Sashe 9
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu Maigari ya miƙa aka Yusha'u ya miƙo masa wasu takardu masu ɗan yawan gaske, glass ɗinsa ya ciro daga aljihu sai da ya ɗan goge shi sannan ya sa a idonsa sannan ya fara karantawa kamar haka:-
_Muna neman Iyalan Malam Murtala bamaina_
_Sai Iyalan Musa Isa Babandi_
_Ina Iyalan Malam Baharu Rabe_
_Da kuma Iyalan Rakiya Sani Gudidi_
_Sai Iyalan Inno Gwadabe Kunkuru_
_Ina Iyalan Muttaƙa Bala Shinkafi_
_Sai kuma Iyalan Maryo Hashimu Nadabo_
Gaba ɗaya waɗanɗa Maigari ya kira ne suka miƙe tsaye banda Indo da sunkuyar da kai kasa tana dariya harda hawaye, ita gaba ɗaya ma Maigari Dariya yake bashi yanda taga kwana biyu duk ya fige ya lalace kamar wanda yayi jinya, wani tunani ne ya faɗo mata aykuwa ta kuma sunkuyar da kai cikin zaninta tana kuma tintsirewa da dariya, Baba Huwaila haushi ne ya fara kamata cikin jij takaicin Indo ta shureta da Kafarta tana kifta mata ido alamun tayi shiru, suna cikin haka Suka ji Maigari ya cigaba da cewa, " Iya karku kenan waɗanda haƙƙinku yake kaina ko? Dan banasan sai daga baya wani yace mun ga zance ga magana " cikin zumuɗi da azarɓaɓi suka amsa, " Eh mune gamu "
Ƙare musu kallo Maigari yayi yana daɗa leƙensu cikin kallan ƙurulla, dawo da idanunsa yayi cen wajen taron jama'a, cen lungu agefen Baba Huwaila ya hango Indo suna haɗa ido ta ɗauke kai gefe kamar bata ganshi ba, cikin jin haushi Mai gari ya cewa Indo, " Ke Sarƙa kinci ƙaniyarki ke bakiji na ambaci sunan Goggonki bane kika yi shiru kika ƙi tashi? "
Indo ɗan tsuke Fuska tayi sannan ta ce, " Allahbya taimakeka ya baka yawan rai naji mana, kawai dai bari nayi ka sallamesu tukunna sai inyi maka magana saboda akwai saƙon da Goggo ta gayamun ta ce ingaya maka acikin Mafarki na " dirar maganar Indo dai-dai tayi da faɗuwar gaban Mai gari, wata irin zufa ce ta yanko masa take cikinsa yayi wata irin kartawa, amma gudun kar agane halin da yake ciki yasa ya maze ya tsuke fuska ya ce, " Ke Sarƙa banasan sakarcin banza da wofi kinji, ni zaki gwadawa sheɗancin ki " ita ɗinma ƙara tsuke fuska tayi ta ce, " Ranka shi daɗe kasan dai bazanyi maka ƙarya ba, har tace mun ma wai na gaya maka sirrinku kai dasu na dare karka sake ka furtawa kowa " A karo na biyu cikin Maigari ne ya sake kartawa tuni zufa ta rufe shi, da hannu ya goge gumin fuskarsa sannan ya ce, " To to to, to shikenan Allah ya kyauta makwancin " Indo dariya ce ta ciyo ta amma gudun kar mai gari ya ramfo ya yasa ta gimtse bakinta.
Maigari kallan mutanen da ke tsaye yayi ya fara da na farkon da ya kira sunan Mahaifinsa, wasu takardun gona guda uku ya ciro sannan yace, " Ku ɗan dakace ni zuwa wani lokaci saboda takardarku ta huɗun mun saida ta mun tura kuɗin Zariya ana noman rake da shi, lokacin da amfanin gona yayi kyau zamuyi muku magana " karɓa suka dinga yi suna godiya har yazo kan kusa da takardun Indo miƙa masa takardunsu guda biyu yayi sannan ya musu shanunsu guda biyu anturasu kiwo cen garin rogo su da wani ƙaninsa kafin damina ta sauka.
Rufa'i ɗan gidan Malam Muttaƙa kallan takardun yayi tsaf sannan ya cewa Maigari, " Allah ya baka yawan rai bayan da mahaifina ya rasu dai nasan takardu biyar aka baka amma naga ka bamu guda huɗu shanu kuma kace suna kiwo? " ɗan duburburcewa Maigari yayi sannan ya ce, " Ai ita ɗayar itama saida ita mukayi mun tura kuɗin cen garin Daura ana mana noma riɗi da ita, idan albarka ta bayyana yabanya tayi kyau ai kuma zaku ga alama " tsuƙe fuska Rufa'i yayi yan ƙunƙuni ƙasa-ƙasa, Maigari zaburowa yayi ya rufeshi da faɗa, " Kaga tsageran yaro zai kawo mana raini cinye maka dukiyarka zanyi da nayi niyyar cinye maka zaka samu sauran wannan ne, jama'a kuna gani fa dan Allah kuga yaran zamani da rashin kunya " Aikuwa Maigari na gama magana akayowa Rufa'i caaaaaa akansa kowa da abinda yake faɗa, ganin haka yasa ya wuce ya koma mazauninsa ya zauna.
Maigari ne ya kalli gurin da Indo take aikuwa kamar jira take ta miƙe tsaye tana faɗin, " Gani Ranka shi daɗe nasan ni zakayiwa magana " Jamilu dake gefe kallon Indo yayi tundaga ƙasa har sama, takaici ne ya rufeshi musamman da yaga yanda cen ƙasan hujabinta ya wani nannaɗe wanda da za ka ja shi yafi haka tsayi, takalmanta ya gani a cikin sangalalin hannuwanta ta zuzzurasu kamar wani zai ɗauke mata, cikin jin haushi yayi tsaki yana ɗauke kai gefe.
Indo kuwa ko ajikinta bata san ma yanayi ba, Maigari ne ya ce mata, " Ke Sarƙa wazai karɓi takardunki ke zan damƙawa ko Baba Huwaila? " Indo ɗan jim tayi sannan ta ce, " A'a Allah ya baka yawan rai daga ni har ita bazamu karɓi waɗannan takardun ba, ka riƙe ka adana mun agurunka nan da wani lokaci Baba Huwaila ta karɓar mun " Mai gari ji yayi kamar ta watsa mai ruwan zafi musamman da ya tuni gargaɗin da fatalwa tayi masa akan lallai dole ya bawa kowanne maraya haƙƙinsa, cikin masifa ya fara mata magana, " Ke Sarƙa rashin mutumcin naki yazo har kaina, to ni bazan riƙe agurina ba zan baku su idan kunga zaku riƙe to inma watsarwa zakuyi ku kuka sani, Baba Huwaila kina ina? " Baba Huwaila dake gefe ta amsa, " Ranka shi daɗe ayni banda abinda faɗa tunda haƙƙi na yarinya ne kuma tace ka riƙe agurunka " girgiza Kai Mai gari yayi ya ce, " Sai yanxu na fahimci haɗin bakinku wato kema zaki cigaba da ɗaure mata gindi kamar yanda....." Maganar Maigari maƙalewa tayi tunowa da yayi karyaje ya faɗi magana mara daɗi akan Goggo cikin dare su kuma yi masa ba daɗi, basarwa yayi ya kalli Jamilu ya ce, " Kai Jamilu zo karɓi " Jamilu bai musa ba ya miƙe ya karɓo takardun Indo ya koma ya zauna.
Indo kallon Maigari tayi ta ce, " Allah ya taimakeka a cikin Mafarki Goggo ta cemun ko na ƙarbi takardun nan sai ta maidasu da kanta dan haka wallahi ni babu ruwana tunda nace maka bazan karɓa ba " Maigaru sak yayi kamar wanda ruwan jikinsa ya ƙare, amma gudun kar mutane su fahimta sai ya basar ya fara rufe taron, bayan rufe taron ya sallami kowa daga gurin, haka masu takardu ahhanu suka juya guda zuciyarsu fak farun ciki, sauran mutane kuwa sai mita suke akan an ɓata musu lokaci.
Lokacin da suka koma gida Jamilu faɗa ya fara yiwa Baba Huwaila akan tana biyewa Indo, daga baya kuma ya dawo kan Indo itama yana mata faɗa kamar ya cinyeta ɗanya, Ɗakin Baba Huwaila ya shiga ya ɗauko wata jaka yasa takardun aciki ya ɗaga katifar gadon Baba Huwaila ya sa aciki, duk abinda yake faruwa akan idanun Indo murmushi tayi acikin zuciyarta ta ce, " Aykuwa a yau takardunan sai sun koma gurun Mai gari " jim tayi kamar mai nazari kome ta tuna ta sauri ta shuru ta kalminta ta fice Jamilu na ƙwala mata kira ko ta kanshi bata biya ba, kai tsaye cen Zangon malam Idi ta nufa wajen shagon Malam Muddasiru mai likkafani.
*_YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING, INA GODIYA DA WANCEN COMMENTS ÆŠIN ALLAH YA BAR ƘAUNAâ¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸._*
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
21&22
_MAI ZAFAFA KINYO BELINKU YAU NA TACE SHI🤣_
Lokacin da Indo taje shagon Malam Muddasiru mai likkafani sai da ta tsaya daga bayan shagon ta kunto bakin zaninta ta cire wata maƙalalliyar ƴar ɗari biyunta da ta koma kamar tsumma, da Sallama ta shiga shagon cikin sakin fuska yace, " Wai yau Sarƙa ce a shagona ya Baba Huwaila? " Bakin Indo har kunne sai yashe baki take kamar gonar Auduga cikin kulawa ta ce, " Baba Muddasiru ina wuni " Malam Middasiru mamaki ne ya kamashi ƙarara wai yau shi Sarƙa ke cewa Baba har tana gaida shi, cikin sanyin jiki ya amsa da, " Lafiya ƙalau Sarƙa ya gida? " da sauri ta amshe da, " Lafiya ƙalau Baba Huwaila ma tana gaisheka " cikin jindaɗi yace, " Madallah ina amsawa " Indo ɗan jim tayi zuwa cen ta ce, " Baba Mudassiru dama zuwa nayi siyan likkafani na ɗari biyu " xaro idanu yayi yana kallanta yace,
" Likkafani Sarƙa waye ya mutu? Kuma wa ya turo ki? " ganin halin da ya shiga ba ƙaramin dariya ya bata ba, aikuwa sai da tayi mai isarta sannan ta ce, " Ba wanda ya mutu, kawai dai wani aiki aka bamu a makarantar boko wai zane ne za'ayi akai sai a ɗinka da baƙin zare "
Ido ya zura mata kamar bai yarda da maganar Indo ba, amma da yaji tace aiki Malaminsu ya bata sai ya amince, cikin mita ya fara magana.
" Yanzu banda shashanci a rasa da wane yadi za'a bawa yara aiki sai sittirar mamaci, shima malamin duk bokonsa dai ƙarshensa wannan farin yadin "
Tashi yayi ya ɗauko mata wani guntu da baifi rabin yadi ba yace, " Ungo riƙe wannan ki bani ɗari biyun amma kusan kyauta na baki tunda kuɗinsa ya fi haka " Indo cikin Murna ta amsa tana zabga masa godiya.
Abinda Malam Muddasirru bai sani ba rabon Indo da makarantar boko to fara jinyar Goggo yau kimanin kusan wata huɗu kenan, wucewa tayi gida zuciyarta fal da farin ciki, kafin ta ƙarasa tuni ta sokeshi a ƙugunta tana tafe tana ƴar waƙarta harta shiga gida, kai tsaye ɗakinta ta wuce taje ta ɓoyeshi a cen ƙasan adakarta.
Mai gari na gama ganin watsewar jama'a shima ya lallaɓa ya ƙarasa gida saboda ba jin daɗin jikinsa yake ba ƙarfin hali ne kawai ya yi dan ya sauke nauyin da fatalwa ta ɗora masa.