Sashe 70
Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jamilu yana hirar ne amma gabaɗaya fargabarsa ɗaya idan ya koma me zasu ɗora a gaba shi da Indo, wata zuciyarce tace. "Ka zauna Indo taga makwancinka dama ya lafiyar kura bare taci nama, Indo bata ga makwancinka bama yaya bare kuma ka bada kai bori ya hau" juyawa yayi ya shiga ciki yana zuwa yabi falon da kallo, ko'ina tsaf ta share shi kamar ba falon da aka farke fulillika ba. Motsinta yaji a kitchen a zabure ya juya hangota yayi tana ta mayar da kayan ɗaya bayan ɗaya, mamaki ne ya kamashi idan tana wani abun kamar me aljanu dan ko da za'a ce masa aljanu gareta bazai musa ba, saboda guraren da ta dinga hawa tana sauka a ƙauye.
Komawa yayi kan kujera ya zaune ba jimawa ta fito daga falon hannunta ɗauke da kofin tea guda biyu, fuskarta sai murmushi take idan ka ganta sai ka rantse wani kyakkyawan albishir akayi mata, cen ƙasa gujera ta zaune ta ajiye nata shayin ta miƙa masa nashi sannan ta koma ta zaune, karɓa yayi yana binta da kallon tuhuma bayajin Indo zata iya kashe mutum amma yana tsoron sharrin zuciya karta kaita ga halaka shi. Ajiye kofin shayin yayi yana kallonta bai tanka mata ba, ita kuwa ta ɗauko remote ta kunna kallo tana shan shayi tana kallo. Sakkowa yayi ƙasa ya zauna ya ce, "Ayusher wai meyasa kike wasu irin abubuwa idan kikayi wani abun kamar me aljani..." wani kallo ta watso masa tun bai rufe baki ba ta katse shi. "Bishiyar Bulukiya ce akaina" Jamilu yace, "Ba magana nazo ki gaya mun ba, zuwa nayi muyi magana cikin masalaha. Yanzu kina ganin abinda kikayi ya dace kenan? Kina gani ashe duk ihun neman agajin da nakeyi maƙota na ji na" cikin halin ko'inkula tace, "Kai ka so" Jamilu yace, "Wallahi duk abinda zaki faɗa ba yin kaina bane ina ƙaunarki inasanki soyayyar da bantaɓa yiwa wata ƴa mace ba, Ayusher meyasa bazaki fahimci zallar soyayyar da nake miki ba shin laifine dan na ƙaunace ki? Kuskure dai nasan nayi da tuntuni ban furta miki ba har kika fara soyayya da wani, amma idan kin duba duk wasu alamomi na nuna miki inasanki ina ƙaunarki na tabbata ko Yaseer baya miki soyayyar da nake..." a hargitse ta dakatar da shi tana ɗaga hannunta. "Ya isa dan Allah! ina cikin nishaɗi da farinciki dan Allah karka tarwatsa min ɗan guntun farincikin dana samu yanzu, har inmutu nasan babu namijin da zai so ni ya nuna mun ƙauna da kulawa kamar Yaseer. Jamilu zaman mutum uku kawai nake a gidan saboda sun isa dani ko ba kai ba suka ban wani da ban sani ba, matuƙar umarni ne zan musu biyayya. Ina zaman Baba Huwaila sai iyayena amma banda wannan bana sanka bana ƙaunarka kuma bazan taɓa sanka ba." ta ƙarasa faɗa hawaye na bin fuskarta. A duk lokacin da zata gaya masa irin waɗannan maganganun suna damunsa amma yana mata uzuri saboda yadda silar aurensu ta kasance, sai dai wannan karan ba ƙaramin ɗacin magangnunta yaji ba, kallan fuskarta yayi yana san haɗa ƙwayar idonsa da nata dan ya tabbatar da abinda ta faɗa cikin ƙwayar idont, amma hakan ya gagara, haɗiyar yawu yayi me ɗaki ya tashi ya fice daga gidan gabaɗaya.
Tun daga wannan lokacin Jamilu yake ƙoƙarin ganin ya kyautata mata koda bazata soshi ba, satinsu biyu fa tarewa ya koma bakin aikinsa hakan ne yasa zamansa a gida yayi ƙaranci idan ba weekend ba, duk yamma idan zai dawo sai ya tahowa da Indo wani abun ɗan na motsa baki musamman kayan zaƙi da yake yasan tafi mu'amala dasu. Indo ta leƙa gidan maƙotansu baifi gida biyar ta shiga ba ta gabatar musu da kanta, yawancinsu yaran matane daga me haihuwa ɗaya sai me haihuwa biyu. Wata maƙociyarsu ce da ake kira da Maman Hibban ita ce me ƴaƴa uku kuma da alama duk ta ɗan girmesu, cikin sakin fuska suka gaggaisa bata jima ba ta koma gidanta. Bayan kwana biyu suma da kaɗan da kaɗan suka shigar mata daga haka babu wanda ya kuma shiga gidan wani a cikinsu, ahaka rayuwa ta gangara dasu Indo har ta shafe wata huɗu a gidan Jamilu, ba yadda batayi da Jamilu ba akan ya barta taje Kaduna amma fir yaƙi, gidan Baba Huwaila ma gabaɗaya zuwanta uku, gidansu Mommy ma zuwanta biyu kuma duk tare da Jamilu suke zuwa ya kaita da yamma, wajen ƙarfe tara na dare yaje ya ɗaukota su wace gida duk zuwan da sukeyi basu taɓa haɗuwa da Fahad ba, tayi masa mitar ya barta taje Kaduna da Abuja amma ya hanata tun abin na damunta har ya daina damunta ta saki jiki ta cigaba da rayuwa. Sai dai har zuwa waɗannan watannin babu wani zama me daɗi da sukeyi, gabaɗaya Jamilu ya rame ya bushe idan ka ganshi sai ka rantse jinya yasha, duk lokacin da zaije gun Baba Huwaila sai ta sashi gaba da tambayar abinda yake damunsa amma ya ce mata babu komai har ta daina tambayarsa.
A Æangaren Yaseer duk yadda yaso yakice soyayyar Indo abun ya gagara, sai dai a hankali yake jin yawan tunaninta na raguwa daga zuciyarsa, kuma har lokacin bai daina miÆ™awa Ubangijin kukansa akan ya yaye masa matsanancin halin da yake ciki ba, ana cikin haka Lubna da Æ™anwarta Ihsan suka dawo gidan su Yaseer yayyansu Lubna suka koma gidansu Indo, kasancewar Mahaifinsu yayi tafiya gida ba kowa. Zaman Lubna a gidan Momma a hankali ta fara shiga rayuwarsa dukda da farko yana shareta, amma bata gaza ba har ya fara sauraronta suna zama suna hira, lokaci-lokaci har É—aukanta yake suna zuwa shopping.
Shima Fahad ya warware babu wani ciwo da yake damunsa sai dai har lokacin bai mayar da jikinsa ba. Fahima ƴar Cousin ɗin Daddynsa ce tasu tazo ɗaya da Fahad sosai, har mamaki take yadda mutane suke faɗar murɗaɗɗen halin Fahad, ya ɗauke ta kamar ƙawarsa itama haka tana da ilimin addini dana boko dai-dai misali, ta karanci fannin lafiya tana aiki a wani ƙaramin asibitin kuɗi anan garin Kano, Mommy ce ta samu Daddynsu da maganar Fahad da Fahima shi kansa Daddy yaji daɗi amma sai ya tambayeta ko yara suna san juna, Mommy tace. "Daddyn yara naga yaran nan sun shaƙu amincewa soyayyar su bazai wuya ba" Daddy yace, "Haka ne Allah ya tabbatar mana da alheri, zan samu Fahad da maganar idan sun daidaita kansu sai na samu Sunusi da maganar" Mommy ba ƙaramin daɗi taji ba cikin zuciyarta take addu'ar Allah ya daidaita tsakanin Fahad da Fahima.
Jamilu na zaune a office ɗin malamai, Malam Isa ya kalleshi yace, "Abokina duk wanda ya sanka a da, da yanzu zai fahimci zallar rashin kwanciyar hankalin da kake ciki, kaga yadda ka rame ka lalace kuwa? Na tambayeka har na gaji amma kace babu abinda yake damunka yanzu rayuwa zata yuwu haka? Ka tuna fa ciwon zuciya ya taɓa barazanar kamaka amma kullin baka da aiki sai tunani har rafkanwar shiga ajin ɗalibai kake" Jamilu ya ce, "Malam Isa ina cikin damuwa wallahi" Isa yace, "Malam Jamilu ai ko baka faɗa ba wanda ya sanka kallo ɗaya zai ma ya fahimci haka" Jamilu yace, "Malam Isa nayi aure amma aurena tattare yake da ƙalubale da tashin hankali, hatta girki sai ta ga dama take mun har na fara wani tunani saboda karna cutar da ƴar mutane, tunda bansan halin da zan jefa ta ba idan ni nayi haƙuri da haƙƙina ina azumi ita fa? Kaga kar azo ayi abunda babu daɗi saboda babu wani farinciki da muke ciki daga ni har ita a cikin gidan nan..." gabaɗaya Jamilu ya kwashe labarin sa da Indo tun daga farko har ƙarshe har irin ƴar tsamar da sukeyi da ita a ƙauye da bayan tariyarsu. Malam Isa murmushi yayi yace, "Malam Jamilu wannan ƙaramar matsala ce ai" da mamaki yace. "Bangane ba Malam Isa"
Malam Isa yace, "Wallahi ita kanta tana sanka kuma zaka gaya mun nan gaba indai ka ɗau shawarar da zan baka, kasan meyasa wancen yafi tafiya da zuciyarta, kasan macen tunaninta kamar na yara yake dan haka kaima sai ka mayar da kanka kamar ƙaramin yaro, ya siye zuciyarta da kulawa tarairaiya, daɗin kalamai kasan mata ba wuya ka saye zuciyarsu da wannan, kuma ka dinga ɗaukanta lokaci-lokaci kuna fita yawon shaƙatawa a hankali zaka ga ta fara rage duk abubuwan nan da take yi maka, amma wani hanzari ba gudu ba" da sauri Jamilu ya Kalli Malam Isa zaiyi magana Malam Isa ya cigaba da cewa.