Sashe 62
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Dan Allah ki saurareni kuma ina roƙonki da kimin adalci, karki ƙi amincewa da buƙatar da nazo gurinki" Indo Zuba masa ido tayi tana kallo haɗe da mamakin wai yau Fahad ne, yake mata magana cikin tausasa harshe tare da roƙon alfarma agurinta, lallai ta tabbatar abu ne me muhimmanci. Haɗiyar yawu tayi sannan ta ce, "Ina jinka Ya Fahad" Fahad kafeta yayi da kallo ya ce, "Humaira na jima ina ƙaunarki..." A zabure Indo ta miƙe tsaye ko ƙarasa jin kalamansa batayi ba, a ɗan tsorace ta ce, "Ya Fahad kasan me kake faɗa kuwa? Anya ba mantuwa kayi ba?" Fahad cikin nutsuwa ya ce, "Dan Allah Humaira ki amshi soyayya ta Please" ya ƙarasa faɗa yana haɗa hannuwa biyu alamar roƙo. Indo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Ya isa Ya Fahad! Dan Allah da wanne zanji? Wance yace, Shi yace kaima yanzu ka ce mun. Dan Allah ku bar zuciyata ta huta wallahi kaina ba ƙaramin caji ya ɗauka ba, yanzu ya kuke so nayi?" ta faɗa tana zubda ƙwallah, bata jira cewarsa ba ta wuce ciki a gaggauce cikin tsananin damuwa. Fahad dafe kansa yayi yana haɗiyar yawu me ɗaci tare da zabga uban tagumi.
Tun daga rana Indo ta fara wasan ɓuya da Fahad, shi kansa Yaseer ya rasa gane kanta. Walwalarta da sakin fuskarta duk ya sauya, ya tambayeta yafi a irga amma babu wata ƙwaƙwƙwarar amsa da take bashi. Haka shima Jamilu tun daga ranar bai ƙara kiranta ba, ko ta whatsapp baya mata magana, ƙarƙari ta tura masa gaisuwa ya bata amsa tare da tambayar iyayenta, bayan wannan babu wata magana da take shiga tsakaninsu. Lokacin da Mahifiyar Indo ta tirke ta da tambaya sai cewa tayi kawai tana jimamin rabuwa da su ne, Aunty Safna sam bata yarda ba amma tasan idan tayi wari dole ta ji.
A kwana a tashi ba wuya lokacin komawa su Hajiya Safiya kotu yayi, kamar kullin a yau ma kotun cike take da mutane, iyayen Indo gabaɗaya sun halarci zaman. Shigo da su Hajiya Safiya akayi ita dasu Hadari, fuskarta harta rame tayi baƙiƙƙirin. Magatakarda ne ya gabatar da ƙararsu Sannan aka buƙaci lauyoyin masu ƙara da su kawo hujjoji, Lauyan su Indo ne ya tashi ya ciro wayar Hadari tare da nuna Musty dake kan kujerar marasa lafiya, da sauran shaidun da ya tattara ya miƙawa alƙali. Alƙali karɓa yayi tare da waiwayar Lauyan waɗanda ake ƙara, domin gabatar da sheda da shedun kariya amma yace bashi da wata shaida. Alƙali ya juya gurin Hajiya Safiya yace, "A zaman da ya gabata kin koro bayani dan haka muna sauraronki"
Hajiya Safiya ta ce, "Bayan na yi duk yadda zanyi na shiga jikin Safna sai watarana bayan Khalil yazo gurinta, sunyi sallama har ta shiga gida sai nai maza na fito daga soron gidanmu da nake a laɓe, nazo na sami Khalil na gabatar masa da kaina da abinda yake zuciyata. Mamaki ne ya kamashi ganin ni babbar ƙawar budurwarsa amma zanyi mata haka? A take ya kifeni da mari tare da zageni tas ya hankaɗa ni gefe ya buɗe motarsa ya shige, tun daga ranar na ɗauri aniyar yadda su biyun nan suka munana mun, na dinga dasa musu ɓacin ran da har sai yayi silar ajalinsu, ana cikin haka wata rana kakar Safna tayi rashin lafiya sai muka je dubata nida mahaifiya, a ranar Khalil yaje da ɗan uwansa wanda ni kuma a ranar ne Allah ya haɗani da Uban ƴaƴana, ganina da yayi yaji duk duniya babu wacce yake so sama dani, ni kuma har lokacin zuciyata na kan ƙaninsa, amma gudun kar nayi biyu babu yasa na amincewa yayansa. An riga bikina da Haruna sakamakon karatun da Khalil yake yi ba'ayi nasu a wannan lokacin ba, ana cikin haka ba daɗewa sai Kakar Safna ta rasu wacce take riƙonta bayan rasuwar iyayenta, wannan dalilin ne yasa ta koma cen gidan yayarta.
Bayan bikin Safna da Khalil sai suka dawo garin Kaduna, anan na cigaba da shige mata kuma duk lokacin da na fuskanci tana da ciki, sai nasan dabarar da nayi na bata ƙwaya tasha cikin ya zube, ana cikin haka har Allah yasa ta haifi Ɗanta namiji da yake Allah yayi sai ya shaƙi iskar duniya, amma ranar suna sai na faki ido na toshe masa hanci har ya mutu, haka nayi tayi mata har lokacin da nasa ƴan fashi suka je suka ɗauki Humaira tana jaririya, ashe basu kashe ba sai gashi ta ƙara bayyana. Bayan dawowarta nayi niyyar sawa a kashe ta amma sai na lura da irin tsaron da suke bata, sai da na bari sun sakankance na aika su Hadari su kashe ta." gabaɗaya kotun hayaniya ta ɗauka sai da Alƙali yayi gyaran murya sannan kowa yayi shiru, Alƙali ne ya yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da horo mai tsanani na shekara uku-uku.
Hajiya Safiya kuka ta rushe da shi ƴan uwanta ma suka saka kuka, suna ji suna gani ma'aikatan gidan yari suka tasa ƙeyarsu. Haka kotun ta tashi kowa yana yabawa da hukuncin da Alƙalin ya yanke.
Su Lubna sunyi kuka kamar ransu zai fita haka mahaifinsu, ya rungumesu yana jin tausayin Æ´aÆ´ansa a zuciyarsa.
*KWANCI TASHI ASARAR RAI*
Bikin Yaseer da Indo ya zo daga kowanne ɓangarori shiri ake ta hidimar biki, saura sati biyu bikin aka kawo lefen Indo akwati shida. Sun zuba mata kaya sosai gwanin birgewa, ganin bikin ya matso yasa Fahad ya tattara kayansa ya koma Kano, Yaseer duk ya shiga damuwa ganin ɗan uwansa ba walwala, kuma yayi juyin duniya ya gaya masa damuwarsa amma yaƙi, har gwara ɓangaren Indo ta ɗan saki jiki ana mata harkokin gyara jiki, Momma tura Yaseer Kano tayi tasa aka kawo mata Indo gurinta acen take mata gyaran jiki da sauran magungunan da take haɗa mata.
Indo ba ita ta koma Kaduna ba sai ana gobe za'a fara biki, Ranar Laraba suka fara shagali, a ranar sukayi Bridal shower, Alhamis akayi Kamu, Juma'a akayi Dinner, Asabar Mother's day.
Babban abinda yafi tsayawa Indo a rai rashin zuwan Baba Huwaila, da ta tambayi mahaifiyarta ta ce mata Jamilu ne babu lafiya yana kwance a asibiti. Fahad da ƙyar ya lallashi zuciyarsa yake zuwa guraren Event ɗin, sai dai duk wanda ya ganshi zai fahimci yana cikin matsananciyar damuwa, sosai yake yiwa amarya da ango liƙi kamar babu abinda yake damunsa.
Ranar Lahadi ita ce ranar ɗaurin aure, daga gari-gari mutane suka dinga zuwa domin halartar ɗaurin aurenta, gidansu Indo cike yake ta ko'ina da mutane. Tun da gari ya waye Fahad yake aman jini abunda ya ɗaga hankalin iyayensu kenan, raba ƙafa akayi wasu suka tafi asibiti wasu kuma suka wuce gurin ɗaure aure. Ƙarfe goma dai-dai na safiyar ranar aka ɗaura auren Indo akan sadaki naira dubu ɗari, dubbunin mutane ne suka shaida ɗaurin aurenta.
Yaseer ne zaune a tsakiyar iyayensa kamar mace banda hawaye babu abinda yake yi, Daddy ne ya gyara zama ya ce, "Assalamu alaikmu, na tabbata gabaɗaya kunsan maƙasudin zamanmu a gurinnan, Yaseer gabaɗaya da kake ganinmu kalma ɗaya ce zamu iya gaya maka wato kayi haƙuri, duk abinda ka gani Allah ya rubuta wani baya auren matar wani, Allah ya rubuta Humaira matar Jamilu ce ba taka ba" Jin wannan kalmar yasa Yaseer ya kuma fashewa da wani irin matsanancin kuka.
ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ NASAN YAU WASU ZASU GA BAƘI NA.ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¼â€â™€ï¸
JAMIL FANS A FITO AYI CELEBRATIONS😂🤪🤣💃ðŸ»
MAGANAR GASKIYA YAU INA JIRAN COMMENTS🤥
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[30/09, 19:28] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
93&94