← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 76

Sashe 21

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Satin Indo Biyu ta ɗauketa ta kaita saloon aka gyara mata kai da wankin ƙafa, daga nan kasuwa suka shiga ta lodowa Indo atamfofi da leshina a ƙalla sunfi kala goma, kai tsaye shagon telansu da yake musu ɗinki ta kai masa tana yi masa bayanin ɗinkin Indo, kallanta kawai yayi ya fahimci size ɗin Indo daga nan gida suka wuce agajiye saboda yanda suka sha tafiya.
Bayan kwana biyu suna zaune gidan ba kowa daga Aunty sai Indo kayan ɗinkin da aka amso mata ta ɗauko ta miƙawa Indo ta ce, " Humaira yau zamuyi baƙi inasan kije kisa kayan nan dan baƙin suna hanya sun kusa ƙarasowa banasan suzo su ganki ba gyara, Indo zuciyarta ɗaya taje tayi wanka ta saka kayan da Aunty ta bata riga da sike ɗin leshi ne orange mai ratsin green, kayan ba ƙaramin karɓarta sukayi ba, ita kanta da ta kalli kanta a mudubi sai da tayi mamakin kyaun da tayi, Aunty ce ta gyara mata kai ta tazo mata gashinta har gadon baya sannan ta ɗaura mata ɗan kwali, masha Allah duk wanda yasan Indo abaya da zai ganta da kyar zai ganeta, ta gama shiryawa kenan sukaji sallama anshiga cikin gidan, fuskar Aunty wasai ta amsa tana musu barka da zuwa tana musu iso cikin falo, Maza ne guda biyu baza'a kirasu da dattawa ba kuma baza'a kirasu da yara matasa ba, aƙallah zasuyi shekara Arba'in zuwa Arba'in da biyar ba, zama sukayi suka gaisa da Aunty sannan ta fita cen ɗakin da Indo take ta ɗebo drinks ta bata sannan ta ce, " Ungo ki shiga ki kai musu kuma bance ki tsugunna har ƙasa ki gaishesu ba akan kujera zaki zauna sannan kice ina wuninku, idan kuma sun tambayeki sunanki kice sunanki Humaira banasan gidadanci, wannan da kike gani na gaban da ya fara wuce ciki Honourable ne ba ƙaramin alheri zaki samu nima naci arziƙi ba, wuce ki tafi ba daga shigarki zaki taso ki fito ba " Indo karɓa tayi har ta yo gaba ta juyo ta ce, " Aunty Ina mayafina " Aunty harara ta watsa mata ta ce, " Wuce ni ki tafi acikin gidan har wani mayafi zaki yafa " Indo gaba tayi ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, ajiye musu tayi ta koma kan kujera kamar yanda Aunty ta gaya mata, ganin girman mutanen yasa ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, " Ina wuninku? " muryar Indo ba ƙaramin ratsa tsakiyar kansa tayi ba, kasa amsawa yayi sai ɗayan da suke tare ne ya amsa mata jin muryar mutum ɗaya ya amsa ya sa Indo da kanta karaf suka haɗa ido, ƙara ɗauke kanta ƙasa tayi tana wasa da ƴan yatsunta.
Ajiyar zuciya Honourable yayi sannan ya ce, " Cutie ya sunanki " Indo batasan me yake nufi ba da farko bata zaci da ita yake ba sai da ta ɗan ɗago taga ita yake kallon sannan tace, " Sunana Humaira " runtse idanunsa yayi tunda yake bai taɓa haɗuwa da yarinya da muryarta take masa amsa kuwwa kamar yarinyar nan, ƙara lumshe idanu yayi ya ce, " Humcy sunanki yamun daɗi " Indo shiru tayi bata ce Uffan ba sun ɗan jima a haka sannan Aunty ta shigo tana shigowa Indo ta tashi ta fita, Honourable kallan Aunty yayi ya ce, " Hajiya ina kika samo yarinyar kamar wannan " dariya Auntua tayi ta ce, " Haba Honourable aini gidan nan duk kalar da kake so ina da ita " Honourable sunkuyowa yayi ya ce, " Amma naga yarinyar kamar tana da kunya ko farin shiga ce? " Itama ƙasa tayi da murya ta ce," Ɗanya shakaf ce fa batafi shekara goma sha uku zuwa sha biyar ba "

Honourable dariya yayi ya ce, " Irinsu nake so amma wannan da ita zan tafi dama zuwa yamma nake san tafiya Abuja ina sa wani meeting kwana biyu ne kawai zamuyi " Aunty daɗi taji har cikin ranta amma sai ta basar ta ce, " A'a Honourable yarinyar nan fa farin shiga ce " Honourable hannu yasa a aljihu ya ciro bandir biyu na ƴan dubu-dubu sannan yace, " Ai so nake a barmun ita ta zama tawa ce ni kaɗai, ga wannan ayi cefane dasu " Dubu ɗari biyu ya ajiyewa Aunty ya miƙe tsaye yace, " Hajiya ta fito yanzu kawai mu wuce dan bani da enough time " gaba ya wuce Abokin tafiyarsa na take masa baya, Aunty daɗi taji kamar ta buga tsalle, ɗakin da Indo take ta shiga wata ƴar ƙaramar akwati ta ɗauko ta miƙawa Indo tace ungo wuce maza zakiyiwa Alhaji rakiya Abuja zaku tafi saura kiyi masa gardama duk abinda ya umarceki kiyi masa kinji me nace miki? " Indo fuska ta kwaɓe hawaye ya ciko idanunta ta ce, " Aunty Abuja fa? Dan ALLAH kice su Aunty Preety su raka shi wallahi tsoro nake ji " wata razananniyar tsawa ta buga mata Indo har sai da ta ja da baya sannan ta ce, " Su Preety ɗin bayinki ne da zasu dinga fita suna nemowa kina zama kina ci, zaki wuce ko sai na ci miki mutumci? Kuma wallahi karki bari ya kawo mun ƙararki " Indo tana hawaye ta ɗauki jakar ta fice, tana fita ya buɗe mata mota ta shiga Aunty sai zabga Addu'a, Indo na shiga Honourable yaja motarsa suka bar unguwar, kai tsaye guest house ɗinsa ya wuce da ita dake Unguwar Nassarawa GRA.

WASA FARIN GIRKI🤒

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[15/07, 19:10] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

43&44
Chapter 21 · 0% Book details