Sashe 64
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jamilu tun bayan da aka ɗaura aurensa da Indo Baba Huwaila da ke gurinsa, sai a lokacin hankalinta ya kwanta. A lokacin Jamilu bacci yake sakamakon allurar baccin da akayi masa, bayan kamar awa biyu da ɗaurin auren buɗe idonsa ya yi, idanunsa sun rine jawur jiki ba ƙwari ya ɗau hannu, ya dafa saitin zuciyarsa da yaji tana yi masa wani irin zugi, idanunsa ne suka ciko da ƙwallah ya buɗe baki ya fara magana dukda muryarsa bata fita sosai. "Baba Huwaila wannan ciwon nawa bazai barni, gani nake kamar rayuwata ta zo..." da sauri Baba Huwaila ta katse shi, "A'a Jamilu ciwonka na tashi ne da yardar Allah, ka kwantar da hankalinka Indo ta zama mallakinka matarka ce halak malak" dukda jikinsa ba ƙwari hakan bai hanashi yunƙurin miƙewa ba, cikin mamaki ya ce, "Da gaske Baba Huwaila?" murmushi Baba Huwaila tayi ta ce, "Da gaske nake Ɗan Jamiluwana" shiru yayi kamar me nazari sai ya ce, "Dan Allah Baba Huwaila karki gayamun haka saboda ciwon da kika ga ina ciki" Baba Huwaila ta ce, "Kasan ni kaifi ɗaya ce Jamilu, bazan gaya maka abinda ba haka yake ba, yanzu haka ranar Laraba iyayenta suka ce zasu kawo ta, gobe talata zasu zo jere mahaifinta ya baka kyautar gida ku zauna a ciki."
A zabure Jamilu ya zuro ƙafafuwansa saura kaɗan ya cire ledar ƙarin ruwan da ake sa masa, a dai-dai wannan lokacin Alhaji ɗan wajen Baba Huwaila ya shigo, da murnarsa ya ƙaraso ganin Jamilu a zaune, Baba Huwaila ce ta yi masa bayanin dalilin tashinsa, nan suka shiga yi masa tsiya suna dariya. Tun daga ranar jikin Jamilu yake ƙara samun sauki, hatta likitocin da suke kula da lafiyarsa hakan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba.
Su Mommy kai tsaye gidan Alhaji suka sauka lokacin Baba Huwaila na gida, ba ita take zaune da Jamilu a asibiti ba. Tarba akayi musu ta sha tara ta arziki cikin farin ciki dangin Mahaifiyar Jamilu dana mahaifin Jamilu suka karɓe su, gidan su Baba Huwaila cike yake da ƴan uwa kamar dama ansan da bikin Jamilun, Su Mommy damƙa Indo sukayi a hannun Baba Huwaila kafin Jamilu ya ƙara warware su tare a gidansu.
Su Mommy basu wani jima ba bayan sun ci abinci, suka yiwa su Baba Huwaila sallama suka wuce gida. Lokacin da zasu tafi Indo ba ƙaramin kuka tayi ba amma duk mutanen gurin babu wacce ta kawo komai a ranta, saboda yawanci haka yake faruwa bisa ga al'adar malam bahaushe.
Washegari ƴan uwa kowa ya kama gabansa gida ya rage daga, Baba Huwaila, Indo matar Alhaji da ƴaƴansa, a ranar ne Baba Huwaila ta shirya ta sa Indo ma ta shirya akan zasu je Asibiti ta duba jikin Jamilu, Indo kamar zatayi magana ta fasa dan gani take bazata iya musantawa Baba Huwaila ba, dan babu wani abu data nunawa Baba Huwaila hasalima wata irin kunyarta take ji, shiryawa tayi tsab cikin doguwar rigar atamfa, ta ɗauko hijabinta coffee ta saka ba ƙaramin kyau yayi mata ba. Ga duk wanda ya fahimceta zai fahimci zallar damuwar dake tattare da Indo, hannunta ɗauke da flask suka ƙarasa asibitin ƙirjinta sai dukan uku-uku yake, Baba Huwaila ce a gaba tana biye da ita har suka shiga cikin ɗakin, tana shiga ɗakin idanunta suka sarƙe da juna, faɗuwar gabanta ce ta tsananta take ta sunkuyar da idanta ƙasa ta nemi kujera ta zauna, Baba Huwaila ce ta ce, "To Jamilu ga matarka na kawo maka ta duba ka" kusan lokaci ɗaya suka ɗago da kansu suna kallon juna, wanda da alama kowannensu mamakin jin kalaman Baba Huwaila yayi, a sanyaye Indo ta janye idonta cikin zuciyarta tana maimaita ni Indo wai nice matar Jamilu..." bata ƙarasa tunanin ba Baba Huwaila ta katse ta, "Jamilu ina kawunka ne?" Jamilu da har zuwa lokacin idanunsa na kan Indo ya ce, "Ya fita siyan kati" Baba Huwaila miƙewa tayi ta ce, "Indo ga abinci nan ki bawa mijinki yanzu Allah ya hutar dani, bari naje na duba shi a waje ina zuwa" Baba Huwaila ta ƙarasa maganar tana yin hanyar fita.
Bayan ta fita shiru ne ya biyo baya Indo ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa ya ce, "Ayusher ba magana?" a hankali ta ɗago idanunta ta ce, "Ina kwana ya jiki?" murmushi yayi yace, "Lafiya ƙalau da sauƙi" shiru suka ƙarayi ya ce, "Yunwa nake ji" Indo bata amsa ba ta miƙe tana tattare hijabinta ta fara zuba masa a plate, kujerarta ta janyo bakin gadon ta zauna ta fara ɗiban abincin zata miƙa masa. Girgiza mata kai yayi sam bata fahimci me yake nufi ba, kallan gefen sa yayi ya ƙara mayar da idanunsa gareta, ta fahimci abinda yake nufi sarai sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa ya ce, "Nan zaki dawo ki zauna Baba Huwaila anan take zama tana bani a baki" ya faɗa cikin shagwaɓa kamar wani ƙaramin yaro.
Tsam Indo ta miƙe ta koma cen kan gadon tana ɗan ɗari-ɗari, daga ɗan nesa dashi ta zauna ta miƙo masa. Ƙara noƙewa yayi badan ta so ba ta ƙara matsowa kusa da shi, ta kai masa cokalin saitin bakinsa. Buɗe baki yayi ya karɓa tana ƙoƙa ƙara ɗebo wani abincin ya riƙo hannunta, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da Jamilu ya ɗago ya kalleta, a hankalin ya sunkuyo saitin fuskarta har suna jin numfashin juna, zuciyarta banda lugude babu abinda take yi.
KWANA BIYU KUN JINI SHIRU WALLAHI NEPA NE SAI A HANKALI YAUMA ƘUƘEWA NAYI, SAM BANSO LITTAFIN NAN ZAI SHIGA WANI WATAN BA, AMMA BA YADDA NA IYA KANA NAKA ALLAH NA NASHI. NAGODE SOSAI DA KULAWARKUâ¤ï¸
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[01/10, 19:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_Ina masoyan Real eeshow na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna *KARAGAR MULKI* cikin farashi mafi sauƙi #300 ta wannan account number 2411022356 aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko transfer credit Mtn ko Airtel ta wa'innan numbers ɗin 08108362334 & 08087971440 sena jiku._
95&96
Sun jima a haka sannan Jamilu ya motsa bakinsa ya fara magana, "Ayusher!" cikin wani irin yanayi ta ɗago ta kalleshi ta kuma sauke idanunta ƙasa, Jamilu ya cigaba da cewa, "Dan Allah kiyi haƙuri" idanun Indo ne suka fara cikowa da ƙwalla ta tsinkayi muryarsa yana cewa, "Nasan zafin rabuwa da masoyi haka nasan bakya so na amma dan Allah kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara" hawayen da ke maƙale a idanunta ne suka sakko, ji tayi kamar Jamilu ya famo mata wani tsohon gyambo dake cikin zuciyarta, yana shirin magana ta ɗebo abinci zata miƙa masa ya ce, "Insha Allah zan riƙe amanarki hannu bibbiyu zakiyi alfahari dani" bata tanka ba kuma bazata tanka masa ba ta kuma miƙa masa abincin saitin bakinsa ya ƙarɓa, daga nan babu wanda ya kuma tankawa kowa da wata kalma haka ta cigaba da bashi abinci yana ci har ya ƙoshi, ruwan tea ta haɗa ta miƙa masa ya karɓa yana sha, ta koma cen kujerarta ta farko ta zauna ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta.
Jamilu mamakin shirun Indo yake ta gefe ɗaya kuma yana alaƙanta hakan da rashin walwala, musamman idan ya tuna Indo bashi take so ba. Babu jimawa Baba Huwaila ta shigo ɗakin ganin Jamilu yaci abincin sosai murna ta kamata, zama tayi ta ce, "Jamilu yau da yake Indo ce ta baka abinci har ka cinye tas amma da nice da tuni kananan kana mun sanabe, ashe dama ni kakewa wannan sanaben yo tunda ka kwanta ciwo kaci abinci me yawa kamar wannan?" Jamilu yace, "Wallahi abincin ne yayi daɗi Baba Huwaila kuma Ayusher a hankali take bani" Baba Huwaila kallansa tayi ta juya ta kalli Indo bakina sake ta ce, "Oh! Yau naga sanabe da kitifi irin na ƴaƴan zamani, yau Indon kake cewa wata Ayusher? Au Jamilu dama ka iya tausasa Kalamai haka bansani ba, da ka dinga azabtar da yarinyar nan" Jamilu kunya yaji sosai ita kanta Indo sai da taji kunya Baba Huwaila ta lura da haka ta ce, "Au Indo yau ni kike jin kunya? Kai jama'a Allah ya kawo zamani wane dare ne jemage be gani ba" Indo ganin idan ta cigaba da kunyar Baba Huwaila ta dinga mata tsiya, shagwaɓewa tayi ta ce, "Wai Baba Huwaila dama haka kike zuwa ki cikashi da surutu mara lafiya bayasan hayaniya fa" Baba Huwaila ta ce, "Eh to kuma fa maganarki na hanya danma naga jikin nashi yayi kyau ai" daga haka hira suka shiga yi sai yamma liƙis suka wuce gida ita da Baba Huwaila.
Jikin Jamilu ya warke garau sai rashin ƙwarin jiki, ranar juma'a likita ya sallameshi suka koma gida cen ɗakinsa ya sauka. Indo na kwance Baba Huwaila ta ce, "Indo ga ruwan wanka cen na sauke je ki sirkawa Jamilu ki kai masa, ɗakinsa da banɗaki a ciki" Indo badan ta so ba ta miƙe ta ɗauki bokiti ta sirkawa Jamilu ruwa ta shiga ɗakinsa da sallama, daga bakin ƙofa ta tsaya ta ce ga ruwan wankanka nan" tana shirin juyawa yace, "Kice Baba Huwaila ta zo ta jai mun banɗakin" ta fahim inda maganar ta dosa dan haka ta watsa masa wani kallo, duk abinda yaga tayi tana masa ne albarkacin idon Baba Huwaila dan tana matuƙar jin nauyinta, da sauri taje ta ajiye masa bokitin a banɗakin ta fito.
Tun daga ranar babu wani abu da yake haɗashi da Indo idan ba kawo abinci ko kai ruwan wanka ba, gaisuwa ma idan ba agaban Baba Huwaila ba bata gaisheshi. Baba Huwaila sai ƴan jiƙe-jiƙe take mata tana bata wani tasha da daɗi wani kuma har sai sunyi faɗa take karɓa ta sha, satinsa ɗaya da dawowa Jamilu ya murmure hatta ramar da yayi duk ya cicciko, babu inda baya zuwa ya samu sauƙi sosai.