← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 76

Sashe 5

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baraka ma na shiga ɗaki ta banko ƙauren ɗakinta ƙarshen gado ta koma tana maida numfashi dan ita a zatonta gamo ne tayi da aljanu cikin dare, fitsarin da bata yi ba kenan har akayi Assalatu.

Magajiya jin shirun Maigari yayi yawa bai fito sallar asuba ba yasa ta ƙaraso ɗakinsa tana ɗaga labule, cikin mamaki take bin ɗakin da kallo duk a hargitse ga ƙaramar katifarsa nan ta ƙasa duk a yamutse, tsoro ne ya kamata ganin ba Maigari babu motsinsa, cikin ta'ajibi ta fara magana, " To yau lafiya ni banji motsin malam ba kofa Sallar asuba banji ya fito ba " daga cen ƙarƙashin gado Maigari ne yake ɗan ɗago zanin gadon yana leƙe hango Magajiya da yayi a tsaye yasa ya yunƙura ya fito da ƙyar gaba ɗaya jikinsa yayi tsami, da mamaki tabi Mai gari da kallo tana faɗin, " Lafiya kuwa Malam naga ka fito daga ƙarƙashin gado? " Mai gari basarwa yayi yana murtuke fuska ya ce, " Ke Magajiya banasan shashancin banza da wofi ko a yaya aka samemu sai antambaye mu dalili ne? Ki kama bakink fa naga kwana biyu kinaji da rashin kunya " Magajiya bakinta ta tsuke ta juya zata fita sannan ta ce, " Allah ya baka haƙuri ya huci zuciyarka " Mai Gari yana ganin fitarta ya riƙe ƙugu yana sunkunyawa da alama bayansa ciwo yake masa, sai da ya fara zuro kansa ya leƙa ko'ina sannan ya samu ya ɗauki buta ya nufi hanyar banɗaki.

Baraka jin motsin Magijiya a waje ne yasa ta yi ta maza ta fito amma har lokacin bata saki jikinta gaba ɗaya ba, tana nufar hanyar banɗaki ta hango Maigari tsugunne abakin rariya yana kama ruwa, riƙe baki Baraka tayi tana faɗin, " Malam yau me nake gani a idona kaine tsugunne a bakin rariya kana kama ruwa " Mai gari baibi ta kan Baraka ba yana gamawa ya zare wandon jikinsa ya ajiye a gefe ya kalleta ya ce, " Ga wancen kayan ki wanke mun su idan kinyi sallah bari na ƙwaɓo na jikina na haɗo miki da su "

Da ido Baraka ta raka shi cike da takaici take kallonsa, banɗaki ta faɗa tana fitowa ta samu ya kawo mata ragowar kayan daya cire ta sameshi tsaye a da bokiti a hannu, juyawa tayi ta kalli kayan wani ɗan bashi-bashi taji yana tashi ta kalli Maigari ta ce, " Wai Malam mai ya samu kayanka ne har kake san a wanke maka su da farar safiyar nan wallahi ni wani bashi-bashi ma naji sunayi " A ƙufule Mai gari ya ce, " Ke saboda baki da mutumci dan na baki wanki har sai na gaya miki dalilin da ya sa na baki wankinsu, ki kiyaye ni fa " yana ƙarasa faɗa ya fa ɗa banɗaki domin wanke jikinsa, mita ta farayi ƙasa-ƙasa sannan ta wuce ɗaki, Mai gari ruwa ya watsa ya wanke jikinsa ya ɗauro Alwala ya koma ɗaki dan gabatar da sallar Asuba.

Maigari tunda ya idar da sallah tunanin duniya ya addabi rayuwarsa, tunda ya zauna a ɗaki yake saƙa da warwara musamman idan ya tuna cewar fatalwa tace kar ya sanarwa da kowa abunda ya faru kuma wai zasu dawo gurin sa, tunowa yayi harda fatalwar mahaifiyarsa Marka mai waina da ta Muzammilu mai icce, hawaye ne ya fara gangaro masa na tausayin kansa da yake yi, kansa tun cikin dare banda raɗaɗi babu abinda yake masa hannu ya kai ya shafa gurun sai ji yayi kansa zuwa goshinsa sunyi wasu manyan Ƙullulai, sauran Robb ɗinsa ya ɗauko ya fara bi yana shafawa sannan ya ɗauko hularsa ya saka ya janyo rawaninsa ya ɗaura duk dan gudun kar matansa su gani su fara jefo masa tambaya.

Baraka ce ta fito tana gayawa Magajiya irin mugun gamon da tayi cikin dare har fasaltawa Magajiya irin shigar da ta ga aljanar dasu tayi da maganar da aka gaya mata na cewar za'a tafi da ita, Mai gari najin haka cikinsa ya kuma ɗiban ruwa wani irin ƙugi yaji cikin yayi masa, da sauri ya tashi ya tafi banɗaki domin ji yake kafin yaje gudawar da take cinsa zata iya zubowa, daga Baraka har Magajiya binsa sukayi da kallo sai da suka ga ya wuce suka fara kus-kus ƙasa-ƙasa.

Baraka ƙarasawa tayi ta far duba kayan da zata wanke ganinsu jiƙe da fitsari da ƴar gudawa yasa ta yafito Magajiya da hannu tana nuna mata, badan ranta yaso ba haka ta fara wanke su cikin ƙyanƙyami, magajiya banda dariya ba abinda take yi tana faɗin Allah ya tarfawa garinta nono ba ita ce da girki ba da tuni ita zata wanke su, Maigari na fitowa ya hau muzurai yana tsuke fuska dan gudun kar su fara tambayarsa yana tafe yana bubbuɗawa har ya ƙarasa cikin ɗakinsa ya rafka uban tagumi.

Indo da ƙyar da iya tashi sallar Asuba saboda baccin da yake addabarta tana yin sallar kuwa ta koma ta ƙara kwanciya, ba ita ta tashi ba sai wajen tara saura, wanke idanunta tayi Baba Huwaila ta zuba mata abinci sai da ta ci tayi ƙat tana gama cin abinci ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanke su sannan ta ɗau bokitin ɗiban ruwa ta wuce gidan su Karime, a hanya suka haɗu da Jamilu kamar bata ganshi ba haka ta ɗauke kanta zata wuce, fisgota yayi ya riƙe kunnenta sannan ya ce, " Idan kinje ɗiban ruwan dan Allah karki dawo akan lokaci yau inkinje ki cire kan ƴaƴan mutane tunda jiya goshi kike fashewa lantan " ya ƙarasa faɗa yana zuba mata ranƙwashi, da sauri ta fisge tayi gaba tana yimai Allah ya isa.

Cikin Arashi aka wani gari da rasuwar wani maƙocin su Indo Malam Haruna mai wankin hula, katangar gidansa ta baya tana jikin ta gidan Maigari lafiya kalau aka kwanta da mutumin ya wayi gari da Amai da gudawa zuwa safiya kafin akaishi asubiti rai yayi halinsa, lokacin da labarin ya isa kunnen Mai gari har ya shirya yana shirin fita fada duk da baya jin daɗin jikinsa amma haka ya daure gudun kar wani ya harbo jirginsa, Maigari na jin mutuwar Malam Haruna wani irin azababban gumi ne ya yanko masa take cikinsa ya karta kafin ya isa banɗaki har ya fara ɓata wandonsa.

MORE COMMENTS.......🥱

_ASEELA FANS NASAN ANATA ZUBA EYES TO AMUN UZURI ZUWA SALLAR MAGRIBA._

_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

9&10

Tsoro ne ya kama su baraka musamman da sukaji labarin amai da gudawa ne ya kai Malam Haruna mai icce ƙasa, gasu sunga mijinsu sai zarya yake tun safe, bayan Mai gari ya fito yana tafe tana tamke fuska, ɗakinsa ya koma cen kan katifarsa ya faɗa ki kake rigija saboda gaba ɗaya jikin Mai gari ya saki, Magajiya da baraka ne suka shiga ɗakin duk yanayinsu ya nuna suna cikin damuwa.

Guri suka samu suka zauna kallon kallo suka farayiwa junansu anrasa wacce zata fara magana, ɗagowa yayi da kansa ya kallesu yace, " Lafiya kuka zo kuka tsare ni da idanu? " Baraka ce tai ƙarfin hali tace, " Malam ga dukkan alamu yau baka wayi gari da daɗin jikinka ba, shine mukazo muji me yake damunka? " tun kafin ta gama ya fara watsa mata harara sannan yace, " Uban waye yace muku bani da lafiya? Wato duk wani motsina akan idanunku nakeyi ko, ku tashi ku bani guri tun ranku bai ɓaci ba " Magajiya da Baraka haka suka fice suna jin haushin wannan hali irin na mijinsu.

Indo gidansu Karime ta biya suka fito suka wuce gidansu Zulai daga nan suka wuce gidan su Saudai suna tafe suna hira Indo sai da ta waiga hagu da dama sannan ta fara bawa su Karime labarin abinda ya faru, aikuwa mai zasuyi ba dariya ba harda hawaye, Zulai ce ta cewa Indo, " Dan Allah Sarƙa inzaki koma ki tafi dani nima ayi Dramer dani " Indo jim tayi sannan ta ce, " Idan kina da farin hijabi sai muje amma fa yau bazan koma ba dan kar ya gano ni bari zamuyi sai ya fara sakin jikinsa tukunna sai muje masa, mu bari zuwa nan da jibi ko gata " Su Saude ma cewa sukayi baza'a barsu a baya ba suma zasu je, Indo wani tunanin faɗa zuwa cen ta saki murmushi ta ce musu, " Gaskiya na fasa kowa ya nemi riga da wano na yadi ko shadda amma fa waɗanda suka muku yawa, nima zan ɗauki na Jamilu insaka kunsan Malam Haruna ne ya rasu inda mukayi shigar maza sai muje a zuwan Haruna ne ya taso da jama'arsa " shawar Indo ba ƙaramin daɗi tayi musu daɗi haka suka cigaba da hira har suka ƙarasa gurin ɗiban ruwan.

Bayan sun ɗebo ruwa suna tafe suna hira a hanya Indo tai farat ta ce, " yauwa Zulai muje zan biya ta gidan Mai gari inga halin da yake ciki " ba musu kuwa maimakon duk su wuce gida suka tafi gidan mai gari, a ƙofar gida suka samu Ado tun baya wani lokaci da ya tura agayawa mai gari yana jiransa zuwa sallar jana'izar Malam Haruna, ganin su Indo yasa yaji daɗi cikin sakin murya yace, "a'a Indo ciki zaki shiga ne " caraf ta amshe zance, " eh zamu je gun Magajiya " da sauri yace, " dan Allah idan kun shiga kuce yallaɓai kawai ake jira " Mirmushi su Inso sukayi saboda tuno muguntar da zasuyiwa Mai ugari.

Da sallama suka shiga cikin gidan Baraka ciki-ciki ta amsa musu hango ƙofar ɗakin mai gari sukayi labule a ɗafe, kallan juna sukayi suna murmushi.
Chapter 5 · 0% Book details