← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 76

Sashe 52

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad bakinsa sai motsi yake kamar zai tari kawun nasa da tambaya, amma sai ya danne ya juya kai gefe. Jamilu jiki a sanyaye ya ce, "Abba in sha Allah zanyi bakin ƙoƙarina wajen ganin na riƙe wannan amana taka, dukda bansan wacce irin amana bace." Alhaji Khaleel ya ce, "Na buɗe sabon kamfanina a garin Kano, kamfanin leda ne da takalma shiyasa na yanke shawarar damƙa maka amanar sa, saboda da Kawunka zan damƙawa amma sai ya nuna mun gwara na sameka tunda shi baiyi zurfi a karatu ba, dan yana gudun kar a samu matsala dan haka kai zan mallakawa ragamarsa amma bansani ba zaka amince kuwa saboda kaima ma'aikaci ne, banasan na shiga haƙƙinka idan kana ganin babu damuwa.Karka ji kunyata idan har da takura ka mun bayani" Wata gwauruwar ajiyar zuciya Fahad ya sauke har sai da ta fito fili, Alhaji Khaleel murmushi yayi saboda ya fahimci sarai inda Fahad ya dosa, Jamila gyara zama yayi ya ce, "Abba ina matuƙar godiya da wannan karamci agareni, kuma insha Allah ba abinda zai gagara Allah ya sa albarka ya taya mu riƙo" gabaɗaya suka amsa da Ameen, sai lokacin Fahad yayi murmushi ya ce, "Malam Jamilu ina taya murna Allah ya taya riƙo" Jamilu ya amsa cikin sakin fuska, bayanin yadda abubuwan suke ya ɗan fara yiwa Jamilu yadda zai gane, sannan suka ɗan taɓa hira daga nan kowa ya kama gabansa.

Washegari Jamilu ya koma sai dai gabaɗaya baiso ba ji yake kamar ya tafi ya bar wani ɓangare na jikinshi, ita kanta Indo taji ba daɗi saboda ba ƙaramin shaƙuwa sukayi da Jamilu ba, dukda dai kafin ya tafinma sai da sukayi faɗa ita, dalilin Faɗansu kuwa. Jamilu na zaune a harabar gidan Indo ta fito da wani kofi, cike yake da ƙanƙara. Kujera ta janyo ta zauna ta fara sha, Jamilu kallan kofin ya yi ya ce, "Ayusher me yasa bakyaji ne" Indo kauda kai gefe tayi ta ce, "Wallahi dama nasan sai ka yi magana, wai kai Ya Jamil meyesa bakasan duk wani abu da zanji daɗi?" Jamilu tamke fuska yayi ya ce, "Har yanzu bakida da kunya ko?" Harara ta watsa masa tana juya idanu haɗe da murguɗa ta ce, "Rashin kunya nayi maka sai dai in tsarguwa kayi..." kafin ta ƙarasa Jamilu ya bige bakin ya ce, "Inajin kafin na tafi sai na fasa wannan bakin naki, dan naga har yanzu hankalinki da saura" Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi Ya Jamil da hankali na, idan ma banida shi ai sai idan a gurinka na koya..." da sauri ya kuma bige mata baki wannan karan ba ƙaramin zafi taji ba, hawayen da take maƙalewa ne ya sauko tashi tayi sai da tayi nisa da shi ta juyo ta ce, "Wallahi banyafe ba mugu kuma sai na gayawa Baba Huwaila" tana gama faɗa ta zuba da gudu.

Jamilu murmushi ya yi a fili ya ce, "Wato Sarƙa har kwanan gobe Sarƙa ce, bazata taɓa sake hali ba. Rashin kunyar nan na nan."

Lokacin da Jamilu yaje gida ba ƙaramin daɗi Baba Huwaila taji ba, kiran Mahaifin Indo sukayi suna yi masa godiya, har akan tagomashi da ya haɗowa Jamilu da zai tafi. Ba ƙaramin kyautata musu yake ba dan kayan abinci kafin wannan ya ƙare zai turawa Jamilu kuɗi a sayi wani.

Bayan wasu ƴan kwanaki an buɗe kamfani cikin ƙudurar Ubangiji komai ya fara tafiya yadda ya kamata. Mahaifin Indo mota ya bawa Jamilu ƴar madaidaiciya ma kyau, kuma dikda wannan cigaba da Jamilu ya samu bai bar aikin koyarwarsa ba, Zumunci mai ƙarfi ne ya shiga tsakanin waɗannan gidajen guda biyu.

Indo sun fara jarrabawar Waec ana ta shirin Candy kuma a shekarar ne zasuyi saukar Alkur'ani, Indo ta ƙara zama budurwa ta kuma wayewa kamar ba ita ba. Sai dai akace idan ka shekara dubu baka ga mutum ba, idan kun haɗu tambayeshi wani abun ba halinsa ba, halin Indo na tsokona da abinda ba'a rasa ba yana nan.Yanzu a cikin dangin Mahaifi da mahaifiyarta babu Wanda bai santa ba, sai dai ba kowa ta cika shiga sabgarsa ba, saboda har a lokacin gani take ita ba ƴar wasu bace, dukda tana ƙaunar iyayenta amma har lokacin tafi jin kanta kamar yadda take ada ƴar ƙauye, shiyasa bata cika shiga sabgar cousin ɗinta na dangin Mahaifinta ba, saboda ta lura wasu daga cikinsu suna da ɗaga kai, musamman ƴan ɗakin su Lubna.

Wasu Ƴaƴan abokin mahaifinta mutum biyu ne suka nuna suna santa, amma sam basu kwanta mata ba, da suka matsa mata sai ta ce sai tayi candy ko zata fara kula samari. A ɓangarenta da Yaseer kuwa ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, kusan duk dangin kowa yasan da shaƙuwarsu, dan ita kanta Indo ta yarda son Yaseer yayi nisa a zuciyarta.Sai dai har zuwa wannan lokacin bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba, hakan ne yasa itama Indo take nuna kamar bata fahimci inda ya dosa ba, A ɓangaren Jamilu shima ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, sai dai ko kaɗan Indo bata tsammanin soyayya daga gurinsa, tafi danganta hakan da shaƙuwa. Kuma Jamilu ya barwa zuciyarsa akan sai Indo tayi Candy koda zai sanar mata da kalmar soyayya, dan idan ya tuna abinda zai sanar mata gabansa har faɗuwa yake, saboda Alasan abokinsa ya taɓa tarar ta tun a ƙauye yace yana santa, tun daga ranar Indo ta daina ganin mutumcin shi sai ma ta koma ce masa Ɗan iska. Shi kansa Yaseer wanan hukuncin ya yanke, na sai Indo ta yi Candy zai sanar da Ita, kuma ya gabatarwa da manyansu maganar aurensu. Fahad a har kullin yanasan nunawa Indo kulawar da zata fahimci yana ƙaunarta, amma wani tsagi na zuciyarsa na ƙaryata wannan tunanin, kuma yana ganin kamar raini ne zai ƙara samun gurbin zama a tsakaninsu, tunda dama tuni Indo ta riga da ta raina shi.

Wata mata na gani a cikin duhun bishiyoyi, fuskarta ɗauke da niƙab. A gaggauce ta ce, "Hadari da kyar na samu lambarka, dan Allah aikin wata yarinya zan baka, akwai adireshin gidansu dana makarantarsu a jikin takardar, banasan a samu matsala kawai ku kashe ta. Na turo muku Million biyu dan Allah banasan a samu matsala." Hadari ƙarɓa yayi yana murmushi ya ce, "Baki da damuwa Hadari baya jagwal, ki baza kunne nan da ƴan awanni zakiji sanarwar mutuwarta." da sauri ta bar gurin saboda batasan ta samu matsala.

Su Indo sun fito daga makaranta Direbansu ta hango, da sauri ta ƙarasa tana yiwa ƙawayenta sallama. Tana shiga mota wasu mutane da ke cikin wata baƙar mota suka rufawa motar su Indo baya, sai da suka fara barin cikin mutane waɗannan mutanen suka sha gaban motar su Indo. cikin tashin hankali Direban motar yake bin motar da kallo, Indo jikinta banda rawa babu abinda yake yi, mutum biyu ne suka fito daga motar hannunsu ɗauke da bindiga. cikin fargaba direban ya ce, "Humaira ya zamu yi?" Indo tace, "Mu gudu kawai, bani wayarka na kira Daddy." bata rufe baki ba suka ɗaga bindiga sama suna sakin harbi. Wayarsa babbar ya ɗauko ya miƙowa Indo, sai dai kash tana kira babu kuɗi a ciki. Da sauri ta miƙa masa cikin kiɗima ta ce, "Ba kuɗi musty, ba kuɗi" ƙaramar wayarsa me madanne ya miƙa mata, wanda alokacin tuni har sun ƙaraso wajen motar su Indo. Da sauri ta danna lambar Mahaifinta wanda yayi daidai da buɗe murfin ƙofar, da sauri indo ta tura wayar cikin aljihun wandon uniform ɗinta.

Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya fisgo Indo yana kifeta da mari, da sauri Musty ya fito ya fara roƙonsu, wanda yayi dai-dai da ɗaukan wayar da Alhaji Khalil yayi, kiran da Indo tayi masa.

"Dan Allah maigida kuyi haƙuri kuyi mana rai" Mutumin da baka ganin komai a fuskarsa, sai ƙwayar idonsa ya ce, "Ɗan samari ba gurinka muka zo ba, mun zo ɗaukan wannan yarinyar ne" Jin maganar nan ba ƙaramin ɗaga hankali su yayi ba, Musty ya ce, "Dan Allah ku haɗa dani dan idan na koma bansan me zan cewa mahaifinta ba, wallahi bazan taɓa fita ba. Idan kuma kuɗi kuke so ko nawa ne Alhaji zai bayar..."Tun bai rufe baki ba mutumin ya sakar masa harbi a ƙafa yace, "Ga shaida nan na bar masa dan na rage masa wahalar nema, dan idan ba'a ganku ba gabaɗaya ɗauka za'ayi tana raye mukuma kwangilar kisa aka bamu" yana gama faɗa ya fisgi hannun Indo tana ihu, Musty durƙushe yake yana ɗaga hannu alamun a taimaka masa, yana ji yana gani suka tasa ƙeyar Indo a mota suka tafi da ita.

Musty na nan wani me mashin yazo wucewa ya ganshi tsugunne cikin jini, da sauri ya ƙarasa gunshi dan ganin halin da yake ciki, Musty hanya ya dinga nuna masa yana cewa, "Ka taimaka sun tafi da ita" mutumin tambayarsa ya yi, a take Musty ya bashi labarin abinda ya faru, taimaka masa yayi ya sashi a mota, sannan ya fita cen gurin mutane yayi yekuwar mutane suka taho suka ɗaukeshi suka wuce da shi asibiti.

Alhaji Khalil duk abinda yake faruwa akan kunnensa, sakamakon kiran da Indo tayi masa da wayar Musty bata katse ba. Jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali, kiran wayar yake amma ba'a ɗauka ba. Da sauri ya kira Lambar Director ɗin makarantar su Indo, dan tsammaninsa a makaranta ne abinda ya faru. Saboda ruɗewa ya manta da lambar Musty ce aka kirashi, amma yana kiran Director ya shaida masa tuni ɗalibai sun jima da tafiya. Da sauri ya katse ya kira lambar kwamishinan ƴan sanda ya sanar da shi halin da ake ciki, Kwamishina cewa yayi ya tura masa lambar da aka kirashi da ita, zasu bibiyu sahun gurin da suke. Alhaji Khalil tura masa lambar yayi sannan ya fita daga cikin office ɗinsa, ya nufi ofishin Kwamishina dan ƙara jaddada masa. Gudu yake kamar zai tashi sama har a ƙarasa, lokacin da yaje tuni har sun fara tracking ɗin lambar kuma sun tura jami'ansu suna bibiyar sahun makasan da suka tafi da Indo.
Chapter 52 · 0% Book details