Sashe 11
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwaɓe fuska yayi ya ce, " Mommy har wani fita zanyi nifa idan naga da takura sai na wuce gida inyaso gobe Yahaya yazo ya tafi da ke "
Mai gari daƙuwa yayi masa yace, " Kai gidanku, nabi takurawar da gudu ba hula, kaga babu inda zakaje sai kun gama kwanakin da ta ɗebo muku " murmushi Mommy tayi ta ce, " Ay Yaya gobe ma zamu wuce, amma Yaya lafiya naga duk kayi wani iri ga alamun raunuka nan akanka ko dai wani abu na faruwa ne? "
Maigari kwallah ce ta ciko mai idanu ya ce, " Babu komai Mejidda ciwo ne dai naji " Mommy sam hankalinta bai kwanta ba shiyasa ta kuma tambayar É—an uwan nata, " Yaya ciwo da me kaji ciwon? "
Baraka dake gefe tace, " Wallahi wata irin jarabta ce aka jarabcemu da ita, fatalwa ce take zuwa har gida tana yiwa Malam Lahani, rannan har mu tace zata haÉ—a damu "
Fahad shi da Mommy suka ce, " Fatalwa kuma, dama akwai wata fatalwa ne " Magajiya ta cigaba da cewa, " Wallahi kusan kullin sai tazo mana yau fa sai da Malam ya kwanta a asibiti saboda tashin hankali da raunin kansa "
Mommy Nuna ƙulalan Maigari tace, " Wannan ciwon ma fatalwarce ta ji maka shi? " Maigari da gabansa ke faɗuwa yace, " Wannan da kika gani hannunta ne yayi mun wannan ƙulalen amma Dan Allah mu bar magana, cigaba da yinta kamar ina ƙara kusantar mutuwa ta ne "
Ganin yanda duk ya firgice yasa Mommy ta shiga tausayin É—an uwan nata, cikin sigar tausayi ta ce, " Zamu bar maganar amma ka gayamun yaushe fatalwar take zuwa " cikin zumuÉ—i yace, " Tsakar dare ne " jinjina kai Mommy tayi suka cigaba da hirar yaushe gamo.
Indo tunda Fahad ya jefarta ƙasa baƙin ciki ne ya cika ta, batayi aune ba sai ji tai hawaye na zuba daga kuncinta, yara ne suka fara taruwa suna yiwa Indo waƙa, " Sarƙa taci Mari, Sarƙa taci mari, Sarƙa taci mari bakinta ya ja mata " Indo tashi tayi jiki ba ƙwari sai su Karime ne suka rakata har cikin gida.
Da kuka Indo ta shiga cikin gida, ba Baba Huwaila ba hatta Jamilu sai da mamaki ya kamashi, cikin tashin hankali Baba Huwaila ta fara jefo musu tambaya, Saude ce ta basu labarin abinda ya faru aikuwa Jamilu mai zaiyi ba dariya ba, da farko Baba Huwaila cewa tayi zata je taji akan me zai marar mata yarinya.
Jamilu ne ya ce mata, " Wallahi Baba Huwaila kije bakisan ba'aiyiwa irin waÉ—annan masu kuÉ—in haka ba, yana haÉ—awa keda ita ya kaimu cen policestation arufe ku "
Baba Huwaila najin haka tsoro ya kamata ta shiga rarrashin Indo tana bata haƙuri.
*CIKIN DADDARE*
Indo ce cikin shigarta da ta saba ta fararen kaya, wannan karan har ɗan ƙaramin tulun Baba Huwailata ɗauka ta tura wannan ƙyallen likkafanin aciki sannan ta nufi gidan Maigari. Kamar yanda ta saba ƴar katangar ta kama ta haye, kai tsaye ɗakin Maigari ta nufa cen kan gado cikin bargo ta hangoshi aikuwa tana zuwa batayi wata-wata ba ta ɗaga hannunta iya ƙarfinta ta ranƙwala masa aka, cikin azaba Fahad ya tashi firgigit saboda ludayin ba ƙaramin shigarsa yayi ba.
Indo tun kafin ya tashi tsaye tsoro ya kamata amma sai ta basar ta fara wani buga ƙafa ɗaya tana baza farin hijabinta, fuskarta bajau tasha hoda sai zaro mai idanu take, tana wani jijjiga kai sannan ya jefo mai tukunyar nan tana cewa, " KAINE RABONMU NA GOBE SAI DAI A WAYI GARI DA GAWARKA A YASHE " Fahad da haushi ya gama cika shi da sauri ya ƙarasa gurunta ya kifeta da mari.
🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *INDO SARƘA FANS ANCE RANA DUBU TA ÆARAWO.... KUJE KU KARÆO INDO YAU TA SHIGA HANNU.*
_AKWAI SABON LITTAFIN SABUWAR MARUBUCIYA MAI SUNA *HATSABIBI BOKA DAMGAS* SALON LABARIN NA DABANNE BAZAN CE KOMAI BA AMMA KU TARA ZAKU GANI DA IDANUNKU, KU DAKACE SHI NAN DA ÆŠAN WANI LOKACI NIDA ITA ZAMU FARA MUKU POSTING._
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
25&26
Indo cikin jin zafin marin tace, " Kuturun karen nan ka mari fatalwa? Wallahi sai ɗauki rayuwarka daga yanxu zuwa safiya kuma..." Indo bata ƙarasa magana ba Fahad ya kuma kifeta da wani marin cijin kausashshiyar murya yace, " Ke wace ce kuma daga ina? Waya turo ki kika zo kina azabtar da bawan Allah da sunan Fatalwa? " Indo tsuru tayi gabanta ya fara dukan uku-uku ilahirin jikinta karkarwa yake yi cikin ƙarfin hali ta ce, " Ni ƴar mutum biyu ce jikar mutum huɗu, kuma wannan marin da Wallahi bakaci banza ba, daga jiy zuwa ni akayiwa wannan marin " da ƙarfin gaske Fahad ya damƙo wuyanta yana huci.
Indo azaba ce ta isheta ba shiri ta janyo hannunsa da gantsara masa uban cizo, da sauri ya riƙe hannunsa yana faɗin, " Auwwtchh "
Indo na ganin haka ta fita da gudu kamar ɗan biri haka tabi katanga ta ɗane ta dirga, Fahad rufa mata baya yayi amma kafin yaje tuni ta sauka daga kan katangar, Maigari dake ɗakin Magajiya ƙarar gudun su Fahad ne ya tashe sakancewar dama baccinma rabi da rabi yakeyi, Fahad babu tsoro a tattare dashi ya yaje soron gidan ya fara ƙoƙarin buɗe sakata, yana fita wayam ya gani ba mutum babu alamarsa, guntun tsaki yaja sannan ya tura ƙofar gidan ya koma ciki.
Yana shiga ɗaki cen ƙasa ya hango wani abu a ƙasa haskawa yayi da fitila ya hango wani takalmin indo dana sai farin likkafin data jefa masa, tsugunnawa yayi yana duba takalmin yana jujjuyasu sannan ya koma cen kan katifar ya zauna yana nazari.
Lokacin da Indo ta dira batai wata-wata ba da gudu ta faÉ—a cikin gidansu, kai tsaye É—akinta ta shige tana sauke ajiyar zuciya, jikinta banda karkarwa ba abinda yake.
Tana nan sai ji tayi anhaske ta da fitila, a zabure ta juyo tana É—auke numfashi, cikin alamar tuhuma yace, " Ke daga ina kike acikin tsohon daren nan? " Indo zuru tayi ta rasa wacce amsa zata bawa Jamilu.
Cikin tsawa ya ce, " Zaki gaya mun ko sai jikinki ya gaya miki daga ina kike nace? " turo baki gaba tayi sannan ta ce, " Gidan Maigari... "
A hassale ya katseta, " Maigarin ƙanin ubanki ne ko na uwarki da zaki je gurinsa da tsohon daren nan ubanme kikaje yi gidansa? "
Indo shiru tayi bata tanka masa ba, Jamilu hassala ya daÉ—ae kai tsaye É—akinsa ya nufa yaje ya É—auko belt, yana shigowa ya rufe Indo da duka ta ko'ina, Indo ihu take kamar wacce ake zarewa rai, Baba Huwaila dake bacci sama-sama ta fara jiyo ihun Indo azabure ta tafi tana salati da salallami, Baba Huwaila ce ta shiga É—akin ganin abinda Jamilu yakeyi yasa ta fashe da kuka tana dukansa tambayar ba'asi.
Sai da jikin Indo ya gaya mata sannan Jamilu ya dakata da dukanta, cikin huci ya zayyanewa Baba huwaila dalilin dukanta, ita kanta jikinta ne yayi cikin jimamin maganar Jamilu ta ce, " Indo saboda Allah yanxu abinda kika aikata kinyi dai-dai kenan, meye haÉ—inki da wani Maigari? Wallahi nima a wannan karan bazan goyi bayanki ba. "
Indo cikin kuka ta ce, " Nifa Wallahi babu wani abu antsakaninmu kawai zuwa nake tsorata shi..." Tas Indo ta kwashe yanda sukeyi da Maigari ta gaya musu har zuwa yanda sukayi da Fahad, Baba Huwaila dariya take harda hawaye shi kansa Jamilu duk yanda ya kai ga tsuke fuska da sai da ya murmusa sannan ya kaiwa Indo rankwashi yace.
Sheɗaniya shakiyya wato shiyasa naga rigata ajikinki, waye yace ki ɗaukarmun kaya? Wato kece kika sa Maigari zugewa har ya fara maidawa da marayu kayansu, gaskiya na yarda Indo ke sarƙa ce ni kinfara bani tsoro ma wallahi"
Murmushi Indo tayi sannan ta yakice hijabin jikinta ta ajiye, gaba ɗaya ta sharɓa uban gumi Jamilu ne ya fice daga ɗakina yana ƙara jinjina shu'umanci irin na Indo.
Indo tare da Baba Huwaila suka wuce cen É—akinta tana tafe tana dariya.
*A CEN GIDAN MAIGARI*
Fahad na zaune yana nazarin yanda zaiyi ya ɓullowa lamarin yarinyar nan dan ya lura abin nata da rainin hankali, murmushi yayi lokacin da ya kalli takalmin ya tuna gadar zaren da zai kulla mata.
Fahad tashi yayi ya fita tsakar gida yana zarya kamar mai neman wani abu, daga ƙofar ɗaki ya hango Maigari na leƙowa cikin zuciyarsa dariya ce ta kamashi, Maigari ta maza yayi ya zuro kai ya cewa Fahad.
" Kai Fahad bazaka koma ɗaki ba sai fatakwar nan ta kuma dawowa ko? " Fahad haushi ne ya kamashi ganin duk girman Maigari amma wai ƙaramar yarinya tana neman raina masa hankali, ɗaki ya shige abinsa ya bar Maigari yana bin bayansa da kallo.
*WASHEGARI*
Bayan gari ya waye Fahad ya samu Maigari bayan aun gaisa yace, " Kawu dama inasan anjima atara mun mutanen garin nan akwai abinda nake sanyi amma bana buƙatar atuhumeni saboda na ganno sirrin fatalwar da take zuwa tana tsoratar da kai "
A zabure Maigari ya miƙe tsaye yace, " Kai ɗan nema kar kazo ina zaman zamana ka jazamun masifa, wallahi ka fitar sabgar Fatalwar nan dan na lura ku ƴan birni kanku rawa yake"
Fahad ɗauke kai gefe yayi bai tankawa Maigari ba har ya gama maganganunsa ya ƙara gaba.
Bayan wani lokaci Maigari ne yasa su Ado suka dinga yawo suna ƙara gayyatar mutane bayan sallar Azahar, kowa da abinda yake faɗa sai dai mutane da dama ba wanda ya nuna goyon bayansa ga zuwa gurin taron.
Bayan wasu daga cikin tsararun mutane sun taru Fahad ne tsaye fuska ba walwala ya kallesu yana sallama kamar me raÉ—a, da zumuÉ—i suka amsa masa suna sauraron ji daga gareshi, sai da ya É—auki Æ´an mintuna sannan ya fara magana.