← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 76

Sashe 33

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lubna ba ƙaramin tsorata tayi da Indo ba, abin da ya hanata guduwa rashin ƙwarin jikin da ƙarancin numfashi, tana jin ta fara daidaita ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin a guje, bata tsaya ko ina ba sai cen falon Momma lokacin Daddy ya koma nashi falon.
A hargitse Lubna ta shiga falon tana haki hannu riƙe da wuya, tun kafin su tambayeta ta fara magana, "Momma wallahi zata kashe ni ba zan ƙara kwana a ɗakin ba wallahi kasheni zata yi" da sauri Momma ta ce, "Wace zata kashe ki" da sauri Lubna ta ce, "Humaira ce wuya na ta shaƙe mun" zaro ido sukayi suna kallan wuyan Lubna da yayi ja ga shatin hannun Indo a jiki, Yaseer ne ya shigo ya riski maganar da sukeyi ya ce, "What? Yarinyar nan tana da hankali kuwa?" Mommy ta ce, "Kafin mu yanke hukunci me ya haɗaku da ita" shiru Lubna tayi daga baya kuma ta fara kame-kame" Yaseer har ya juya zai fita Momma ta ce ya je ya kira mata Indo, hakan daɗi yayi masa saboda shima dama gurun nata zai je, yadda Lubna ta barota haka yaje ya sameta . Yana shiga daga bakin ƙofa ya ce, "Saboda ɗan uwana ya tona asirinki shine zaki huce akan ƙanwata? Kar kiga ina bata rashin gaskiya idan kukayi faɗa badan bana ƙaunarta bane, ina ƙaunar ta fiye da yadda kike tsammani saboda ita ɗin ƴar uwata ne ta jini, duk yadda kike tunanin kanki agurina baki kaita ba" Maganganun Yaseer ta yake furtawa dai-dai suke da da saukar guduma a tsakiya kan Indo, kalmar da tafi tsaya mata arai, "Ina ƙaunarta fiye da yadda kike tsammani saboda ita ɗin ƴar uwata ce ta jini, duk yadda kike tsammanin kanki a gurina baki kaita ba!" wani irin abu ne mai nauyi da ɓacin rai ne ya turniƙe zuciyarta take taji wani irin hawaye mai zafi na zuba daga idanunta, ɗauke kansa gefe yayi ya ci gaba da cewa, "Ka tashi kije Momma na san ganinki idan kin ga dama" yana kawo wa nan ya fice daga ɗakin.
Indo kifewa tayi ta kuma rushewa da matsanancin kuka sai da tayi mai isarta, sannan ta fice zuwa kiran da Momma take mata. Fuskarta tayi jawura idanuwanta sun kumbura, gefe ta samu ta zaune murya a dakushe ta ce, "Momma gani" Momma ba ƙaramin tausayin Indo taji ba amma tasan duk irin laifin da Lubna zatayi mata bai kamaci ta shaƙe wuyanta ba saboda guri ne mai matuƙar hatsari, Mommy ce ta katsewa Momma tunanin da take yi ta ce, "Humaira me ya haɗaku da yayarki Lubna" Indo da zuciyarta ta gama bushewa ta ce, "Ba komai Mommy" Momma ma tambayarta tayi amma gabaɗaya babu wanda ta gayawa abin da ya faru, duk yadda sukayi da Indo sai dai tace musu babu komai, daga haka faɗa Momma tayi musu sannan ta ce su tashi su bata guri, a tsorace Lubna ta bi bayan Indo tana fargabar karta ƙara yi mata abinda tayi mata ɗazu.

Indo ji take zuciyarta kamar ana hura mata wuta, tana shiga ɗakinsu hijabinta ta ɗauko ta saka ta fice daga ɓangarensu Lubna bata iya furta mata komai ba sai binta da tayi da ido, Indo kai tsaye bakin gate ta nufa tana zuwa ta buɗe kofa ta fice daga gidan, mai gadin baiyi gigin hanata ba saboda yasan matsayin Indo a gidan sai dai mamakinsa ɗaya da ya ga ta fita ita kaɗai kuma a ƙafa, tafiya take tana jefa ƙafarta ko kallan gabanta batayi saboda ɓacin rai. Har ta kusa zuwa titi taga ansha gabanta da mota ɗagowa tayi da niyyar masifa ta hango shi zaune cikin mota fuska ba walwala. Idanunsa na kallan titi ya ce, "Ki shiga mu koma gida" cikin tsiwa Indo ta ce, "Bazan koma ba" tana faɗa ta ci gaba da tafiya da sauri ya kuma shan gabanta ya ce, "Idan baki shiga ta lallami ba zaki shiga ta ƙarfin tsiy" a fusace Indo ta ce, "Idan na koma me zanyi maka? Wai me kake so dani ne ka barni na tafi mana" Fahad murmushin takaici yayi ya ce, "Alƙawari na ɗaukarwa kaina sai na kaiki har garinku badan haka ba da duk inda zaki je bazan hanaki ba, idan Lagos ki nufa bazan hanaki ba nan ne dai ƙarshen garuruwan da riƙaƙƙun ƴan duniya suke zuwa, ko ki shigo ko na ɗauke ki na saka ki" guntun tsaki Indo tayi ta ci gaba da tafiya bata tanka masa ba.
Fahad fitowa yayi daga mota ya fisgi hannun Indo ya buɗe mota ya wurga a ciki kamar wata kayan wanki, shiga motar shima yayi ya bata wuta suka wuce gida, horn yake kamar zai tashi sama da sauri mai gadin ya buɗe masa suka shiga ciki, yana parking tun bai ƙarasa ba Indo ta fito fuska a tsuke, yana fitowa Yaseer yana ƙarasowa gurin ya ce, "Brother daga ina kuke?" Fahad ya nuna Indo a yatsine ya ce, "Wannan abar ce zata gudu na dawo da ita" Yaseer kallan Indo yayi cikin jin haushi ya ce, "Ashe dama haka halinki yake ban sani ba? Saboda su Momma sunyi miki faɗa shine zaki gudu, tir da wannan ɗabi'ar taki ashe Allah ya taimake da na kwasarwa kaina ƙaddara" ƙarasa kalaman Yaseer yayi daidai da ɗagowar kan Indo da wata irin murya ta ce, "ƘADDARA? Ya Yaseer ni kake kira da ƙaddara" a zafafe ya ce, "Yadda kunnenki yaji" yana gama faɗa ya juya ya koma ɓangarensa. Indo cikin ƙunan rai ta itama ta juya ta wuce sashen su.

Indo saboda ɓacin rai yadda ta ga rana haka ta ga dare kwana tayi tana kuka haɗe da dana sanin zuwanta gidansu Yaseer, a ɓangaren ɗaya kuma tana jin wani irin abun game da Yaseer sai dai ta rasa gane wane irin abu ne, tabbas tana jin haushin yadda Lubna take shigewa Yaseer amma ta rasa dalili. Ƙarin takaici da haka ra faru har yana ƙara nuna mata muhimmancin Lubna a gurinsa. A daren ranar Daddy ya sanarwa da Momma akan su shirya, da safe zasu tafi garin Kura domin miƙa Indo hannun iyayenta da basu haƙuri akan tahowar da tayi ba tare da izininsu ba.

Washegari da safe gabaɗaya suka shirya Indo tunda taji maganar tafiyarsu gabanta yake faɗuwa, ɗaurewa tayi tana ambaton sunan Allah a zuciyarta. Mota biyu suka ɗauka Daddy, Momma, Mommy, a mota ɗaya Fahad na driving ɗinsu, Lubna, Indo suna mota ɗaya Yaseer na Driving ɗinsu. Lubna na zaune a gaban mota sai zabga surutu take da iyayi, Yaseer ban da ummm ba abinda yake amsa mata da shi, Indo kuwa zabga tagumi tayi cikin tunani tana kallan titi. Yaseer da ya gaji da surutun Lubna parking yayi cikin tsukewar fuska ya ce, "Lubna tashi ki koma baya" turo baki tayi ta ce, "Yaya kayi haƙuri dan Allah" tsawa ya guga mata ya ce, "Ki fice ki koma baya nace ko, yarinya sai shegen surutu kamar aku fice mun" Lubna jiki ba ƙwari ta fita ta koma baya haushi fal zuciyarta, saboda wannan ba ƙaramin wulaƙanci Yaseer yayi mata ba, haka ta dinga cika tana batsewa a fakaice tana watsawa Indo harara.

Tun daren ranar da zasu je Kura Mommy ta kira wayar Maigari ta sanar da shi game da zuwansu, duk wani shiri na tarbar. baƙi Maigari ya sa matansa sunyi.

Bayan wasu awanni Motocin su Yaseer suka ƙarasa cikin garin su Indo, suna zuwa ƙofar gidan Maigari yaran garin suka fara dafifin zuwan kallon motar ƴan birni, Indo kallan ƙauyen nasu take tana jin wani irin farinciki a zuciyarta, hawaye ya fara gangarowa daga idanunta, juyawa tayi zata nufi hanyar gidansu da sauri Fahad ya damƙi hannunta yana watsa mata mugun kallo, bata ƙara ƙoƙarin tafiya ba suka ƙarasa cikin gidan. Shinfiɗa akayi musu a ɗakin Maigari cikin murya shi da iyalansa suka tarbi su Mommy. Bayan sun gaisa Maigari ya ƙurawa Indo ido sannan ya ce, "Amma Indo kedai anyi sheɗaniyar yarinya, kamar fitar tusa haka muka nemeki muka rasa, anya kinyiwa Baba Huwaila adalci? Ashe sheɗancinki ba iya taɓin aljanu bane?" Indo harara ta watsa Maigari ta ɗauke kai gefe.

MASHA ALLAH INA GODIYA DA KULAWARKU, CAJINE BANA SAMU SHIYASA KUKA JINI SHIRU, YAU DAI NA CIKA ALƘWARAI🥺🥺🥺🥺 FATAN ALHERI GAREKU.❤️

ALHAMDULILLAH NAYI NASARAR LASHE GASA INA GDY GA ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MASOYA BAZAKU LISSAFU BA ALLAH YA BAR ƘAUNA.❤️

INA JIRAN COMMENTS✋🏻🤠🤚🏻

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[18/08, 18:18] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

61&62
Chapter 33 · 0% Book details