← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 76

Sashe 51

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a lokacin Indo ta farga wata ƴar kunya ce ta kamata, shi kuwa tsuke fuska yayi kamar zai yi mata magana sai ya tuna, yana mata magana yasan zai iya wargaza komai zata iya ƙin fita. Miƙewa yayi ya ce, "Sauri ki fito yana jiranki" yana fita Indo ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Nan take ɗaya daga sashen zuciyarta ya ce, "Me yake damunki? kin manta waye Fahad? Kawai dan ya tausasa miki harshe na lokaci ɗaya, har zaki fara tunaninsa." guntun tsaki tayi a filinta ce, "Ko meye abin tunani akan wancen oho, dukda kamar su ɗaya da Yaseer amma Yaseer ya fishi komai" tana gama magan ta ɗau hijabi ta fice.

Tana zuwa ta hau kan kujera ta ƙame guri ɗaya, Malam Khalid alwala ya ƙara ɗaurowa sannan ya zauna ya fara karatun alƙur'ani. Sai da Malam Khalid ya shafe awa ɗaya cif amma ko motsi baiga Indo tayi ba, kallan Fahad yayi ya ce, "Malam Fahad muje inasan magana da kai" Malam na gama maganar ya nufi bakin ƙofar, da sauri Indo ta ce, "Malam angama ruƙiyyar zan iya tafiya?" Malam yace, "Eh! Zaki iya tafiya" Indo kamar dama jira take tun bai rufe baki ba, ta tashi zata wuce sashenta su Momma suka fito. Da mamaki suka bi Indo da kallon ganin tasha zumbulelen hijabi, barka da hutawa tayi musu ta wuce ɗakinta.

Malan ya gaida su Mommy sannan ya koma suka zauna gabaɗaya, ya fara musu bayani akan ruƙiyyar da aka kirashi yayi. Sai dai sam babu wasu ginnu a jikin Indo, mamaki sukayi suka kawo kuɗi suka bashi tare da yi masa godiya, ya yi musu sallama ya tafi. Mommy ce ta kalli Momma ta ce, "Amma lamarin da mamaki fa" Momma ta ce, "Wallahi nikam banyi mamaki ba idan kika tuna da lamarin da su Baba Huwaila suka bamu, wallahi nifa dama jikina bai bani aljanu bane shaƙiyancin yarinyar nan yawa gareshi" Fahad dake gefe ya ce, "Amma wallahi yarinyar nan data gane kurenta" yana gama magana ya nufi ɗakin, Indo ta cire hijabi kenan Fahad ya ja hannunta ko magana babu, bai dire ta a ko'ina ba sai gaban su Mommy. Aunty Safna ce ta rufe da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Mommy ce ta karɓe zancen cikin lallami da nasiha.

Nasiha mai kashe jiki Mommy tayi mata tare da nuna mata illar kwaikwayon abinda takeyi, sosai jikin Indo yayi sanyi nadama ƙarara ta hau kan fuskarta. Su Mommy sun lura da haka ita kanta Aunty Safna ba ƙaramin daɗi taji ba, ganin yanayin da Indo ta shiga na nutsuwa. Fahad kallan Indo yayi ya ce, "Allah sa dai ta ɗauki faɗan da akayi mata, dan Allah Aunty ji yadda take sunne kai kamar ta kirki" Aunty Safna ta ce, "Kaima dai ka faɗa Fahad, wai a haka Yaseer yake so da wannan sakarcin nata" Indo zumɓurar baki tayi gaba ta ce, "Dan Allah Ammi ku daina faɗa a gaban Ya Fahad karya rainani" Indo ba ƙaramin dariya ta bawa su Mommy ba, Aunty Safna ta ce, "Wane raini kuma bayan shi ya fara saninki a lokacin da kike ƴar ƙauyenki, ba yanzu da kike waye ba. Ai wallahi kome kika zama yanzu Ɗana Fahad ne sila" Fahad kansa murmushi yayi, ko ba komai ya samu abin gori nan gaba, Indo kamar zatayi sabida takaici. Mommy ta ce, "Rabu da su Humaira, kice asalin kowa ma ai ƙauye. Kuma cen ɗinma ai a gida kike tunda kin rayu da Kawunki Maigari" Indo kamar wata yarinya ta yiwa Fahad gwalo, sannan ta ce, "Yauwa Mommy naji kince Maigari ɗan uwanku ne, amma banji kun gaya mun alaƙarku da shi ba rannan" Mommy ta ce, "Mahaifinsa da Mahaifin abokan wasa suke, lokacin da Mahaifinmu zaizo garin saida ya yiwa mahaifin Maigari tayin zuwa amma yaƙi, sai wani zuwa da Mahaifinmu yayi suka taho tare, har dai Allah ya sa shima yayi tunanin dawo da iyalinsa garin nan. Amma shi Mahaifinsa sai ya fara safarar kaya yana kaiwa garin Kura, har aminci ya haɗasu da Maigarin wancen lokacin. Humaira labarin yana da tsayi a takaice dai Maihafin Maigari ya zamu zama a wancen garin kuma mutum ne me amana, da tsoron shiga haƙƙin wani. Lokacin da Maigarin wancen garin ya fara wata jinya, sai yayi sanarwa tare da saka sojojin masarauta, ya sa hannu akan ko da bayan ransa Mahaifin Maigari, shi zai cigaba da mulkarsu saboda tausayinsa da amanarsa. To kinji yadda akayi, banda ma zumuncin yanzu ya zama yadda ya zama, dama duk cikin ƴan uwana ba yabon kai ba nafi su ƙoƙarin zumunci, kuma da har zuwa Kura muke muna zuwa mu shafe watanni a cen. Ni da kike gani a cikin garin da kikayi rayuwa babu inda bansani ba, idan na fara baki labari sai mu kwana anan." Indo ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Taɓ amma wallahi Maigari nasha da ƴan ƙauyen nan sam be ɗauko halin mahaifinsa ba, zalinci a cikin mutumin nan kamar..." da sauri Mommy ta ce, "Gidanku Humaira" Fahad yayi karaf ya ce, "Ku barta ta faɗa dan ni kaina wani zuwa da mukayi inaji wasu mutane na zaginsa, wai ya cinye wata gonar gadonsu" Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarka ana kwaɓar ƙanwarka kana kuma sakin bakinka" Fahad dariya yayi ya tashi zai shiga ɗakin, Indo ta ce." Ai wallahi nina saita shi sai da ya mayar musu da dik gonakinsu" da mamaki ta fara suka kalleta, gyaɗa kai Indo tayi basu labari tun daga lokacin da aka damƙawa Maigari takardunta, da ɓadda kamar da sukeyi ita ƙawayenta. Hatta ludayin da suka dinga ranƙwalawa Maigari sai da ta faɗa da umarnin da suka bashi akan ya mayar wa da mutane dukiyarsu.

Fahad duk gimtsewar da yakeyi sai da ya dinga ƙyalƙala dariya, su Mommy dariya suke harda hawaye sai da suka tsaida, Mommy ta ce, "Dama Humaira ke kika rikitamu ɗan uwa lokacin da muka je" Indo dariya tayi ta ce, "Mommy nima ai Ya Fahad tasoni yayi saura kaɗan asiri na ya tonu, wallahi da ya kamani da na kaɗe dan ƴan garin nan sai mun tofin Allah tsine" Fahad me zaiyi banda dariya, Aunty Safna ta ce, "Ikon Allah wato mu duk shakiyancin ƙuruciya da mukayi muna yara, bamu kama ko rabinki ba Humaira. Allah ya ƙara shirya mana ku gabaɗaya." gabaɗaya suka amsa da Ameen, suna nan zaune Daddy mahaifin su Fahad ya shigo hannuwansa riƙe da su Aseem, zama sukayi suka cigaba da hira cikin barkwanci.

Alhaji Mahmud Lamiɗo shine ainihin sunan Mahaifin su Fahad, asalinsa Fulanin daura ne. Sai dai kakanni da iyayensa a buɗi ido ya gansu a cikin garin Kano, Iyayensa sun rasu bayan haihuwar su Fahad babu jimawa, Su uku ne rak a gurin iyayensa. Shine babba sai ƙannensa mata biyu, Alhaji Mahmud ɗan kasuwa ne saboda baiyi wani zurfi a karatun boko sosai ba, Allah ya bunƙasa kasuwancinsa har ƙasashen waje yana fita sarin kaya. Mutum ne mai matumci da karamci gashi da zumunci da taimakon marasa ƙarfi, uwa uba gashi da alheri da sakin fuska.

MU KOMA LABARI

Kwanan su Indo biyu suka wuce garin Kaduna, wannan karan ma ba tare da Fahad suka wuce ba, saboda wani uzuri da zai gabatar kafin komawarsa. Indo ji tayi kamar ta je ta ajiye masa takardar da ta É—auka, amma sai kawai ta share har suka koma.

Makaranta me kyau Mahaifinta ya nemar mata idan tare da direban da yake kaita, yana dawo da ita. Wannan karan a JSS3 aka sakata tare da É—aukan malam da suke yi mata lesson a gida, makarantar su Indo haÉ—e take da islamiyya basu suke dawowa gida ba, sai gabanin magriba. Wannan dalilin yasa koda Fahad ya koma basu cika wani haÉ—uwa ba.

Indo batasan yadda akayi Yasir ya samu lambarta ba, amma kodai mene ne tasan a gurin Momma ya ƙarɓa, Indo tun tana fushi da Yasir har ta sakko suka cigaba da mutumci, kamar yadda Indo ta ɗauka tunda har yau Yasir bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba.

Wata ranar Asabar Indo na cikin garden Yasir ya kirata a waya, sun shafe awa guda suna waya banda murmushi babu abinda take, wani lokacin sai dai ta tuntsire da dariya, kome Yasir ya gaya mata ta miƙe tsaye tana murna harda tsallenta.

Dun abinda takeyi Fahad na tsaye yana kallanta wani ƙululun takaici ne ya rufeshi, Bai ankara ba yaji tace, "Wallahi nima nayi missing ɗinka Ya Yasir, amma kasan me zaka siyo mun idan zaka zo?" Kafin Yasir yayi magana Fahad ya ƙaraso a zafafe ya fusge wayar, kasheta yayi gabaɗaya fuska a tamke yace, "Ƙaramar yarinya da ke har kin iya soyayya ko? Shi kansa Yasir ɗin zamu gauraya dashi, zanga wanda zai ƙara baki waya yanzu" Indo batasan lokacin da hawaye ya fara zubar mata a fuska ba, da gudu tabi ta gefensa ta wuce ɗakinta. Iska mai zafi Fahad ya fesar ya wayar a aljihu ya bar gurin.

AKWAI ƘURA🙊🤣😂

KUYI HAƘURI DA KURAKUREN CIKI.

WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA ƳAN GROUP ƊINA NA *AMEERA ADAM FANS GROUP* DA MUTANENA ƳAN AMANA TA *WATTPAD*

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[24/09, 13:08] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

87&88
Chapter 51 · 0% Book details