Sashe 39
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ne ya kalli ɗan uwan nasa ba ƙaramin tausayin su yaji ba, amma sai ya danne ya tsuke fuska ya ce, "Khaleel ban tsammani haka daga gareka ba, na ɗauka zaka iya amsa mini tambaya ta, shin zan sami amsar tambayar ta ko kowa?"Alhaji Khaleel russunar da kai ya yi cikin girmamawa ya ce, "Yaya dan Allah kayi haƙuri. Wallahi a duk lokacin da aka ambaci Ƴar mu Aisha sai inkasa controlling ɗin kaina, amma banyi haka saboda wata manufa ba." Murmushi Daddy ya yi ya yana ƙarajin ƙaunar ɗan uwana nasa a zuciyarsa, saboda irin biyayyar da yake masa kamar shi ya haifeshi, kallan Alhaji Khaleel ya yi ya gyaɗa masa kai sannan ya ci gaba da cewa. " Yaya ina tunanin yau dai shekara goma sha shida da haiihuwarta ." Daddy ya gyaɗa kai ya ce, "Ko ka riƙe watannin ta lokacin da muka rasa ta?" Ɗan jim ya yi yana nazari Aunty Safna murya a ɗan dakushe ta ce, "Yaya ko wata biyu bata cika ba. Muna yin arba'in da kwana biyar ne." tana rufe baki hawaye ya ƙara ziraro mata. Alhaji Khaleel ya gyaɗa kai ya ce, "E h tabbas haka ne" Daddy Jakar da ke hannun Momma ya karɓa ya zaro azurfar Indo tare da kayan da aka tsince ta haɗe da wannan tsohon hoton da aka saka mata a pampers. ɗaga musu ya yi ya ce, "A cikin ku ko akwai wanda zai gane waɗannan kayan?" Alhaji Khaleel a zabure ya miƙe, Aunty Safna ma tashi tayi tsaye bakinta na rawa ta fara nuna kayan tana faɗin, "Ka...ka...kayan...Aisha..." bata ƙarasa magana ba ta yanke jiki ta faɗi a gurin. Da sauri su Momma suka yo kanta tare da Maigidanta, Daddy ne ya bata umarni a ɗebo ruwa a zuba mata, ba musu Fahad ya tashi ya ɗebo ruwa aka yayyafa mata. A hankali ta fara buɗe idanunta, jiki babu kwari ta yunƙura ta tashi zaune. Idanunta ne suka ci gaba da zubar da hawaye ta ce, "Yaya dan Allah a ina kuka samo waɗannan kayan? Tabbas nasan akwai babban al'amari dangane da zuwan nan na ku." Daddy ya ce, "Tabbas Safna akwai babban al'amari, kamar yadda kika yi tsammani. Kinga waccen yarinyar?" ya ƙarasa faɗa yana nuna Indo, da ke zaune cen kusa da Baba Huwaila. Sai raba ido take kamar shege a rabon gado. cikin zumuɗu suka amsa masa, Daddy ya ci gaba da cewa, "Allah cikin ikon sa ya bayyana muku ita. A lokacin da kuka cire tsammani da sake sata a cikin idanun ku..." a hanzarce suka katse shi da faɗin, "Yaya kana nufin waccen ƴarmu Aisha ce?" Dadday murmushi ya yi ya ce, "A iya zama na da ku ban taɓa muku irin wannan wasan ba, dan haka yanzu ba wasa nake muku ba tabbas Humaira ƴar ku ce." tun bai ƙarasa rufe baki ba Aunty Safna ta tashi ta ƙarasa gurin Indo. Rungume ta tayi sosai a jikin ta kamar wani zai ƙwace ta, ta rushe da wani irin matsanancin kukan. Duk dakiya da taurin zuciya irinta Indo sai da ta zubda hawaye. Haka su ma mutanen falon gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi tausayin su gabaɗaya ya kama su, Mai gari sai a lokacin ya yi dariya ya ce, "Ja'ira Sarƙa ƴar nema ji yadda tayi luff, kamar kwailar mage" Maigari dariya ya basu sosai saboda dama ahi mutum ne mai barkwanci. Sai a lokacin Alhaji Khaleel ya ƙaraso ya riƙo kafaɗar Indo, ya riƙota suka koma kan kujera. Indo sai raba ido take tana sunne kai kamar mutuniyar kirki.
Lubna sai harara take watsawa Indo a fakaice, Gabaɗaya zuciyar ta a dagule take saboda baƙin cikin ta ɗaya ace wai kusan matsayinsu ɗaya, lokaci-lokaci take furzar da iska tana ƙissima abubuwa acikin zuciyarta.
Alhaji Khaleel ɗaga hannuwa sama ya yi ya ce, "Ya Ubangijin sammai da ƙassai ina godiya da ka nuna mini wannan ranar. Tabbas lamarin Ubangiji daban yake, na jima da fidda ran ganin wannan ranar, sai gashi Ubangiji ya nuna ƙudurarsa. Allah na gode maka, Allah mun gode maka da ka bamu ikon cinye jarrabawar da ka jarabcemu har zuwa wannan ranar." kallan Daddy Aunty Safma ta yi ta ce, "Amma Yaya muna buƙatar ƙarin bayani game da yadda akayi kuka samo Aisha" Daddy nuna Momma yayi ya ce, "Auntynki ita zata fara baki labari. Ina ce kinji labarin wata yarinya da muke riƙewa kwanakin baya?" A tare suka gyaɗa kai.
Momma ce ta gyara zama ta fara basu labarin Indo tun lokacin da suka ganta a ƙofar gidansu, har zuwan su Momma da tafiyar su garin Kura. Zata ci gaba da magana Daddy ya ce, "Momman yara iya nan kaɗai zaki tsaya, saboda nan ne huruminki sauran ki barwa Baba Huwaila. Kinsan Hausawa sun ce waƙa a bakin me ita tafi daɗi." Baba Huwaila sai a lokacin ta yi magana, "Maganar ka haƙƙun haka take, musamman da yake fage ne na Indo, ko ban da murya dole na gyarata ta yadda za'aji daɗin sauraron ta." miƙe ƙafarta tayi saboda tsamin da tayi mata sannan ta fara basu labari tun daga farkon alaƙarsu da Goggo har zuwa rasuwarta, labarin gwagwarmayar da Goggo ta sha da Indo da irin tswangwamar da aka dinga yiwa musu ta basu, saboda tausayinta har zubar mata da ƙwallar sukayi, a taƙaice dai Baba Huwaila babu abin da ɓoye musu game da Indo, har dalilin tafiyar da tayi wanda shi ne silar faɗawarta hannun su Momma. Jikinsu ne ya yi sanyi da haɗe da tausayin Indo mariƙiyarta. Sai kuma yabawa da jinjinawa da suka yi wa Baba Huwaila da Jamilu, musamman da suka ji irin diramar da suke tafkawa tsakanin Indo da Jamilu. Dariya mutanen falon suke sosai banda Fahad, Yaseer da Lubna dan shi kansa Jamilu da ana maimaita abin da ya dinga faruwa a tsakaninsa da Indo abin ba ƙaramin dariya ya bashi ba, sunkuyar da kai ya yi yana murmushi ƙasa-ƙasa. Alhaji Khaleel ne ya yi murmushi ya ce, "To Jamilu ko ƴar gida za'ayi n? Wannan faɗa na ku kamar Tom and Jerry?" Baba Huwaila zuciyar ta fess ta ce, "Ai kuwa da nafi kowa murna" Wani irin abu ne ya tokare zuciyoyin Yaseer miƙewa yayi da niyyar fita Momma ta ce, "Kai ya zakuyi mana juyin mulki tuni Ɗana Yaseer ya sanar mana da buƙatarsa ta auren Humaira ko ba haka ba Daddyn Yara?" Daddy murmushi ya yi ya ce, "Haka ne amma namu ido ne sai wanda Ƴata Humaira ta zaɓa" Indo na jin haka ta sunne kai cikin jikin mahaifiyarta tana jin wani irin matsanancin kunyar su, Jamilu ne ya saci kallanta ba ƙaramin birgeshi tayi ba, amma mamaki yake wai yau Indo ce take jin kunya. Duk garin su babu wanda baisan Indo ba babu wanda take jin Kunya, karshe har Maigari da su Malam Liman.
Mommy ce ta kalli Fahad yake danna waya kamar bai san sunayi ba ta ce, "Ɗana ya ana ta magana kayi shiru." Fuska ba walwala ya ce, "Mommy wannan fagen su ne ni kinsan babu wannan a tsarina" Kamar ya sosowa Mommy abin da yake mata ciwo ta kalli Alhaji Khaleel ta ce, "Daddyn Aseel ina jin fa sai kun fara nemawar ɗana magani nina rasa gane kansa, wai yaron nan ko maganar budurwa bayasan nayi masa. Kuna ji fa yanzu abin da ya faɗa." Daddy ya ce, "Wai Fahad har yanzu kallan ƙaramin yaro kake wa kanka? Yanzu haka fa kana shekara ta talatin ko so kake sai na kaɗa maka ƙararrawa ne?" Indo kamar jira take aikuwa ta kwashe da dariya ta ce, "Kamar gwanjon Ɗan Iya na garin gangare" Maigari ya karɓe zancen da, "Idan bashi da farin jini yazo Kura na haɗa shi da Alawiyya itama ba mashinshini, kunga abinsu fes musha biki" Aikuwa duk inda ɓacin rai yaje Fahad ya kai, kwaɓe fuska ya yi kamar zaiyi kuka ya ce, "Mommy kina jin fa me Yarinyar nan take faɗa, wai har da Kawu ma. Wallahi ko mata na rasa bazan auri ƴar ƙauye ba." ya faɗa kamar me shirin rushewa da kuka.
Hira suka ci gaba dayi gwanin birgewa, Indo daga gurin wannan sai ta koma gurin wannan. Daddy ne kalli ÆŠan uwansa ya ce, "Khaleel ina yaran nan ne banji motsinsu ba?" Alhaji Khaleel ya ce, "Yaya suna Islamiyya amma babu jimawa zaku ji shigowar su" jinjina kai Daddy ya yi ya ci gaba da cewa.
"Khaleel naso na bawa su Baba Huwaila tarihinku. tun daga farko har zuwa ƙarshe amma sai nayi wani tunani. Kamar yadda su Baba Huwaila suka baku labari tiryen-tiryen da bakin su, haka nake so kai ko matar ka ku basu labari game da rayuwarku, har zuwa lokacin da kuka rasa ƴar ku da bayan rabuwar ku da ita."
Alhaji Khaleel ne ya gyara zaman ya fara cewa.
BANDA BAKIN GODE MUKU MASOYA MASU TAMBAYA KWANA BIYU DA KUKA JI NI SHIRU, FATAN ALHERI GAREKU *AMEERA ADAM FANS GROUP* â¤ï¸â¤ï¸ ZUNZURUTUN ƘAUNA GA MUTANENA NA *WATTPAD*â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥° MESSAGE ÆŠIN KU HAR BA ADADI 😂 INA GDY SOSAI DA KULAWAâ¤ï¸ ALHAMDULLAH NA WARTSAKE ALLAH YA ƘARE MU DA LAFIYAðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»
KU SUBURBUÆŠO RUWAN COMMENTS ANJIMA MU TAFI NEXT LEVEL✋ðŸ»ðŸ˜‚🤚ðŸ»
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[09/09, 19:23] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
69&70