← Book details Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 76

Sashe 16

Indo Sarƙa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Baba Huwaila bakyajin waƙar da suke mun kuma kawai sai insaka musu ido su rainani wallahi ni ba wanda ya isa ya gayamun ba daɗi " Baba Huwaila ƙwafa tayi ta ce, " Ai shikenan Indo hausawa suka ce Jiki magayi tunda haka kika ga yafi miki " Indo ɗauke kai gefe tayi tana ƙara jin ba daɗi a zuciyarta, tunani kawai take ta wace hanya zata rama cin kashin da Jamilu yayi mata a idanun yara.

BAYAN WANI LOKACI

Baba Huwaila ce tsaye agurun Indo tana mata magana cikin lallashi, " Yanzu Indo haka zaki zauna da yunwa tun ɗazu kici abinci kinƙi, wa yace miki ana zuciya da abinci? " Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Baba Huwaila wallahi ni bazanci abincin nan na rantse kuma bazan karya rantsuwa ta ba " Jamilu ne ya shigo gidan hannunsa ɗauke da ledar Uniform ɗin indo ya riski maganar da sukeyi da Baba Huwaila.

Uffan bai furta ba ya wurgawa Indo ledar Uniforma ɗinta ya ce, " Gashi nan sai ki kwana da shirinki a gobe insha Allah zan gama miki komai..." yana cikin magana sallamar da akeyi a ƙofar gida ce ta katse shi, cikin ƙosawa yasa hannu ya dafe goshinsa yana furta, " Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un " yana nan tsaye yaji ankuma rafka sallama ana cewa.

" Salamu Alaikum idan ba'a amsa ba zamu shigo da kanmu, aike ne daga fadar Maigari yace ko aka ne mu É—auko yarinyar nan Indo "

Cikin takaici Jamilu ya ce, " Basai kun shigo ba zamuje fadar da kanmu " Jamilu na gama magana ya kalli Indo fuska a murtuke ya ce, " Sai ki tashi mu tafi baƙar munafuka kike sinne kai ƙasa kamar mutuniyar kirki " Shiru Indo tayi bata tanka masa ba ta yunƙura ta tashi jikinta na mata tsami, Indo da Jamilu suna gaba Baba Huwaila na biye dasu a baya har suka ƙarasa fadar Maigari.

Kamar ɗazu ne yanzu ma fadar cike take sai dai yanzu fuskoki gaba ɗaya a tamke suke babu alamun wasa har shi kansa Maigari, da ƙarfin gaske Jamilu ya ƙarasa ya dunƙufar da Indo agaban Maigari ya koma gefe ya zaune.Maigari tun daga ƙasa ya fara ƙarewa Indo kallo sai da ya kai har tsakiyar kanta sannan ya ce, " Gaki ƴar ƙanƙanuwa wacce batafi na haɗeki da hannuwa na biyu na karye ki ba amma sai sheɗanci da hatsabibanci fal kanki, mu zaki kawowa iya shege ko? Sarƙa iskancinki har kaina yazo da sauran mutanena kamar ni da girmana da darajata zakiyi aljanun ƙarya ki dinga duka ko? Yanzu kin fashe kan ɗan gidan Shafa laifin me yayu miki? Sarƙa raini ne yasa kike haka ko iskanci ne? " Indo shiru tayi kamar bataji mai yace ba sai da ya buga mata tsawa sannan ta ce, " Ranka shi daɗe dama ni kullin ai ba'a bani dama ta ne amma ai ansan haka kawai bazan fasa masa kai a banza ba da wani dalili ba, kuma ai nima..." Tsawa Maigari ya ƙara buga mata ya ce, " Ke akwai abokin wasanki anan gurin? Rashin kunya nace kiyi mana ba tambayarki nayi ba? " ɗauke kai gefe Indo tayi ta ce, " Aini ba rashin kunya nayi ba bayani kawai nakeyi..."

Maigari ne ya katseta da cewar, " Ya isa haka, Baba Huwaila zaku kai yaron nan kyamis sannan akwai aikin horo da za'a bawa Indo tayi na tsawon kwana bakwai tun safe har yamma, kullin zata dinga share fadar nan sau biyu a rana kuma ruwan gidana kullin sai É—ebo ta cika ko'ina na tsawon mako guda, Zaki dinga É—ebowa Mati É—an wajen Shafa ruwan wanka kullin kina yiwa uwarsa cefane ke duk aikin da Mati yakeyi zuwa nan da sati guda " Baba Huwaila ce ta kalli Maigari cikin sanyin murya ta ce.

" Allah ya baka yawan rai munji duk bayananka zamu biya duk abinda za'a kashe amma ataimaka a ragewa Indo waÉ—annan ayyukan sunyi mata yawa ko a gida bana bata rabin wannan aikin " Shafa da ke gefe tana cika tana batsewa tayi karaf ta ce, " Eh, da yake ba É—anki ko Æ´arki aka jiwa ciwo ba ko? Dole ki nemar mata rangwame yanzu da antsokanewa ÆŠana idonwa gari ya waya? "

Maigari fuska ba walwala ya ce, " A dakata banasan cecekuce,Indo taci mutumcin masarauta dole mu hukuntata saboda masu tunani irin nata su hankalta, dole tayi abubuwan dana lissafa mata kuma Allah sa inkuma jin wani ya kawo mun ƙararta,Akwai Bulala goma da Ɗan Jummai zaiyi miki yanzu kai Ɗan Jumma a hukuntata " Maigari gama Ɗan Jummai ya taso ya fara zubawa Indo bulala amma ko motsin kirki batayi bare tayi Ihu, dan a ganinta idan ta kuma kuka agaban mutane da sauran yara ba ƙaramin raini zai ja mata ba, Hatta Jamliu yayi mamakin jarumtar da Indo tayi saboda kowa na faɗar bulalar Ɗan Jummai musamman waɗanda suka taɓa laifi aka hukuntasu, manya ma kuka sukewa bulalar Ɗan Jummai bare yara, idanun Indo ya kaɗa yayi jawur amma ko ɗigon ƙwalla babu a idonta.

Maigari gyara zama yayi ya cigaba da cewa, " Ga mai irin tunanin Indo wannan ya zama izina agurinsa, idan muka samu waninya aikata makamancin haka nasa hukuncin sai ya ninka nata, Indo zata fara gudanar da aikinta daga gobe da ƙarfe bakwai na safe saɓawa umarninmu hukunci ne mai tsanani, idan babu mai magana zaku iya tafiya mun sallami kowa "

Jamilu ne ya É—aga hannu alamar yana da magana, Maigari gyaÉ—a masa kai yayi sannan Jamilu ya ce, " Allah baka yawan rai ba wai ina nema mata rangwamen aikin bane, amma ya zatayi da zuwa makaranta? " Mai gari wani kallo ya watsawa Jamilu sannan ya ce.

" Duk faɗin garin nan kowa yasan ya zuwa makarantar Indo yake, idan taje sau ɗaya sai ta shafe wata bata koma ba, saboda min bata horo za'a ɓullo mana da haka? " Jamilu furzar da iska mai zafi yayi ya ce, " Wata makarantar zan canja mata da zan mayar da ita makarantar Rimaye inda nake koyarwa yanzu haka har Uniform na ɗinka mata " Maigari ya ce, " Ai abun yazo da sauƙi tunda ma bata fara zuwa ba sai ka bari idam ta kammala aikin sai ta fara zuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne,idan babu mai wata maganar xaku iya tafiya " sannu a hankali mutanen gurin duk suka watse.

Baba Huwaila,Jamilu,Indo da au Shafa tarkatawa sukayi suka wuce chemist domin duba kan Mati, duk abinda akayi masa Jamilu ne ya biya ana gama duba yaron Baba Huwaila da Indo sukayi gida Jamilu ko ta kansu baibi ba ya wuce sabgar gabansa.

WASHEGARI
Tun bayan sallar asuba Indo bata koma ba ita kaɗai take ta saƙa da warware abinda zata shukawa Jamilu dan ta huce abinda yayi mata kafin ta koma kansu Maigari, wata dabara ce ta faɗo mata saboda jin daɗin shawarar data yanke har sai da ta dinga ƙyaƙyata dariya ita kaɗai, sai da tayi Mai isarta sannan ta koma ta kwanta tana jiran lokacin, gari ne ya fara wayewa Jamilu tana ta shirin tafiya makaranta, cen ƙasan kayanta ta fara lalubawa har ta ciro wata waƙunanniyar Bireziyar da suka taɓa siya ta gwanjo, ita dasu Zaliha suka taɓa siya naira Ashirin -ashirun ita bata taɓa sawa ba tana jin kunya kar Baba Huwaila ta lura tayi mata magana, soketa tayi a ƙugunta kamar ba komai a jikinta ta koma ɗakin Baba Huwaila ta zauna tana tsammanin futowar Jamilu ya yiwa Baba Huwaila sallama.

Ta zauna ba jimawa Jamilu ya fito tsaf dashi yasha wani farin yadi mai ɗison baƙi sai zabga ƙamshi yake, dama Jamilu ba daga nan ba akwai tsafta kwasai-kwasai dashi, Baba Huwaila na daga kwance tayi masa fatan alheri Indo fuskarta wasai ta gaida shi, ahi kansa sai da yayi mamakin yanayin Indo, dan ya lura tana cikin nishaɗi, har ya kusa bakin ƙofa wayarsa ta fara ringing tsayawa yayi domin ya cirota daga aljihu, cikin hanzari Indo ta ciro maƙalalliyar Bra ɗin gurinta wani ɗan guntun Gum ta manna ajiki ta fice ta sabi bokiti kamar mai ɗiban ruwa, lokacin da taje wucewa ta wajen Jamilu yana tsaye yana waya, da sauri ta manna masa ita a bayansa har tayi gaba ta juyo tana masa sannu, mamaki ne ya kama Jamilu shi dai yasan badai Indo ta bigeka har ta juyo ta baka haƙuri ba amma da ya tuno zamam fadar da akayi sai yayi tsammanin taji faɗan da akayi mata ne, yana gama wayarsa ya fice.

Jamilu tafe yake zashi makaranta, amma abinda ya bashi mamaki yanda yaga ɗalibai da sauran ƴan mata suna masa dariya idan ya gifta suwani lokacin harda manyan ma, Jamilu haka ya ƙarasa makarantar da yake koyarwa shigarsa keda wuya Ɗalibai aka dinga zinɗensa wasu na nunashi a fakaice suna tuntsirewa da dariya.

FATAN ALHERI🥰🥰🥰🥰🥰🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[11/07, 14:50] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

37&38
Chapter 16 · 0% Book details