Sashe 38
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
65&66
Jamilu furzar da iska mai zafi yayi sannan ya watsa masa manyan idanunsa ya ce, "Kai wane naka dalilin har zaka tsare ni da tambaya?" Yaseer gani yake kamar ma Jamilu ya raina masa hankali, be ƙara bi ta kan Jamilu ba. A karo na farko riƙe hannun Indo yayi ya ce, "Muje Humaira karki ɓata mun rai" wani irin yar taji amma sai ta maze, ba yadda ta iya haka ta bi Yaseer ta fito daga cikin motar. Haushi ne ya turniƙe Jamilu ya yunƙura da ƙyar zuciyarsa na zafi ya fito.
Fitowar Indo yayi dai-dai da ƙarasowar Fahad lokacin su Momma tuni sunyi gaba, Kallan Hannun Yaseer yayi ya ganshi saƙale da na Indo, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke fuska a tsuke ya ƙara gurinsu, bai bi ta kan kowa ba ya sa hannuwa biyu yana zare hannuwan Yaseer dana Indo, da mamaki Yaseer ya bishi da kallo ya ce, "Brother meye haka" Fahad juyowa yayi lokacin idanunsa sun rine jawur, wani yawu mai ɗaci ya haɗiye sannan ya juya hannunsa riƙe dana ta.Da sauri Indo ta yunƙura zata cire fusge hannunta ji tayi ya riƙe katamau, cikin muryar ta ta ce, "Wai meye haka ne ka wani riƙemun hannu?" Watsa mata dara-daran idanunsa yayi ya ɗauke kai, cen har lamubu ya bi da ita, a jikin bango ya jingina ta ɗan yatsa ya sa ya nuna ta sannan ya ce, "Kar inƙara ganin kin shigewa ɗan uwana! Ina fatan kin jini, Saboda banasan ki ɓatamin ɗan uwan" yana gama faɗa ya wuya yayi gaba, ai kuwa da sauri Indo ta sha gabansa tana faɗin, "Kambun ubancen! Wallahi bazaka faɗa mun baƙa ka wuce haka nan ba, ni kake cewa zan ɓata maka ɗan uwa? To daga yau wallahi kace masa ya fita harkata" ta nuna shi da ɗan yatsa tana murza su sannan ta ci gaba da cewa, "Idan ba haka ba wallahi sai ya gane kurensa" Murmushi yayi ya fara latsa wayarsa, sannan ya nuna mata ya ce, "Kina nufin kin manta wannan rayuwar da kika yi" Indo zaro ido tayi ganin bidiyon ta da Honourable a resturent sai dariya take, shi ɗinma dariya yake sai dai bata kai ga jin me Honourable zai faɗa ba Fahad ya ce, "Oh! na tayar miki da tsohon tsumi ko? To ai..." Muryar Yaseer suka tsinta cikin ɓacin rai ya ce, "Fahad wau meye kake yi haka ne? Ka janyo yarinya nan gurin su Momma na jiranmu" hawaye ya gani shaɓe-shaɓe a fuskar Indo, da sauri ya ƙaraso yana huci ya ce, "Me kayi mata? Nace kayi mata?" duk a hargitse yake tambayar Fahad.
Fahad murmushin gefen baki yayi cikin isa ya ce, "Idan wani abu nayi mata zaka rama mata ne?" Yaseer wani hargitsatstsen kallo ya watsawa Fahad cikin kausashshiyar murya ya ce, "Ka dinga gyara kalamanka fa akan Humaira zan iya yin komai" yana gama faɗa ya sa hannu a aljihu ya ciro Handkee ya miƙa mata, wani banzan kallo ta watsa masa ta juya da gallawa Fahad harara ta wuce abinta, sororo Yaseer yayi ya juya yana yiwa Fahad kallon tuhu sannan ya ce, "Me ka gayawa yarinyar nan akaina?" ɗaga kafaɗa Fahad yayi cikin halin ko'inkula ya ce, "Ka binciki kanka idan kana da wasu munanan halaye to su na sanar mata" yana gama faɗa ya wuce ya barshi a tsaye.
Indo na fita taci karo da Jamilu ya kawo kai, da sauri ya ce, "Ayusher me yayi miki?" Girgiza kai tayi ta ce, "Babu komai" badan ya yarda ba ya nuna mata kamar ya amince, cen hanyar da yaga su Mommy sunyi cen suka nufa, kafin su ƙarasa Daddy ne ya fito yana faɗin, "Yaran nan wai ina suka shiga ne?" yana rufe baki yaga tahowarsu gabaɗaya.Bayansa suka bi sannan suka ƙarasa katafaren falon.
Wata Farar mata suka hango zaune kusa da maigidanta, ko ba'a faɗa maka ba kana ganinsa kaga daddy zaka fahimci ƴan uwan juna ne, matar bata fi shekara talatin da bakwai ba. Fuskar ta ɗauke da murmushi ta tarbe su, Indo bin matar tayi da Kallo har ta ƙarasa kusa da Baba Huwaila ta zauna, Daddy ne ya kalli Aunty Safna ya ce, "Safna yau nazo miki da wani abu mai girman gaske" da zumuɗi Alhaji Khaleel ya ce, "Na me fa Yaya?" Aunty safna ta ce, "Amma Yaya kafin wannan dan Allah a ina kuka samo ƴar beauty haka, ga kuma Baba baku min bayaninsu ba"
KUYI MANAGE ƘARFIN HALI NAI KAWAI NAYI TYPING SBD YAU NAYI BUSY WALLAHI
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[26/08, 16:13] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_

67&68
Daddy Murmushi ya yi ya ce, "Safna zumuÉ—in me kike yi? Ai duk gaggawar asara ta jirayi samu ko?" dariya duka mutanen falon sukayi banda Jamilu, Yaseer da Fahad da suke watsawa junansu harara a fakaice.
Daddy ne ya ci gaba da cewa, "Khaleel yau shekara nawa kenan da haihuwar ƴarka Aisha?" Alhaji Khaleel yanayinsa ne ya sauya cikin sigar damuwa. Murya a raunane ya ce, "Yaya nayi matuƙar mamaki da jin wannan tambayar taka" yana rufe baki Aunty Safna ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kukan ta yake ji har cikin ransa, saboda kowacce uwa dole zuciyarta ta sosu a duk lokacin da aka ambaci ɗiyarta wacce rasa, musamman idan ba mutuwa bace wani sanadi ne na daban. A raunane Alhaji Khaleel ya runtse idanunsa shima kamar zai zubar da ƙwalla ya ce, "Yaya wannan maganar da kayi mana kamar ka famo mana da tsohon gyambon da yake damun mu a zuciyar mu, ka gafarce ni Yaya idan maganar nan bata da wani muhimmanci muyi haƙuri mu barta, amma kayi haƙuri idan maganganuna sunyi tsauri." ya ƙarasa maganar idanunsa na cikowa da ƙwalla. Gabaɗaya mutanen falon babu wanda bai tausaya musu ba duba da yanayin da suka ga ma'auratan sun shiga, bisa tambayar da akayi musu. Jamilu cikin zuciyarsa yake faɗin, "Tabbas labarin Humaira tafe yake da sarƙaƙiya da tausayawa, ga dukkan alamu an zalinci waɗannan bayin Allah."