Sashe 71
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk waɗannan abubuwan ka fara ajiyesu a gefe har sai ka bari ta fara zurfi a sanka" guntun tsaki Jamilu yayi ya ce, "Wane so Malam Isa yau fa mun tafi wata biyar da aure tuntuni bata so ni ba sai wani zaman da zamu ƙara nan gaba?" Jamilu ya faɗa cikin damuwa. Malam Isa ya ce, "Haba Malam Jamilu kamar ba Namiji ba, yanzu abinda nake so da kai sai ka jajirce kacire duk wani abu da zaka ji yazo maka zuciya, dan ka daidaita rayuwar aurenku. Idan kaga tana zaune tsiri wayar ƙarya kai dan ka nuna da gaske kake ko ni ka kirani sai kayi kamar wayar gaske kakeyi da budurwa, idan ka dawo daga aiki da yamma gabannin magriba ka sheƙa wanka ka fice, kai abincinta ma ka rage ci idan ka samu ta tambayeka kace unguwar da kaje kaci acen, kuma idan dare yayi ka daidaici lokacin bacci yayi" Malam Isa ɗagowa yayi ce, "Wai intambayeka tare kuke kwana ko daban-daban" Jamilu yace guri ɗaya muke kwana" Malam Isa yace, "Yauwa to idan kaga ta kwanta ɗauki waya ka fita amma karkayi nesa da ɗakin, ka hau wayar ƙarya ka zuba kalamai yadda zata ji ka, ka shafe kamar minti biyar zuwa goma sannan ka dawo ɗakin ka kwanta. Amma fa da farko zaka ga barazana karka damu a hankali zaka ga ta fara damuwa har ta fara sakkowa" Jamilu yace, "Nagode ƙwarai Malam Isa, amma bakasan wace Aisha ba nasanta da taurin kai ƙwarai" Murmushi Malam Isa yayi ya ce, "Malam Jamilu kenan mace fa duk girmanta duk tsufan mace ce, ba'a sakewa tuwo suna" Jamilu ya daɗe yana ɗaukan darasi agun Malam Isa har lokacin tashi yayi.
Yamma liƙis ya shiga gidan lokacin Indo na kwance kan doguwar kujera tana karanta littafin MARWAN (Littafin Ameera Adam) taji shigowarsa, a ɗan tsorace ta juya saboda labarin da take karantawa cike yake da bantsoro, sanye take da T-shirt sai gajeren wando iya gwiwa tana kallansa ta ɗauke kai gefe tana cigaba da harkarta, a zatonta zaizo gurinta ya mata magana kamar yadda ya saba ta ga ya wuce ɗakinsa, ya jima a ciki da alama wanka yayi ya fito sanye da singlet da gajeren wando, ruwan tea kawai ya zuba ya hau kujera ya zauna yana danna waya ya kara a kunne cikin salon kashe murya yace.
"Hello, barka da yamma ina fatan banyi laifi ba?" shiru yayi ya ɗan saci kallon Indo da yaga ta ɗanyi wani jim, sannan ya cigaba da cewa. "Ok ba damuwa ai ko yanzu kika ce nazo aguje zanzo amma dai ataimaka abarni nayi magriba tukunna" Indo ya kuma kallo a fakaice yaga yadda tayi kicin-kicn ta tsuke fuska har abun yaso bashi dariya, tashi yayi ya cigaba da wayar ƙaryar har ya shige ɗakinsa ya laɓe daga ƙofa yana leƙen yanda zatayi. Indo na ganin shigewarsa ta tashi zaune tana cewa, "Ƙundun uba mutumin nan badai budurwa yayi ba" Jamilu na ganin haka ya ɗan ɗaga murya da ƙarfi yace, "I love you my baby" ƙirjin Indo ne ya buga kujera ta koma ta zauna jaɓar ganin zaman bazai kaita ba ta tashi ta shige ɗaki.Bayan sallar magriba tana zaune a ɗakinta ya shigo cikin galalleliyar shadda sai zuba ƙamshi yake, da biyu dama ya shigo dan taga shigar da yayi zai fita, cen gaban mudubi yaje ya ƙara fesa wani turaren yana nan tsaye wayarsa ta fara ringing, da sauri ya ɗauka yace, "Ina hanya karki fushi" yana katsewa ya fice daga ɗakin, tun bai ƙarasa falo ba Indo ta biyoshi cikin masifa tace, "Wai da wacce shegiya kake waya a gabana kuma ina zaka" wani kallo ya watsa mata har cikin ransa baiji daɗi ba a fili ya ce, "Karki ƙara zaginta saboda tana bani farinciki kuma babu ruwanki da inda zani" yana maganar ya fice. Indo saboda takaici kuka ta rushe dashi ta haye kujera ta ƙudura a ranta saita zauna taga dawowarsa. Jamilu tun da ya fita ya rasa gurin da zashi saboda bai saba fitar dare ba, yawo ya dingayi a mota har wajen ƙarfe tara da rabi na dare sannan ya shigo gida, Indo tun tana jiransa har bacci yayi awon gaba da ita ƙarar shigowarsa ce ta tasheta, yana ganinta yayi kamar be ganta ba zai wuce ta sha gabansa ta ce, "Daga ina kake?" fuska a tsuke yace, "Aikena kika yi, malama karki dagula mun farincikin da nake ciki da baƙin ciki" ya raɓa ta gefenta ya wuce ɗaki, kayansa ya cire ya haye kan gado ya kwanta yana nan kwance Indo ta shigo ta kwanta, sai da yaga kwanciyarta ya miƙe ya fara waya kamar yadda Malam Isa ya gaya masa sannan ya dawo ɗaki ya kwanta, yana jin Indo tana ta shassheƙar kuka tausayinta ne ya kamashi kamar ya rarrasheta sai kuma ya basar kamar be ji ta ba ya juya mata baya, yana jinta tun tana kuka har bacci yayi gaba da ita. Juyawa yayi ya haska fuskarta yaga duk ta kunbura bargo ya janyo ya rufesu ya tofesu da addu'o'i shima bacci yayi awon gaba dashi.
Tun daga ranar Jamilu ya sauyawa Indo kamar ba shi ba a haka har suka shafe wata biyu a wannan yanayin, ga wani irin kishinsa da yake nuƙurƙusar zuciyarta dan ta gama yankewa kanta hukuncin Jamilu aure zaiyi, gefe ɗaya kuma wata irin kulawa da take san bashi amma sam babu dama, ta rasa wa zata gayawa har tayi niyyar gayawa Mahaifiyarta taga idan ta faɗa ma ba lallai su yarda ba tunda sunsan dama cen ba san Jamilu take ba, Jamilu ya lura da halin da take ciki har ramar da tayi ba ƙaramin damunsa tayi ba, dan wani zuwa da sukayi gurin Baba Huwaila har hannunka me sanda ta dinga yi musu, dan a tunaninta Indo laulayin ciki take, Indo duk ta rame tayi zuru-zuru ko abincin kirki bata ci har olsarta ta tashi ga wani irin zazzaɓi me zafi daya rufeta, lokacin da ciwon ƙirji ya kamata ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, da kansa ya haɗa mata ruwan shayi ya sameta a ɗakin duƙunƙune cikin bargo, yakice bargon yayi ya riƙota ya zaunar da ita ya dinga bata tana sha da kaɗan-kaɗan har ta shanye. Magungunan daya siyo mata ya ɓallomata ya bata tasha bayan wani lokaci ya kamata ya kwantar ya rufa mata bargon, zagayawa yayi ya kwanta ya rungumota yana jin yadda jikinta yayi zafi sosai, zazzaɓin jikinta sai cikin dare ya sauka zuwa safiya jikinta yayi sauƙi sosai.
Washegarin ranar asabar ce Jamilu bashi da aiki wuni yayi yana bawa Indo kulawa, mamaki ne ya kamata sosai kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, haushi ɗaya ne ya kamata idan ta tuna Jamilu na soyayya da wata.Da daddare sun fara shirin kwanciya wayar Jamilu ta fara ringing ɗauka yayi ya fita daga ɗakin, Indo ji tayi zuciyarta na zafi hayewa fado tayi ta fashe da wani irin kuka, Jamilu bai jima ba ya shigo ɗakin ya sameta tana rera kuka me tsuma zuciya. Tausayinta ne ya kamashi haurawa yayi gadon ya zauna kusa da ita yace, "Ayusher me yake damunki" wani takaici ne ya kuma rufeta wato ma baisan me ya mata ba kuma rushewa tayi da kuka, janyota yayi jikinta yana bubbuga bayanta ya fara lallashin har ta tsagaita da kukan sannan yace, "Me yake damunki Ayusher ji yadda kika rame ko abinci bakya ci" Indo goge hawayenta tayi ta ce, "Ya Jamil meyasa yanzu baka sona baka kula dani ka tsaneni wai har wata ta fini a gurinka, baka farantamin sai dai waccen dan Allah ya Jamil meyasa ka koma haka?" ta ƙarasa faɗa tana hawaye wani farinciki ne ya lulluɓe Jamilu yace, "Naga bakya sona Ayusher shiyasa na samo wata" janye jikinta tayi daga jikinsa ta ce, "Ka rabu dani to sai ka zauna ita" janyota yayi jikinsa yace, "Ai nida ke mutu ka raba, duk wacce zata zo ma a bayanki take" Indo bata tanka masa ba ta cigaba da ruwan hawaye ganin yadda hankalinta ya tashi yasa Jamilu ya warware mata duk plan ɗin da suka haɗa shi da Malam Isa, kunya ce ta kamata Jamilu ya dinga mata dariya. Da wata irin murya yace, "Ayusher har yanzu baki bani amsar tambayata ba" wata kunyarsa ce ta kamata ta tura kanta cikin jikinsa tana murmushi, ɗago da fuskarta yayi yana ɗaga mata gira sannan ya furta. "Ina ƙaunarki Ayusher kuma bazan daina ƙaunarki ba" runtse ido tayi tana ƙasa da murya tace, "I LOVE U YA JAMIL!" waro ido waje Jamil yayi yana mamakin jin kalamanta ganin haka yasa ta janyo bargo ta rufe fuskata, dariya Jamilu yake ta farinciki sosai jin sa yake kamar wani sabon mutum, janyota yayi jikinta yana ƙara zubar mata da kalaman soyayya, nan take hirar ta fara sauya salo cikin salon faranta zuƙatan masoya wanda da alama a wannan lokacin Jamil zai tabbata cikakken angonsa.
Bayan wani lokaci Jamilu ne ya janyo bargo ya rufawa Indo tare manna mata kiss a goshi, a hankali yace, "Allah yayi miki albarka Ayusher" kunyarsa taji ta rufe fuska ta ce, "Ameen ya rabbi" tashi yayi yaje ya haɗa musu ruwa sai da yayi wanka sannan ya dawo ya taimaka mata ya rakata ƙofar toilet ta shiga, zai biyota da sauri ta banke ƙofar shida ita suka sa dariya lokaci ɗaya.
Da asuba Jamilu ne ya fara tashi ya fara tashin Indo yaji jikinta da ɗumi kamar me zazzaɓi, da ƙyar ta tashi bayan ya idar da alwala tashiga ta gabatar da tata alwalar ta koma dadduma ta gabatar da sallar asuba, bayan ta idar kafin su koma bacci sai da tasha paracetamol sannan suka koma bacci yayi awon gaba dasu.