jiri da yake neman ɗibansa.

Indo na shiga ɗaki ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta fara haɗa kaya a gaggauce cikin ƙaramar trolly ɗinta, tana gama haɗawa ta janyo abarta fuskarta ta yi jawur saboda kukan da ta sha. Lokacin da fito Falo yana zaune a inda ta barshi harta zo tsakiyar falon binta yayi da kallo bai tanka mata ba dan yaga iya gudun ruwanta, kai tsaye wucewa tayi ta buɗe ƙofar ta fita harabar gidan da sauri yabi bayanta, yana zuwa ya fisgo hannunta yace, "Ke wai me yake damunki ne, meye haka zakiyi?" cikin zafin zuciya ta ce, "Ina ruwanka da duk ma abinda zanyi ka sake ni Malam infita wallahi bazan zauna ba" ta faɗa tana fisge hannunta tayi gaba.
Chapter 68 · 0% Book details