← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 76

Sashe 20

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da suka shiga gidan shiru ba wani ɗaki ta buɗe mata ta ce, " Shiga kafin na dawo " Indo a hankali ta taka ta shiga jiki ba kwari ga wani irin ciwo da kanta yake mata, guri ta samu ta zauna tana ƙarewa falon kallo, ba laifi Falon ya ƙayatu ga wasu luntsuma-luntsuman kujeru, bayan fitar Dear daga wata ƙofa taji anturo ƙofa anfito, wata mata ta hango mai jiki ta nufo gurinta, itama matar da mamaki take kallan Indo har ta ƙaraso gurinta ta zauna kan kujera, kallan Indo tayi taga yanda fuskarta da alamaun jini, dubanta ta ƙarayi da kyau sannan ta ce, " Yarinya sannu kinji " Indo gyaɗa kai tayi ta kuma sunkunyar da kanta ƙasa, kallan matar tayi taga kamar ta santa tunowa tayi da inda suka haɗu,cikin zuciyarta ta tuno itace matar nan da taji wannan matashiyar budurwa na cewa Aunty, suna nan zaune sukaji anturo ƙofa anshigo.Da murna matar nan ta fara magana, " Oyoyo oyoyo, barka da zuwa mutanen Kaduna, Matar Minista kece tafe da daren nan? " cen gefen matar ta zauna tana ajiye katuwar jakarta, ɗora kafaɗarta tayi akan ta matar sannan ta ce, " Wallahi Aunty munso dawowa da wuri so sai wani uzuri ya tsaida Nasir " kallonta ta ƙarayi tace, " Tun safe nake sa ran ganinki naji shiru har na fidda rai, Matar minista kinga yanda kikayi shar kuwa? " murmushin jindaɗi tayi suka cigaba da hira dan sam sun manta da wata Indo dake gefe a zaune, Matar minista ce ta ce, " Aunty muna tafe mun kusa ƙarasowa mun bige yarinyar cen amma naga jinin ya daina zuba, ko zuwa safiya akaita asibiti " Aunty leƙawa tayi tana kallan Indo tana tunanin inda tasan fuskarta, cikin muryar tausayi ta ce, " Allah sarki Allah ya kaimu, gata very young and she is so cute ƴan mata ya sunanki? " Indo ta ce, " Suna na Indo " kallan juna sukayi suka tuntsire da dariya sannan matar tace, " Wane irin wani Indo ana zaune ƙalau, daga yanzu duk wanda ya ƙara tambayarki kice sunanki Humaira " wannan karanma Indo gyaɗa kai tayi, Aunty tashi tayi tace, " Bari na ɗora miki ruwan wanka kiyi wanka ki kwanta zuwa safiya musan abinyi, ni sai nake ganin kamar nasan fuskarki ma " Indo ta ce, " Ɗazu tare da ku muka hau Adaidaita sahu " Da Aunty ta juyo ta ce, " Tabbas anyi haka " tana gama faɗa tayi gaba, da ƙarfi matar minista ta ce, " Aunty nima ki ɗora dani dan jikina gaba ɗaya ciwo yake saboda gajiya " tana gama magana ta tashi ta ɗauki jakarta ta shige wani wani ɗaki aka bar Indo zaune tana mamakin mutumci da karramawar waɗannan bayin Allah.

Ba'a ɗauki lokaci ba Aunty ta dawo cikin falon ta koma mazauninta na da ta zauna tana ƙarewa Indo kallo, acikin zuciyarta take yaba kyawun fuska da kwantaccen gashinta irin na fulani, bayan wani lokaci matar minista ce ta fito taje ta juye ruwan wanka ta faɗa toilet,bata jima ba ta fito ta wuce su Indo, Aunty ce ta juyewa Indo ruwan wanka da kanta ta kamo hannun Indo ta rakata har banɗaki sannan ta juyo, Indo a hanakali rake komai saboda har zuwa lokacin kanta banda sarawa ba abinda yakeyi, itama bata jima ba tayi wanka ta fito tana tafe tana dafa kanta.
Ruƙota Aunty tayi ta wuce da ita cen ɗakinta wata ƴar doguwar riga mara nauyi ta ɗaukowa Indo ta miƙa mata sannan ta ce," Ki saka wannan ki cire na jikinki idan kin gama ki fito falo sai ciki abinci kisha ko Paracetamol ne " Indo amsa mata tayi sannan Aunty ta fito, ba'a jima ba Indo ta sa doguwar rigar ta fito ta koma gurin da ta zauna da farko ta rakuɓe, a dai-dai lokacin Aunty ta shigo hannunta ɗauke da kofun Tea ɗayan hannunta farfesun kayan ciki ne acikin plate, cen tsakiyar Falon Aunty ta kai mata ta ce, " Humaira taso ga abinci ki saki jikinki kamar nan gidanku ne, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki kinji? " Indo tasowa tayi ta ce, " To Aunty nagode Allah saka da alheri " Aunty gyaɗa kai tayi tana murmushi, biredi ta miƙowa Indo sannan ta wuce cikin ɗakinta, Indo zama tayi ta fara cin abinci sai da taci tayi ƙat ta ƙoshi sannan ta kwashe kayan ta kai, hanyar da taga Aunty ta shigo da kayan abincin nan ta bi ta shiga cikin kitchen ta ajiye ta dawo ta koma ta zauna, dawowarta ba da jimawa ba Aunty ta shigo da magani ta bawa Indo da ruwa ta shanye, Aunty juyawa tayi ta koma ɗaki ta ɗan jima kafin ta fito har indo ta fara gyangyaɗi, tashinta tayi suka shiga ɗakinta.

Katifu ne manya guda biyu ɗakin banda zabga ƙamshi babu abinda yakeyi, ɗaya daga ciki Aunty ta nunawa Indo ita kuma ta haye guda ɗaya, Indo katifar ta hau tana mamakin taushi da laushin wannan katifa, kwanciya tayi babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita duba da yanayin gajiyar da tasha awunin ranar, bargo Aunty taja ta rufe Indo saboda yanda taga Indo ta takure guri ɗaya da alama sanyin AC ne yayi mata yawa, Aunty ta jima akan Indo tana murmushi ita kaɗai tasan abinda take ayyanawa game da Indo, hannu tasa ta shafi fuskarta tana shafa cukurkuɗaɗɗen kitson Indo da har tsagarsa ta haɗe, afili ta furta, " Yarinya nan idan ta goge sai tafi su Preety kawo haske " komawa tayi ta kwanta itama ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.

WASHEGARI
Tun da asuba Indo ta fara ganin ƴan mata kala-kala kyawawa dasu, azuciyarta take mamakin duk yawansu ace ƴaƴan Aunty ne, bayan tayi sallah bacci ta ƙara komawa ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe.Indo na fitowa taga kusan ƴan mata biyar zaune a falo tana shigowa har ƙasa Indo ta tsugunna ta ce, " Ina kwananku? " kallan junansu sukayi lokaci guda suka kwashe da dariya wasu daga cikinsu har suna tafawa, Matar Minista ce ta fito a lokacin itama kan kujera ra samu ta zauna, Indo ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma sai ta basar ta juya ta gaida matar minista, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa tana mata ya jiki, Ƴar ƙwai ce ta kalli matar minista ta ce, " Matar minista saukar yaushe kefa kamar fataken dare haka kike " Wayarta ta ɗauka tana dannawa sannan ta ce, " Kjiya muka sauka lokacin duk kunyi bacci, kuma ni kinsan bana harkar ƙananan ƙwari " taɓe baki ƴar ƙwai tayi tace, " Ko tare kuke da magen? " Sanin rainin hankalin ƴan gidan yasa ƴar minista ta tsuke fuska ta ce, " Eh tare muke kuma bance kowacce yarinya ta taka ta ba " sanin halin matar minista yasa ba wanda ya tanka mata kowa ya cigaba da harkar gabansa, Aunty ce ta haɗo musu breakfast suka cikin girmamawa Indo ta gaida Aunty, fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana mata ya jiki.

HaÉ—uwa sukayi suka karya sannan sukayi wanka, matar minista da Aunty ne suka kai Indo wani private hospital dake Zoo raod, É—inki akayiwa Indo a goshinta danma bataji wani ciwo sosai ba sai magunguna da aka bata sannan aka basu wasu Æ´an dokoki da zata bi domin samun É—orewar lafiyarta, tun bayan da suka dawo Indo ba abinda takeyi daga wanka sai dai taci abinci tasha magani ta kwanta.
Cikin abinda baifi sati guda ba Indo ta murje tayi haske har wata ƙiba tayi ga wuyanta wasu garaye da suka fito mata, abu ɗaya ne yake damunta kullin idan ta cewa Aunty zata tafi sai tace mata tayi haƙuri ta zauna jikinta ya ƙara samun sauƙi, Indo ba ƙaramin damuwa ta shiga ba ga wasu ɗabi'u data fuskanta daga ƴan matan gidan, idan wannan tayi tafiya sai tafi kwana uku ko huɗu bata dawo ba kuma Aunty ba abinda take ce musu sai ma addu'a fatan alheri da take musu.
Chapter 20 · 0% Book details