← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 76

Sashe 50

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana Indo ta dawo daga makaranta da yamma liƙis, tana shigowa kamar a mafarki ta hangoshi zaune akan kujera da waya a hannunsa yana dannawa, cikin bazata gabanta yayi mummunar faɗuwa. Dukda shi ba fari bane amma ba ƙaramin canjawa taga ya yi mata dukda batafi wata shida rabon da tayi tozali da shi ba, kyawunsa ya ƙara fitowa har wata ƴar ƙiba taga ya yi. cikin murna ta jefar da jakarta gefe ta zuba da gudu kamar zata rungumeshi sai kuma ta tsaya, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce, "Ya Jamil kaine! Wow dama zaka zo amma ko jiya a waya baka gaya mun ba, ina My Baba Huwaila wallahi nayi missing ɗinku gabaɗaya, Ya Jamil ka ga yadda ka ƙara kyau kuwa" tana faɗa ta ɗan taɓe baki ta cigaba da cewa, "Inama yadda ka ƙara kyau haka ka daina mugunta amma ina wallahi nasan halinka yana nan, Yauwa ya wajensu Zulai yanzu ƴaƴanta nawa?" Kafeta yayi da kallo, wani abu na tsarga masa cikin jikinsa. Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Indo ta hura masa iska a fuska, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu Ayusher wacce tambaya kikesan na fara amsa miki?" ya ƙarasa faɗa yana harɗe hannuwa a ƙirji.

Tura baki gaba tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Ni duka zaka amsa mun" Murmushi yayi ya ce, "To ko zan amsa miki sai kin cire Uniform ɗinki kin huta tukunna" ɗan ɓata fuska tayi zatayi magana ya sa ɗanyatsansa akan laɓɓansa, sannan ya ce, "Kinsan dai bansan..." da sauri Indo ta karɓe zancen da, "Banasan musu, kedai Allah ya yi ki da kunnen ƙashi taurin kai kamar mutanen farko." gabaɗaya suka kwashe da dariya, Jamilu ya ce, "Shiyasa nake missing ɗinki Sarƙar Baba Huwaila yanzu gidanmu duk ba daɗi saboda bakya nan" Indo ta ce, "Ai nasan kashedin ka kenan shiyasa tuni na haddace shi." Duk abinda yake faruwa Fahad dake cen jikin mota yana jinsu kuma yana ganinsu, takowa yayi fuska a haɗe ya ce, "Ke! ba daga makaranta kika dawo ba, wuce ki shige ciki banasan sakarci" Indo ta ce, "Ya Fahad rabin raina na gani, kasan kuwa yadda nakeji da Ya Jamil kuwa? Tagwayen Baba Huwaila wasu ke kiranmu dan Allah ka barmu muyi hirar yaushe gamo" Jamilu wani irin daɗi yaji har cikin ransa, ko ba komai yasan Indo ta bashi babban matsayi. Fahad jin maganganun Indo yayi kamar saukar aradu, yana shirin magana Jamilu ya ce, "Wuce cikin gidan, kinsan banasan rashin kunya..." da sauri Indo ta kuma karɓe zancen da, "Kinsan dai banasa rashin kunya, dan wani lokacin kamar ɓeran birni haka kike" Jamilu murmushi yayi ya taka ya ɗauko mata jakarta ya miƙa mata sannan Indo ta wuce. Fahad sai lokacin ya bar gurin yabi bayan Indo suka wuce ciki, Jamilu yaji ba daɗi sosai dan idan duba alaƙar da ke tsakanin Indo da Fahad sai ya ga kamar zai rasa ta gabaɗaya, dan duk mai hankali yaga abinda Fahad yakeyi yasan Zallar kishi ne yake sashi.

Alhaji Khaleel yaji daÉ—in zuwan Jamilu akan lokaci dukda bai sanar dashi dalilin kiran da yayi masa ba, kafin zuwan nasa. Da daddare suna zaune shi da Fahad,Jamilu da Mommy ya ce.

"Nasan zakayi mamakin jin kiran da nayi maka! Jamilu dalilin da yasa na kiraka ba komai bane sai dan na damƙa amanata ta agurinka, saboda na yaba da hankali da nutsuwarka, na tabbata ko bayan rayuwa ta bazaka ci amana ta ba, zaka riƙe hannu bibbiyu tsakaninka da Allah " Tunda Mahaifin Indo ya fara magana gaban Fahad yake lugude jikinsa har rawa yake, wani irin gumi ne yake keto masa dikda Ac dake cikin falon. Alhaji Khalil ya cigaba da cewa.

"Ban yanke wannan shawarar ba sai da muka tattauna da ƴan uwana, kuma suma ba ƙaramin dadi suka ji ba, danma basa ƙasar da su zasu tattauna da kai ba ni ba. Haka Kawunka Alhaji mun sanar da shi komai kuma yayi farin ciki sosai, sai dai mun roƙi alfarmar karya sanar da kai dan nafisan naji komai daga bakinka." fuskarsa ce ta sauya cikin damuwa ya cigaba da cewa, "Sai dai bansan ya zaka ɗauki lamarin ba zaka amince ko bazaka amince ba shine damuwa ta" a firgice Jamilu da Fahad suka ɗago da kai suna kallan Alhaji Khalil a yayin da ya dire a zancensa.

Hmmmm wallahi akwai ƙura bari nayi nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️

Naga bakya comments sosai 😥 kuyi haƙuri mu raka dan littafin yazo ƙarshe.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[24/09, 13:08] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

83&84

Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon.

Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu.

Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Indo kanta tsaye ta fito itama falon, lokacin da ta ƙaraso Falon Malam Khalid na zaune da sallama, ta shigo falon ta nemi kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fahad da ya shiga kitchen domin ɗebo ruwa a kofi, yana zuwa falon ya bugawa indo tsawa, "Ke! Baki da hankali ne? Wuce ki sako hijabinki" Indo ta ɗan tsorota da yanayin da ta ga Fahad a ciki, amma sai ta shanye tsoronta ta ce, "Ya Fahad ruƙiyar ce har sai na sa wani hijabi meye haɗin aljanu da hijabi na ko..." tun bata rufe baki ba ya tunkaro gurin da take a hassale ya ce, "Zaki wuce ko sai na karya ki a gurin nan" nan take fuskar Fahad tayi jawur jijiyoyin wuyansa duk sun tashi, Indo shiru tayi gabanta sai faɗuwa yake, wannan karan ba ƙaramin tsoron Fahad taji ba. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya ƙarasa gurin ya fisgi hannunta, ya wuce da ita har ɗakinta. Yana shiga ya ce, "Wallahi idan kika kuma fitowa a haka sai na baki mamaki" yana faɗa ya bar gurin ya koma falon.

Bayan Fahad ya koma ya ce, "Malam kayi haƙuri kasan lamarin mata sai a hankali ." Malam Khalid ya ce, "Malam Fahad kasan mata sai da lallami, tunda matarka ce ka dinga janta a jiki bare kaga da ƙuruciya, sai kana kauda kai. Yanzu ka je ka lallasota ku fito tare, kasan ko jinnun jikinta zasu iya sata wasu abubuwan"

Fahad tashi yayi ya wuce ɗakin yana jin zafin Malam dan ya dangantashi da mijin Indo, sai dainta wani fannin tausayinta yaji da ya tuna aljanin da suke jikinta, yana zuwa ya same ta zaune akan katifa ta rafka tagumi kamar wata mutuniyar kirki, cikin sanyin murya yace, "Ki sako hijabinki ki fito Malam yana jiranki" bata ɗago ta kalleshi ba, itama muryarta a sanyaye ta ce, "Ni ka ƙyaleni na fasa zuwa, a ƙyale aljanun su mun duk abinda zasu mun kowa ya huta, tunda dama ba sona ake ba." bakinta yake bi da kallo da yadda take motsa su, lumshe ido yayi ya girgiza kai. Har zai mata faɗa sai kuma ya tuna maganganun Malam, ƙasa-ƙasa ya ce, "To ni da ba mijinta ba? Meye zan wani lallame ta" sai wata zuciyar ta ce masa, "Amma ko ba komai ƴar uwarka ce ta jini" tsugunnawa yayi gabda ita har suna jin numfashin juna ya ce, "Kinsan mutumin nan saboda mu yazo, idan yaga baki fito ba bazai ji daɗi ba. Kuma wa yace miki bama sanki? Da bama sanki zamu nemo miki mai maganin warakar lalurarki?" Indo ware manyan idanunta tayi ta shagala da ƙarewa Fahad kallo, da yadda yake sarrafa laɓɓansa yake mata magana, cikin zuciyarta take ayyana dama Fahad ya iya tausasa murya wajen kalamai? Amma komai yake mata cikin masifa da hantara." ganin ta shagala da kallonsa yasa hannun saitin fuskarta, yana murza ƴan yatsunsa.
Chapter 50 · 0% Book details